Kwankwasiya Ta Yi Kamu, Shugabar Matan APC da Wasu Yan Siyasa 100 Sun Koma NNPP
- Wasu mambobin jam'iyyar APC a jihar Kano sun tattara kayansu, sun sauya sheka zuwa NNPP a yankin karamar hukumar Kibiya
- Kwamishinan harkokin jin kai da rage talauci, Alhaji Adamu Kibiya ne ya jagoranci tarbar masu sauya shekan a garin Tarai
- Shugaban matan APC a yankin, Hajiya Sabuwa Tarai, wacce ta jagoranci masu sauya shekar, ta ce sun gamsu da mulkin Gwamna Abba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano da darikar Kwankwasiyya sun kara raunata APC mai adawa.
Shugabar matan APC a mazabar Tarai da ke yankin karamar hukumar Kibiya a Kano, Hajiya Sabuwa Tarai da wasu magoya baya 100 sun sauya sheka zuwa NNPP.

Source: Facebook
Kwamishinan Jin Kai da Rage Talauci na Jihar Kano, Alhaji Adamu A. Kibiya, ne ya tarbi masu sauya shekan hannu bibbiyu a garin Tarai, kamar yadda Vanguard ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama'a na Ma’aikatar Jin Kai, Balarabe Kiru, ya fitar a ranar Laraba, 5 ga watan Nuwamba, 2025 a Kano.
Dalilan sauya shekar 'yan APC a Kano
A cewar sanarwar, waɗanda suka sauya sheka ƙarƙashin jagorancin Hajiya Sabuwa Tarai, sun bayyana cewa salon jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ja ra'ayinsu.
A cewarsu, ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen ci gaban jama’a da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke aiwatarwa ne suka sa suka yanke shawarar komawa jam’iyyar NNPP.
"Mun gamsu da dimbin ayyukan ci gaba da Gwamna Abba Kabir Yusuf yake aiwatarwa a matakin ƙaramar hukuma da na jiha,” in ji Hajiya Sabuwa Tarai.
An karbi masu sauya sheka zuwa NNPP
Da yake jawabi a taron da aka shirya, kwamishinan harkokin jin kai da rage talauci na Kano, Alhaji Adamu Kibiya ya yaba wa wadanda suka sauya sheka zuwa NNPP.

Kara karanta wannan
Daga shiga APC, Gwamna Diri ya yi wa Tinubu alkawarin kaso 99 na kuri'u a zaben 2027
Ya kuma ba su tabbacin cewa za a tafi da su a harkokin jam'iyyar NNPP ba tare da nuna banbanci ba, yana mai cewa da sababbi da tsofaffin mambobi duk daya su ke, iyali daya.

Source: Facebook
Kwamishinan ya kuma ƙarfafa masu gwiwa tare da bukatar su da su haɗa kai wajen daga martabar jam’iyyar NNPP a yankin Tarai domin cimma burin kawo ci gaba a jihar Kano.
Ya ce gwamnatin NNPP karkashin Gwamna Abba ta kuduri aniyar inganta rayuwar al'umma ta hanyar gina ababen more rayuwa, bunkaaa ilimi, da sauran bangarorin ci gaba, in ji rahoton People Gazette.
APC ta kara karfi a jihar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa wasu yan NNPP sama da 1,000 sun sauya sheƙa daga jam'iyya mai mulki a Kano saboda wasu dalilai, sun koma APC.
Yan siyasar sun ce sun koma APC ne saboda nasarorin shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin wajen ciyar da kasa gaba.
Shugaban tawagar da suka sauya sheƙar, Aminu Minjibir, ya bayyana cewa sun yi aiki tukuru wajen ganin nasarar tafiyar Kwankwasiyya amma daga baya aka yi watsi da su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
