Barazanar Trump: Tsohon Hafsan Sojoji Ya Gano Manufar Amurka kan Najeriya
- Tsohon hafsan sojojin kasa, Laftanal Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya), ya yi tsokaci kan barazanar da Donald Trump ya yi wa Najeriya
- Dambazau wanda ya taba rike mukamin ministan gida, ya bayyana cewa akwai wata manufa da Amurka ke son cimmawa a kasar nan
- Hakazalika Janar din ya nuna cewa matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Najeriya, tana shafar mabiya kowane addini ne
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon hafsan sojojin kasa, Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya), ya yi magana kan barazanar da Donald Trump ya yi wa Najeriya
Laftanar Janar Dambazau mai ritaya ya ce Amurka na kokarin kafa sansanin sojoji a Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Dambazau ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin taron shekara-shekara karo na bakwai da kungiyar Just Friends Club of Nigeria ta shirya a birnin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Dambazau ya ce kan barazanar Trump?
Ya ce maganganun da wasu ‘yan siyasa da shugabannin addini na kasashen waje musamman na Amurka, ke yadawa kan zargin cin zarafin Kiristoci a Najeriya, na iya zama wani shiri na cimma muradunsu.
“Shekaru fiye da 10 Amurka tana da sansanonin sojoji biyu a Jamhuriyar Nijar, amma hakan bai hana yaduwar matsalar tsaro a can ba."
“A bayyane yake cewa a farkon dawowar gwamnatin Trump, ‘yan majalisar dokokin Amurka sun zargi hukumar USAID da taimaka wa ta’addanci a Afirka."
"Don haka, ina ganin Amurka tana neman dama ta kafa sabon sansanin soja a Najeriya, kasar da ta shahara wajen kare bukatunta ta kowace hanya, har da amfani da karfi.”
- Abdulrahman Dambazau
Ya koka kan halayen wasu 'yan Najeriya
Tsohon ministan harkokin cikin gidan ya kara da cewa akwai wasu ‘yan Najeriya da ke goyon bayan da irin wadannan tsare-tsaren na kasashen waje saboda rashin hadin kai a cikin gida.
“Abin takaici, suna da abokan hulɗa a Najeriya. A bayyane yake cewa babu hadin kai wajen fuskantar makiya da magance ta’addanci da rikice-rikicen da ke addabar kasar nan."
- Abdulrahman Dambazau
Me Janar Dambazau ya ce kan ta'addanci?
Ya bayyana cewa matsalar ta’addanci a Najeriya tana da alaka da rikice-rikicen yankin Sahel da tafkin Chadi, rahoton The Punch ya tabbatar da labarin.
Tsohon ministan ya bayyana cewa dukkanin Musulmai da Kiristoci suna fuskantar matsalar ta'addanci.

Source: Facebook
Ya jero misalan hare-haren da aka kai a Arewacin kasar nan, ciki har da kashe malaman addini, sace sarakunan gargajiya da kashe masallata a masallatai.
Dambazau ya yi kira da a hada kai wajen yaki da ta’addanci, yana gargadin cewa kasashen waje na iya amfani da rashin daidaito da rarrabuwar kawuna a Najeriya don cimma wasu muradunsu.
Wike ya fadi matsayarsa kan Trump
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi martani kan barazanar da Donald Trump, ya yi wa Najeriya.
Wike ya musanta zargin cewa ana tsangwamar Kiristoci tare da yi musu kisan kiyashi a kasar nan.
Ministan ya bayyana cewa a shirye yake ya goyi bayan Trump da duk wani mai son taimakawa Najeriya ta shawo kan matsalar rashin tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


