Hukumar Kula Da Shige Ta Fice Ta Kori Jami'anta 4, Ta Hukunta Wasu 32

Hukumar Kula Da Shige Ta Fice Ta Kori Jami'anta 4, Ta Hukunta Wasu 32

  • Hukumar shige da fice ta Najeriya (Immigration) ta hukunta wasu daga cikin bara gurbin cikin jami'anta
  • Daga cikin wadanda aka hukunta, hukumar ta kori jami'ai guda hudu, ta rage wa jami'ai 14 mukami kuma ta ba wa jami'ai 11 wasikar gargadi
  • Tony Akunneme, mai magana da yawun hukumar ya ce an dauki wannan matakin ne don tsaftace hukumar tare da karfafa yaki da rashawa na gwamnatin tarayya

Hukumar Kula da Shige da fice na Najeriya, NIS, ta kori wasu jami'anta guda hudu sannan ta hukunta wasu jami'anta guda 32 saboda laifuka daban-daban.

Ta ce ta dauki matakin ne a yunkurinta na korar bara-gurbi a cikinta sannan ta karfafa yakin da gwamnatin tarayya ke yi da rashawa, The Nation ta rahoto.

Hukumar NIS
Hukumar Kula Da Shige Ta Fice Ta Kori Jami'anta 4, Ta Hukunta Wasu 32. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

An samu ci gaba: Kafin ya sauka, Buhari zai kaddamar da jirage kiran Najeriya

An rage wasu jami'ai 14 mukami, an yi wa jami'ai 11 gargadi, wasu 11 na jiran shari'a

Mai magana da yawun hukumar, Tony Akunneme, cikin sanarwar da ya fitar ya ce an rage wa jami'ai 14 mukami bayan sun gurfana a kwamitin ladabtarwa na Orderly Room.

Akuneme ya ce an wanke wasu jami'ai hudu daga tuhumar da ake musu, yayin da wasu biyun an sauya musu wurin aiki.

Ya kara da cewa an bawa jami'ai 11 wasikar gargadi sannan an yi wa wasu murabus na dole.

A cewarsa, akwai wasu jami'ai 11 da har yanzu suna jiran a yi musu shari'ar tare da yanke hukunci.

Kakakin hukumar ya ce:

"Kwatrola Janar na hukumar shige da fice yana tabbatarwa al'umma cewa babu shafaffu da mai a hukumar NIS don dukkan wadanda suka yi laifi za a hukunta su.
"Ya kuma bukaci al'umma su cigaba da sa ido tare da tallafawa hukumar don ganin ta sauke nau'in da ke kanta."

Kara karanta wannan

Ana bata sunan shugabanmu: Hukumar DSS ta fusata kan yadda ake cece-kuce game da Yusuf Bichi

Hukumar NIS ta ce ta kama yan kasar waje da katin zaben Najeriya

A gefe guda, jami'an hukumar shige da fice sun ce sun kama wasu yan kasashen ketare dauke da katin zabe na yan Najeriya gabanin babban zaben 2023.

The Punch ta rahoto cewa shugaban hukumar Kwastam na Oyo, Isah Dansuleiman ne ya sanar da hakan a Ibadan, babban birnin jihar Oyo yayin hirar wayar tarho.

Ya ce kada duk wani wanda ba dan Najeriya ba ya sake a gan shi da katin zabe na kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164