Ana Rade Radin Shirin Gwamna, Shugaban Majalisa da Mambobi 14 Sun Yi Murabus daga PDP
- Alamu sun kara tabbatar da cewa da yiwuwar za a samu gagarumin sauyin siyasa a jihar Adamawa nan ba da jimawa ba
- Shugaban majalisar dokokin Adamawa, Rt. Hon. Bathiya Wesley, da mambobi 14 sun fice daga jam'iyyar PDP a hukumance ranar Laraba
- Sun bayyana cewa sun dauki wannan matakin ne sakamakon rigingimun cikin gida da suka raba jam'iyyar PDP zuwa gida biyu a matakin kasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Adamawa, Nigeria - Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Adamawa, Rt. Hon. Bathiya Wesley, tare da wasu mambobin majalisar su 14, sun fice daga jam'iyyar PDP a hukumance.
'Yan Majalisar sun sanar da murabus din na su daga PDP a hukumance ne a zauren majalisar dokokin da ke birnin Yola, yayin zaman ranar Laraba.

Source: Facebook
Kakakin Majalisa da mambobi 14 sun bar PDP

Kara karanta wannan
'Dan majalisa ya gaji da rikice rikice, ya rubuta wasikar murabus daga jam'iyyar PDP
Jaridar Leadership ta tattaro cewa shugaban Majalisar, Rt. Hon Wesley, ne sa kansa ya karanta dukkan wasikun da yan Majalisar suka gabatar don sanar da ficewarsu daga PDP.
Da yake bayanin dalilinsu na raba gari da PDP, kakakin majalisar ya bayyana cewa “rigingimun da suka ki ci suka ki cinyewa a shugabancin PDP na kasa” ne babban dalilin da ya sa suka yanke shawarar barin jam’iyyar.
Dalilin 'yan Majalisar Adamawa na barin PDP
A nasa bangaren, ahugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Hon. Musa Kallamu, ya goyi bayan shugaban Majalisa.
Ya tabbatar da cewa shawarar da ‘yan majalisar suka yanke na raba gari da PDP ta samo asali ne kai tsaye daga rikicin cikin gida da ke addabar uwar jam'iyyar ta kasa.
“Mun dauki wannan matakin ne sakamakon sabanin da ya tsaga uwar jam’iyya ta kasa zuwa gida biyu,” in ji Hon. Kallamu.
Ya jaddada cewa an dauki matakin ne domin tabbatar da kwanciyar hankali a fagen siyasa da kuma tafiya da yanayin siyasar kasa na yanzu.
Shin Gwamna Fintiri na shirin komawa APC?
Yayin da aka matsa masa da tambayar kan ko ficewar su tana da alaka da jita-jitar da ake yi na cewa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na shirin komawa jam’iyyar APC, Hon. Kallamu bai musanta hakan.

Kara karanta wannan
An fara nuna yatsa ga Tinubu da 'yan bindiga suka farmaki Peter Obi, tsohon shugaban APC

Source: Facebook
Sai dai ya nuna cewa 'yan majalisar dokokin suna nan tare da mai girma gwamna kuma za su magasa biyayya yadda ya kamata a siyasance.
“A matsayinmu na masu bin tsarin demokradiyya, a ko da yaushe muna tare da gwamna. Saboda haka, idan gwamna ya sauya sheka, tabbas mu ma zamu sauya sheka tare da shi,” in ji Kallamu.
Wannan lamarin dai ya kara rura wutar rade-raden cewa nan ba da dadewa ba gwamnan jihar Adamawa zai fice daga jam'iyyar PDP, kamar yadda DW Hausa ta kawo.
Gwamna Fintiri na shirin komawa APC
A dazu, mun kawo rahoton cewa alamu na nuna cewa nan ba da dadewa ba jam'iyyar APC mai-ci a kasa za ta karbi Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri
Majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin sun bayyana cewa Gwamna Fintiri tare da ’yan majalisun tarayya da na jiha sun shirya canza sheka a siyasance.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar aiki Adamawa, inda ya kaddamar da ayyuka.
Asali: Legit.ng