Gwamna Abba Ya Yaba Wa Sojoji bisa Nasarar da Suka Samu a Kano, Ya Tura Sako ga Tinubu

Gwamna Abba Ya Yaba Wa Sojoji bisa Nasarar da Suka Samu a Kano, Ya Tura Sako ga Tinubu

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna farin cikinsa da nasarar da jami'an tsaro suka samu kan yan bindiga a Shanono
  • Abba ya yabawa rundunar sojojin Najeriya bisa namijin kokarin da suka yi, tare da ba su tallafin motoci da babura don inganta ayyukansu
  • Kwamandan rundunar sojoji ta sashe na daya, Manjo Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase ya kai ziyara Kano don duba halin tsaro

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yaba wa rundunar sojojin Najeriya da jami’an tsaro bisa matakin da suka dauka cikin gaggawa yayin da yan bindiga suka kai farmaki a Kano.

Gwamma Abba ya ce kokarin da jami'an tsaron suka yi na tunkarar yan bindigan a kan lokaci tare da kashe da dama daga cikinsu abin ya yaba ne.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Tsohon hafsan sojoji ya gano manufar Amurka kan Najetiya

Gwamma Abba da Janar Wase.
Hoton kwamandan rundunar sojoji ta sashe na daya, Manjo Janar Wase tare da Gwamna Abba a fadar gwamnatin Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamandan sojoji ya kai ziyara Kano

Abba ya yi wannan yabo ne da ya karbi bakuncin Kwamandan Rundunar Sojoji na Sashi na 1 da ke Kaduna, Manjo Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase, a fadar gwamnatin Kano.

Manjo Janar Wase dai ya kai ziyara jihar Kano ne domin duba yanayin tsaro a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa bayan harin yan bindiga.

Kwamandan rundunar ya tuna lokacin da mahaifinsa, Marigayi Kanal Muhammad Abdullahi Wase, ya kasance shugaban mulkin soja na jihar Kano a shekarar 1994.

Da yake jawabi, Manjo Janar Wase ya ce:

“Na zo wannan ziyarar ne ta sada zumunta. Tun bayan da na karɓi ragamar rundunar, na ziyarci wuraren da aka kai hare-hare domin in yaba wa jarumtar sojojin mu.”

Kara karanta wannan

'An rasa jigo a Najeriya,' Tinubu kan rasuwar tsohon gwamna, Janar Mohammed

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan bindiga 19 sojoji da hadin gwiwar wasu jami'an tsaro suka hallaka a yankin karamar hukumar Shanono a Kano.

Gwamna Abba ya godewa Tinubu, sojoji

Gwamna Abba ya nuna godiya da yabo ga dakarun sojojin bisa jajircewarsu da sadaukar da kai wajen tabbatar da tsaro a jihar.

Haka zalika, ya aika sakon godiya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa nadin hafsoshin tsaro masu kishin ƙasa.

Gwamna Abba da sojojin Najeriya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da dakarun sojojin Najeriya a gidan gwamnatin Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya sanar da bada kyautar motoci sintiri Hilux guda 10 da babura 60 ga rundunar tsaro ta hadin gwiwa da ke aiki a yankunan da abin ya shafa.

Gwamna Abba ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro wajen yaƙi da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da satar shanu.

Sojoji sun kashe yan bindiga 19 a Kano

A baya, kun ji labarin cewa jami'an tsaron hadin gwiwa karkashin jagorancin sojoji sun yi nasarar dakile yunkurin yan bindiga na kai hari kan jama'a a jihar Kano.

Dakarun taaron sun dakile harin, wanda ‘yan bindiga suka kai kan wasu kauyuka a karamar hukumar Shanonota jihar Kano, inda suka kashe ‘yan ta’adda 19.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gwangwaje tsohon hafsan sojoji da ya yi ritaya, ya kara masa girma

Sai dai, rundunar ta tabbatar da cewa sojoji biyu da ɗan sa-kai guda ɗaya sun rasa rayukansu a yayin artabu da maharan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262