Me Suka Aikata? Kotu Ta Yanke wa Mutane 3 Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya a Kwara

Me Suka Aikata? Kotu Ta Yanke wa Mutane 3 Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya a Kwara

  • Wata kotu da ke Ilorin ta sallami mata biyu da ake tuhuma da mallakar bindiga da taimaka wa masu garkuwa da mutane
  • Alkalin kotun ya ce masu gabatar da kara sun kasa kawo hujjojin da ke tabbatar da laifin da ake zargin matan da shi
  • Amma kotun ta kuma yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu matasa uku da aka kama da laifin fashi da makami

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara – Wata babbar kotu a jihar Kwara dake da zama a Ilorin ta wanke mata biyu da aka kama da zargin taimaka wa masu garkuwa da mutane.

Hakazalika, kotun ta wanke matan, Aisha Haruna da Rabi Umar Murtala daga zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Kotu ta wanke mata 3 da ake zargi da mallakar makamai a Kwara
Hoton babbar kofar shiga babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: @FederalHigh
Source: UGC

An gurfanar da mata 2 gaban kotu

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kama bindigogi da mugayen makamai ana shirin shiga da su Zamfara

Matan biyu, ciki har da daya mai juna biyu, na tafiya cikin wata mota lokacin da ‘yan sanda suka cafke su a Babanla, karamar hukumar Ifelodun, a ranar 25 ga Yuni, 2025, inji rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa, sauran mutanen da suke cikin motar sun tsere a lokacin da 'yan sanda suka tsayar da su, lamarin da ya sa aka kama matan biyu kawai.

A yayin bincike, ‘yan sanda suka gano bindigar AK-47 da harsasai 31 a cikin jakar daya daga cikin matan.

An gurfanar da su gaban kotu bisa tuhume-tuhume hudu, ciki har da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, taimaka wa masu garkuwa da mutane, da hada baki wajen aikata laifi.

'Hujjoji sun saba wa Juna' — Alkalin Kotu

A lokacin da yake yanke hukunci, Mai Shari’a M.O. Folorunso, ya ce masu gabatar da kara sun gaza tabbatar da zarge-zargen da ke kan matan.

Ya bayyana cewa, bayanan da shaidun ‘yan sanda suka gabatar sun saba wa juna – wani ya ce AK-47 aka gano, wani kuma ya gaza tabbatar da nau’in bindigar.

“Kotu ba ta ga wata hujja da ke nuna matan sun yi wani aiki na laifi ba. Hakan yasa aka wanke su daga dukkan zarge-zargen,” in ji Mai Shari’a M.O. Folorunso.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware kusan N5bn don wasu muhimman ayyuka

Mai Shari’a Folorunso ya kuma umarci lauyoyinsu su ba su kudin sufuri domin su koma garuruwansu na Kaduna da Kanmbi, karamar hukumar Moro.

Kotu ta yanke hukuncin kisa ga matasa 3 da aka kama da laifin fashi da makami
Taswirar jihar Kwara da ke a Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kotu ta yanke hukuncin kisa kan mutum 3

A wani bangare na shari’ar, alkalin kotun ya yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu matasa uku da aka kama da laifin fashi da makami da mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.

An ce sun aikata laifin ne a Oko Erin, cikin Ilorin, a ranar 2 ga watan Maris, 2024, da misalin karfe 6:00 na safe, in ji rahoton The Sun.

A yayin da suke aikata fashin, an ce sun sace wayar salula, kirar Infinix Note 11 daga hannun wani mutum ta hanyar nuna masa bindiga.

Mai shari’a Folorunso, wanda ya nuna damuwa yayin da yake yanke hukunci, har yana matse kwalla, ya ce:

“Waɗannan matasa uku za a rataye su ta wuya har sai sun mutu.”

Katsina: An yanke hukuncin kisa ga mutum 2

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotu a Katsina ta yanke hukuncin kisa ga mai gadi da mai dafa abinci bisa kashe tsohon kwamishina, Rabe Nasir.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan bindiga sun hallaka mutane bayan sace da dama, an 'gano' inda suka fito

Mai shari’a Ibrahim Mashi na kotu mai lamba tara ya samu Shamsu Lawal da Tasi’u Rabi’u da laifin kashe Nasir ta hanyar sa masa gubar da ya ci ya mutu.

Lauyan masu laifi, Ahmad Murtala Kankia, ya roƙi kotu da ta sassauta hukunci saboda waɗanda ake tuhuma na da iyali da masu dogaro da su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com