Gwamnati Ta Saki Sunaye da Hotunan Jami'an Hukumar DSS 115 da Aka Kora daga Aiki

Gwamnati Ta Saki Sunaye da Hotunan Jami'an Hukumar DSS 115 da Aka Kora daga Aiki

  • Hukumar DSS ta tabbatar da korar jami’anta 115 daga aiki saboda aikata ayyukan da suka sabawa doka, kamar rashawa
  • Hukumar ta gargadi jama’a da su guji hulɗa da waɗanda aka kora domin wasu suna ci gaba da nuna kansu a matsayin jami’ai
  • DSS ta bayyana yadda jama'a za su iya ganin sunaye da hotunan jami'an da aka kora, a wani mataki na tsaftace ayyukanta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar DSS ta sanar da korar jami’ai 115 daga aiki saboda rawar da suka taka a ayyukan da suka saba ka’ida da kuma cin hanci da rashawa.

Hukumar tsaro ta farin kayan ta bayyana cewa matakin na daga cikin shirinta na yin garambawul a cikin gida don kawar da duk wani jami’i da ke lalata sunan DSS.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace mata 9 a Sokoto, sun hallaka wasu

DSS 115
Hoton wasu jami'an DSS da aka sallama daga aiki. Hoto: @OfficialDSSNG
Source: Twitter

DSS ta kori jami'anta 115 daga aiki

Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwa da hukumar ta fitar da yammacin Talata, a shafinta na X, kamar yadda Legit Hausa ta gani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta gargadi jama’a da su guji duk wata hulɗa da waɗanda aka kora, domin wasu daga cikinsu har yanzu suna nuna kansu a matsayin jami’an DSS.

A cewar sanarwar, an wallafa sunayen waɗanda aka kora a shafin yanar gizo na hukumar — www.dss.gov.ng — don jama’a su iya tantance su.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Don neman karin bayani ko yin korafi, jama’a za su iya kiran lambar 09088373515 ko turo da sakon imel zuwa dsspr@dss.gov.ng.”

DSS ta kama wasu tsofaffin jami’anta

Wannan na zuwa ne yayin da DSS ta bayyana cewa ta kama wasu tsoffin jami’an da aka kora, wadanda suka ci gaba da amfani da sunan hukumar wajen yaudarar jama’a.

Kara karanta wannan

Lamari ya girma: Amurka ta soke bizar mutane 80,000, ciki har da 'yan Najeriya

Cikin su har da Barry Donald da Victor Onyedikachi Godwin, wadanda ake zargi da amfani da matsayin su na baya wajen yin zamba da karɓar kuɗi daga mutane da sunan DSS.

An tabbatar da cewa an kama su, kuma za a gurfanar da su a kotu nan ba da jimawa ba, cewar sanarwar DSS a shafinta na X a lokuta daban daban.

Hukumar ta ce wannan ya nuna cewa ta tsaya tsayin daka wajen tsaftace ayyukanta da tabbatar da cewa babu wani da zai yi amfani da sunanta wajen cutar da ‘yan ƙasa.

Matakin na zuwa ne yayin da ake ƙara bincike a kan ayyukan jami’an tsaro a ƙasar, musamman bayan rahotannin da suka nuna rashin gaskiya da cin zarafi a wasu bangarorin na hukumar.

DSS ta gargadi muta ne da su guji mu'amala da jami'anta 115 da ta sallama daga aiki
Hotuna da sunayen jami'an hukumar DSS 115 da aka sallama daga aiki. Hoto: @OfficialDSSNG
Source: Twitter

'Yan Najeriya sun nuna damuwa

A zantawar Legit Hausa da wasu 'yan Najeriya, sun nuna damuwa kan yadda aka bayyana hotuna da bayanan jami'an DSS da aka kora daga aiki.

Kabiru Mai Fulawa Rigasa ya ce:

"Yayin da muke jinjinawa hukumar kan sallamar gurbatattun jami'anta, yana da kyau mu kalli illar da ke tattare da bayyana sunayensu da hotunansu ma.

Kara karanta wannan

INEC ta dauki matasa 24000 aikin zabe, Yiaga ta hango abin da zai faru a Anambra

"Akwai kungiyoyi ko mutanen da su dama irin wannan damar suke jira, za su iya daukar jami'an nan aiki, su rika aikata miyagun ayyuka, saboda ai suna da duk wata kwarewa ta aikinsu.
"Ya kamata a rika boye bayanan ire iren wadannan jami'ai, musamman ma hotuna, suna, da adireshinsu, saboda hakan zai hana a yaudaresu zuwa wani mugun aikin."

Nura Haruna Maikarfe Katsina ma yana da ra'ayi irin na Kabiru Mai Fulawa, inda ya kara da cewa:

"Mun ji irin wahalar da ake sha wajen tantance wadanda ake dauka aikin DSS, saboda tasirin aikin da yadda ya shafi tsaron kasa baki daya.
"To ka san ba a gane halin wani sai ya samu dama, kila, lokacin tantance wadannan jami'an ba su da wani kashi a jikinsu, ba su da wata matsala.
"Amma a hankali suna cikin aikin, sai shaidan ya rude su, su rika aikata laifuffukan da suka sabawa aikinsu da mutuncinsu. A karshe a sallame su.
"To da wannan, muke rokon gwamnati, ta boye bayanansu, sannan a samu masu bibiyar rayuwarsu don ganin cewa ba su sake aikata wani laifin ba."

Kara karanta wannan

Anambra 2025: Manyan laifuffukan zabe a Najeriya da hukuncin da doka ta tanada

'Illar da Bichi ya yi wa DSS' - Jaafar Jaafar

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitaccen dan jarida, Jaafar Jaafar ya ce tsohon shugaban DSS, Yusuf Bichi ya yi mummunar illa ga hukumar lokacin shugabancinsa.

Jaafar Jaafar ya zargi Yusuf Bichi da rikita tsarin daukar aiki a hukumar inda ya ke daukar wadanda suka kammala karatu a jami'o'in Cotonou.

Dan jaridar ya nuna damuwa kan yadda Bichi ya bar matarsa ke shiga lamarin daukar aiki da karin girma a hukumar, da kuma zargin cin zarafin mutane a kan hanya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com