Fadar Shugaban Kasa Ta Tanka bayan 'Yan Adawa Sun Yi Matsaya kan Dokar Zabe
- Jam'iyyun adawa sun fito sun yi fatali da sabuwar dokar zabe wadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattabawa hannu
- Fadar shugaban kasa ta fito ta yi martani kan jam'iyyun adawan inda ta zarge su da yada bayanana karya kan dokar zaben
- Ta bayyana cewa dokar zaben ta kawo sauye-sauye masu muhimmanci wadanda za su kara inganta tsarin zabe a Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi zargi kan jam’iyyun ADC da NNPP da sauran na adawa dangane da dokar zabe.
Fadar shugaban kasar ta zargi jam'iyyun adawa da yaɗa labaran ƙarya game da dokar zaɓe ta shekarar 2026.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X a ranar Alhamis, 26 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan
Atiku da jagororin adawa a Najeriya sun cimma matsaya kan sabuwar dokar zabe ta 2026
'Yan adawa sun yi fatali da dokar zabe
A ranar Alhamis ne jam’iyyun adawar suka soki sabuwar dokar, inda suka bayyana ta a matsayin "mai cutarwa," barazana ga dimokuraɗiyya, kuma yunƙuri na mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya tilo.
Muhimman tanade-tanaden dokar sun haɗa da tura sakamakon zaɓe ta yanar tare da amfani da tattara sakamako ta takarda idan aka samu matsala ta intanet.
Haka kuma, dokar ta tanadi cewa jam’iyyun siyasa su zaɓi ɗan takara ta hanyar zaɓen fitar da gwani na kato bayan kato ko kuma ta hanyar maslaha.
Jam’iyyun ADC da NNPP sun yi watsi da waɗannan sabbin tanade-tanaden, inda suka kira majalisar tarayya da ta soke dokar tare da sake samar da wata.
Wane martani fadar shugaban kasa ta yi?
A cikin sanarwar, Bayo Onanuga ya buƙaci ADC da NNPP da su daina "yawan korafe-korafe da fushin da ba shi da dalili" ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin APC.
"’Yan adawa, musamman jam’iyyar ADC, sun mayar da kalamai marasa kyau a matsayin abin ado, duka don neman shahara a jaridu da kuma ɓatar da jama’a.”
“Kamata ya yi ’yan adawa su daina ƙara gishiri kan tasirin sabuwar dokar zaɓe. Rashin iya daidaita kansu da kuma dabi’arsu ta ɗora wa wasu laifi a bayyane yake.”
- Bayo Onanuga
Onanuga ya jaddada cewa sabuwar dokar zaɓen da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu babban ci gaba ne akan wadda aka soke, domin ta toshe kofar da shugabannin adawa ke son amfani da shi don maguɗi.
Gwamnati ta yi zargi kan 'yan adawa
Ya kuma zargi jam’iyyun adawar da haɗa kai da wasu ƙungiyoyin sa-kai don yaƙar majalisar tarayya da gwamnati ta hanyar yaɗa labaran ƙarya.
Game da korafe-korafen zaɓen fitar da gwani, Onanuga ya ce tsarin zaɓen kato baya kato da na maslaha sun fi nuna dimokuraɗiyya fiye da tsarin amfani da deliget da aka saba amfani da shi a baya.

Source: Facebook
Ya ce ’yan majalisa sun tattauna da kwararru da ’yan ƙasa na tsawon shekaru biyu kafin samar da wannan dokar.
Daga ƙarshe, Onanuga ya yi watsi da zargin cewa Tinubu yana ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.
Tinubu ya mika bukata ga majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika bukatarsa ga majalisar dattawa.
Mai girma Bola Tinubu ya bukaci majalisar da ta fara shirin gyara kundin tsarin mulki domin samar da ’yan sandan jihohi.
Shugaba Tinubu ya ce gyaran kundin tsarin mulki ya zama dole domin a kare dazuzzuka daga hannun masu laifi tare da kawar da tsoro daga zukatan 'yan kasa.
Asali: Legit.ng

