'Sai An Biya Kudi Ake Ganin Tinubu a Aso Villa,' Sanata Ndume Ya Yi Sabuwar Bankada

'Sai An Biya Kudi Ake Ganin Tinubu a Aso Villa,' Sanata Ndume Ya Yi Sabuwar Bankada

  • Sanata Ali Ndume ya yi ikirarin cewa, sai mutum ya ba da cin hanci ne ake bari ya gana da shugaban kasa a Aso Villa
  • Dan majalisar dattawan ya ce akwai wasu jami'an fadar shugaban kasa da ke shirya haduwa da Tinubu idan an biya su
  • Sanata Ndume ya ba da labarin yadda ganin Tinubu ya gagaresa duk da takardun da ya rubutawa jami'an fadar Aso Rock

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mai tsawatarwa a majalisar dattawa, Ali Ndme, ya sake yin sabuwar bankada, inda a wannan karon, ya ce sai an biya kudi ake ganin Shugaba Bola Tinubu.

Sanata Ali Ndume ya ce akwai jami'an fadar shugaban kasa da ke karbar cin hanci daga mutane da ma manyan jami'an gwamnati da ke son gana wa da Tinubu.

Kara karanta wannan

Ido zai raina fata: An cafke dan takarar NNPP da zargin kai wa Gwamna Bago hari

Sanata Ali Ndume ya zargi wasu jami'an fadar shugaban kasa da karbar cin hanci don hada mutum da Tinubu
Hoton Shugaba Bola Ahmed Tinubu da na Sanata Ali Ndume Hoto: @officialABAT, @ChinasaNworu
Source: Twitter

Ndume ya yi zargin rashawa a Aso Villa

Ndume, wanda ya ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da tashar Arise TV a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan majalisar dattawan ya bayyana takaicinsa kan abin da ya kira 'cin hanci da rashawa,' da kuma gurbataccen tsari a tsakanin wasu makusantan shugaban kasa.

A cewar dan majalisar, wasu kalilan daga cikin mutane ko jami'an gwamnati ne ake ba su izinin ganin Shugaba Tinubu ba tare da sha-maki ba.

Amma ya ce duk wadanda ba sa a cikin wannan jerin, sai sun bi ta hannun wasu daga cikin jami'an fadar shugaban kasa, sun biya cin hanci, kafin su ga Tinubu.

Neman kudi kafin haduwa da Tinubu

Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa:

"Ni yanzu haka ba ni da wata kafa ta ganin shugaban kasa. Ina ganinsa ne kawai idan muka hadu a wani taro, baya ga haka, ba na haduwa da shi."

Kara karanta wannan

Tinubu zai karbo rancen sama da Naira tiriliyan 1, ya aika bukata ga majalisa

Ya kara nuna damuwa game da lamarin, yana mai cewa:

"Haka suke tafiyar da gwamnatin. Gwamnatin na cike da wasu bara gurbi, mutanen da ba su cancanta ba, wadanda ba su san komai sai cin hanci da rashawa ba.
"A duk lokacin da ka ce kana da bukatar ganin shugaban kasa, sai su tambaye ka nawa ne kake ganin za ka iya biyansu, domin su yi maka hanya."
Sanata Ali Ndume
Sanata Ali Ndume a majalisar dattawa yana jawabi a Abuja. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Facebook

Sanata Ndume ya gaza ganin Tinubu

Wannan magana ta Sanata Ndume na zuwa ne a dai dai lokacin da ake nuna damuwa game da rashin kyakkyawar alaka tsakanin fadar shugaban kasa da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da 'yan majalisa.

'Dan majalisar dattawan ya ce ya sha bin matakan da suka dace don ganawa da shugaban kasa amma yana samun cikas daga wadannan baragurbin jami'an.

"Na rubuta masu takarda, na nemi ganawa da shugaban kasa don tattaunawa game da batutuwan kasa, amma suka ci gaba da wasa da hankalina kamar wanda ke neman zuwa Aljannah ta hannunsu."

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Bayan PDP ta dare 2, kallo ya koma kan iko da hedkwatar jam'iyyar

- Sanata Ali Ndume.

Har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, jaridar Vanguard ta ce babu wata sanarwar martani daga fadar shugaban kasa game da kalaman Ndume.

'Laifin gwamnati ne,' Ndume kan kalaman Trump

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Ali Ndume ya ce sakacin gwamnati da majalisa ne suka jawo saka Najeriya a jerin kasahen da ke da matsalar 'yancin addini.

Tun da fari, Shugaba Donald Trump na Amurka ne ya maida sunan Najeriya cikin jerin wadannan kasashe saboda zargin kisan kare dangi da ake yi wa kiristoci.

Sai dai, Sanata Ali Ndume ya ce tun farko ya hango wannan matsalar kuma ya ankarar da gwamnatin Bola Tinubu da Majalisa amma suka yi biris.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com