Duniyar Musulunci Ta Yi Babban Rashi, Mufti Haji Umer na Habasha Ya Rasu

Duniyar Musulunci Ta Yi Babban Rashi, Mufti Haji Umer na Habasha Ya Rasu

  • Kasar Habasha ta tabbatar da rasuwar tsohon shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci, Mufti Haji Umer Idris
  • Firaminista Abiy Ahmed da shugabannin addini sun yi jimami tare da yabawa gudunmawar da marigayin ya bayar
  • Sheikh Isa Ali Pantami na cikin wadanda suka yi ta'aziyyar rasuwar malamin bayan dubban mutane sun halarci jana’izarsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Habasha – Al’ummar Musulmi a kasar Habasha na cikin jimami bayan rasuwar tsohon shugaban majalisar koli ta harkokin Musulunci, Mufti Haji Umer Idris, wanda ya rasu bayan rashin lafiya.

Rasuwar malamin addinin ta jawo sakonnin ta’aziyya daga sassan kasar da kuma kasashen waje, inda mutane da dama suka yaba da irin gudunmawar da ya bayar.

Mufti Haji Umer Idris
Babban malamin Habasha, Mufti Haji Umer Idris da ya rasu. Hoto: @AmericaEthiopia
Source: Twitter

Sheikh Isa Ali Panyami ya yi ta'aziyyar rasuwar malamin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya ba Shugaba Tinubu shawara kan yajin aikin ASUU

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar koli ta harkokin Musulunci ta sanar da rasuwarsa a ranar Lahadi, tana mai bayyana shi a matsayin uba ga kowa da kowa.

Shugaban Habasha ya yi ta'aziyyar rasuwar

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya bayyana cewa ya yi matukar bakin cikin rasuwar Mufti Haji Umer Idris wanda ya jagoranci majalisar Musulunci da kwanciyar hankali da jajircewa.

A cewarsa:

“Za mu ci gaba da tuna rawar da Haji Umer ya taka wajen hada kan bangarori daban-daban da kuma tabbatar da doka a majalisar Musulunci.”

Haka kuma, shugaban kasar Habasha Taye Atske-Selassie ya bayyana marigayin a matsayin jagora nagari wanda ya bar tarihi mai kyau a fannin addini da hadin kai a kasar.

An yi sallar jana’izar Mufti Haji Umer

Dubban jama’a sun taru a masallacin Nur dake Addis Ababa domin yin addu’a da sallar jana’iza ga marigayin wanda ya shafe fiye da shekaru 40 yana koyarwa da jagorantar salla a masallacin.

Kara karanta wannan

Zaben 2019: Yadda Akpabio ya yi karyar an yi masa magudin zabe a gaban Sanatoci

An yi karatun Alƙur’ani da addu’o’i na musamman domin neman rahamar Allah SWT ga marigayin wanda aka bayyana a matsayin mutum mai natsuwa, tausayi, da kishin kasa.

Majalisar Musulunci ta bayyana cewa Haji Umer ya kasance jagora da ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomi daban-daban.

Karramawar da Haji Umer ya samu

Kwamitin hulɗar addinai na Ethiopiya ya bayyana marigayin a matsayin mai kishin kasa, wanda bai nuna bambanci tsakanin addinai ko kabilu ba

Shugaban majalisar Musulunci na yanzu, Dr. Sheikh Haji Ibrahim Tufa, ya bayyana rasuwarsa da cewa babban rashi ne ga kasar.

Rahoton TRT Afrika ya nuna cewa an ce marigayin ya taka rawa wajen kafa tsarin bankin Musulunci da tabbatar da sahalewar hukumomin addini a kasar.

Tarihin rayuwarsa da ta’aziyyar Pantami

An haifi Haji Umer Idris a shekarar 1940 a gabashin Habasha, inda ya fara karatun Alƙur’ani a garin Harar kafin ya ci gaba da karatun addini a Sudan da Saudiyya.

Sheikh Isa Ali Pantami, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalansa, dalibansa, abokansa da gwamnatin Habasha, yana addu’a da cewa Allah Ya gafarta masa Ya kuma sanya shi a Aljannar Firdausi.

Kara karanta wannan

'An fi kashe Musulmi,' Hadimin Trump ya karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya

Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Pantami yana wani jawabi a taro. Hoto: Professor Isa Ali ibrahim Pantami
Source: Facebook

Malamin Musulunci ya rasu a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Malam Aminu Adam ya rasu.

Malam Aminu Adam na cikin limaman masallacin Al-Furqan da Sheikh Bashir Aliyu Umar ke jagoranta a Kano.

Malamai a ciki da wajen jihar Kano sun fara ta'aziyyar rasuwar malamin tare da fatan Allah ya gafarta masa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng