Majalisa Ta Dakatar da Shirin Tantance Sabon Ministan Tinubu, an Ji Dalili
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu aika da sunan Kingsley Udeh ga majalisar dattawa domin tantance shi ya zama minista
- Majalisar dattawan ta shirya gudanar da aikin tantancewar a ranar Laraba, 5 ga watan Nuwamban 2025, amma hakan bai yiwu ba
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya gayawa sanatoci dalilin da ya sa ba za a tantance wanda ake so ya zama ministan ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta dakatar da tabbatar da Kingsley Udeh (SAN) a matsayin minista.
Majalisar dattawan ta dakatar da tantancewar ne saboda rashin samun takardar tantancewar tsaro da ake bukata kafin a tabbatar da shi a matsayin minista.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da hakan yayin zaman majalisar na ranar Laraba, 5 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ba za a tantance ministan Tinubu ba?
Godswill Akpabio wanda ya jagoranci zaman, ya bayyana cewa majalisar ba za ta iya ci gaba da aikin ba, har sai an samu cikakken rahoton tsaro daga hukumomin da abin ya shafa.
“Tabbatar da minista ya kamata ya kasance a jerin jadawalinmu, amma muna bukatar rahoton tantancewar tsaro kafin mu ci gaba."
- Godswill Akpabio
Tinubu ya nemi a tantance minista
A ranar Talata, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da sunan Kingsley Udeh, daga jihar Enugu, zuwa majalisar don tantancewa.
Wannan bukata ta kasance bisa sashe na 147(2) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara), wanda ya bai wa shugaban kasa ikon nada ministoci bayan neman amincewar majalisar dattawa.
Nadin Kingsley Udeh ya biyo bayan murabus din tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, wanda ya ajiye aikinsa bayan cece-kuce kan takardun karatunsa.
Cece-kucen dai ya biyo zargin yin amfani da takardun bogi, musamman game da digirin da ake cewa ya samo daga jami’ar Najeriya, Nsukka.
Uche Nnaji, wanda shi ne kadai dan majalisar zartarwa daga Enugu, ya yi murabus bayan matsin lamba daga jama’a da kuma kiraye-kirayen neman maye gurbinsa.
Murabus dinsa ya sanya jiharsa ta kasance ba tare da wakilci a majalisar zarrtarwa ta tarayya (FEC) ba.
Bayan Akpabio ya karanta wasikar shugaban kasa a Talata, ya mika batun tabbatarwar zuwa ga kwamitin gaba daya na majalisar dattawa gaba ɗaya domin gudanar da tantancewar.

Source: Facebook
Majalisa ta shiga zaman sirri
Sai dai a ranar Laraba, lokacin da batun ya zo a jerin ayyukan majalisar, Akpabio ya sanar da cewa tabbatarwar ba za ta gudana ba saboda rahoton tsaro bai iso ba.
Ya kuma bayyana cewa wani sanata ya shaida masa cewa an riga an turo da takardar tsaro kuma ministan yana kan hanyarsa ta zuwa majalisar.
Daga nan ne Akpabio ya umarci shugaban masu rinjaye da ya gabatar da kudirin shiga zaman sirri domin tattaunawa kan “batutuwan kasa.” Kudirin ya samu goyon bayan ‘yan majalisa, inda daga bisani aka koma zaman sirri.
Majalisa za ta tattauna da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya za ta tattauna da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu.
Majalisar dattawan za ta yi tattaunawar ne kan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan Najeiya.
Shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio ya ce batun ya shafi manufofin diflomasiyya da hulɗar ƙasashen duniya, saboda haka ba za a yi magana gaba-gadi ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


