Sojoji da 'Yan Sanda Sun Fada Tarkon 'Yan Ta'adda, An Rasa Rayuka Masu Yawa

Sojoji da 'Yan Sanda Sun Fada Tarkon 'Yan Ta'adda, An Rasa Rayuka Masu Yawa

  • Gwamna Nasir Idris ya tabbatar da kisan sojoji tara da dan sanda daya bayan yan bindiga sun yi musu kwanton bauna a jihar Kebbi
  • 'Yan bindiga sun kona motocin sojoji guda biyu kurmus a yankin Shanga yayin da dakarun tsaron ke kokarin kare wani gidan kera gine-gine
  • Gwamnatin jihar Kebbi ta yi alkawarin biyan kudaden maganin wadanda suka ji raunuka tare da tallafa wa iyalan jami'an tsaron da suka rasu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kebbi - Wani mummunan harin kwanton bauna da 'yan bindiga suka kaddamar ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji tara da ɗan sanda ɗaya a ƙaramar hukumar Shanga dake jihar Kebbi.

Gwamnan jihar, Nasir Idris, ne ya tabbatar da faruwar wannan lamari mai ban tausayi wanda ya auku a daren ranar Talata a yankin al'ummar Giro Masa.

Kara karanta wannan

Sunayen manyan jami'an 'yan sandan Najeriya da suka samu sauyin wuraren aiki

Yan bindiga sun kashe sojojin Najeriya a harin kwanton bauna a Kebbi
Wasu sojojin Najeriya sun shirya fita rangadi a Maiduguri, jihar Borno a ranar 16 ga Maris, 2026. Hoto: Audu MARTE / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

'Yan ta'adda sun kashe sojoji a Kebbi

Rahotanni daga majiyoyi daban-daban sun nuna cewa jami'an tsaron sun fada tarkon ‘yan bindigar ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani kamfanin gine-gine bayan samun bayanan sirri, in ji rahoton Channels TV.

A cewar mazauna yankin, maharan sun yi wa jami'an tsaron kofar-rago, inda suka buɗe masu wuta ba zato ba tsammani, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an da kuma farar hula biyu.

Wasu da wannan mummunan lamarin ya faru a kan idonsu sun bayyana cewa maharan sun ƙone motocin sojoji guda biyu yayin fafatawar.

Mazauna garin, waɗanda suka buƙaci a sakaya sunayensu, sun bayyana cewa harin ya munana, kuma ya jefa garuruwan yankin cikin dimuwa da fargabar abin da ka iya biyo baya.

Gwamna ya tabbatar da kisan sojoji

Duk da cewa hukumomin soja ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba, barnar da aka yi ta nuna girman harin, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Matakin farko da alkali ya dauka a zaman shari'ar El Rufai da gwamnatin Najeriya

Gwamna Idris ya bayyana harin a matsayin “rashin imani,” inda ya jaddada cewa sojojin da aka kashe su ne kashin bayan tsaron rayukan al'ummar jihar Kebbi.

Gwamna Nasir Idris ya ziyarci asibitin koyarwa na tarayya dake Birnin Kebbi ranar Laraba, inda ya duba gawawwakin jaruman da kuma waɗanda suka ji raunuka.

Gwamna Nasir Idris ya tabbatar da wannan hari da aka kai wa sojoji da 'yan sanda a Kebbi
Gwamna Nasir Idris yana jawabi ga manema labarai a Kebbi. Hoto: @NasiridrisKG
Source: Twitter

Gwamnati ta dauki nauyin jinyar sojoji

Yayin da yake jawabi ga manema labarai, gwamnan ya ce:

“Wannan lamari ne mai ban takaici. Waɗannan sojoji ne da ke kare rayukan mazauna Kebbi, amma sai suka tsinci kansu a wannan yanayi.”

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jiha za ta biya dukkan kuɗaɗen magani na waɗanda suka ji raunuka, sannan za ta tallafa wa iyalan jami'an tsaron da suka rasa rayukansu.

Bayan ziyarar asibitin, gwamnan ya nufi inda harin ya faru domin gane wa idonsa irin barnar da aka tafka, tare da alƙawarin ƙarfafa matakan tsaro a faɗin jihar.

'Yan bindiga sun kai mummunan hari Kebbi

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe mutane takwas a kauyuka biyu na jihar Kebbi, sannan sun cinna wa gidan shugaban gari wuta.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da jami'an tsaro sun fafata ana shirin kama jagoran yan bindiga a Kano

Hare-haren sun tilasta wa daruruwan mazauna yankin tserewa zuwa garin Shanga bayan barin saboda tsananin tsoro da fargaba.

Rundunar yan sandan ta ce jami'an tsaro sun fara gudanar da sintiri na musamman domin kamo 'yan ta'addar da suka aikata laifin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com