Asiri Ya Tonu: Bello Turji Na Shirin Kai Sababbin Hare Hare a Wasu Garuruwan Sokoto
- Shahararren dan ta’adda Bello Turji yana shirin kai sababbin hare-hare a garuruwan sokoto bayan da damina ta ja baya
- Yanzu da ruwan koramu ya fara shanye wa, Bello Turji da rundunarsa sun samu hanyoyin kai hare-hare cikin sauki
- An kuma ruwaito cewa, Bello Turji ya sauya kwamandojinsa a wasu yankuna domin sake karfafa ikonsa na 'uban daba'
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Rahotanni daga Arewa maso Yamma sun tabbatar da cewa shahararren dan ta’adda, Bello Turji, ya fara shirye-shiryen kai sababbin hare-hare bayan damina ta ja baya.
Majiyoyi sun bayyana cewa ruwan da ya mamaye kududdufan yankunan Isa da Sabon Birni ya ragu, wanda hakan ya buɗe hanyoyin da suka katse tsawon watanni.

Source: Twitter
Tun lokacin damina, Turji da dakarunsa sun takaita ayyukansu saboda rashin iya ketare rafuka da kwazazzaban da ambaliya ta cika, inji rahoton Zagazola Makama.

Kara karanta wannan
Bayan shan suka, gwamnatin Tinubu ta yi magana kan sakin Maryam Sanda da sauran masu laifi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yanzu kuwa, bayan ruwan ya janye, an ce yana shirye-shiryen komawa kauyuka da dama don sake kafa ikonsa a yankunan.
Bello Turji ya fara sababbin shirye-shirye
Wata majiya daga yankin Isa ta bayyana cewa Turji yana amfani da wannan lokaci don sake farfado da ayyukansa a kauyuka sama da hamsin.
“Ruwan sama da ya hana su kai hare-hare yanzu ya ja baya, Turji zai iya shiga yankuna da dama kai tsaye ba tare da matsala ba,” in ji majiyar.
An kuma ce Turji yana shirin kai ziyara da tattaunawa da wasu shugabannin kauyuka domin tabbatar da biyayya ga rundunarsa.
Wannan al’amari, a cewar mazauna yankin, na iya zama barazana ga kokarin gwamnatin Sokoto wajen dawo da zaman lafiya.
Turji ya yi sabon shiri, ya sauya kwamandoji
Majiyoyi sun ce Turji ya fara sake tsara rundunarsa ta hanyar sauya wasu kwamandoji da suka rasa tasiri ko suka zama masu rauni a yanzu.

Kara karanta wannan
'Dalilin da ya sa na kasance Musulmi kuma Kirista a lokaci guda': Mawaki ya magantu
A yankin Gangara, an ce ya sauya kwamandansa, Jammo Ba’ki da wani sabon na hannun damarsa mai suna Arne Qulu, inji rahoton Daily News.
Rahotanni sun ce sabon kwamandan yana da alaka da wasu manyan ‘yan ta’adda a iyakar Zamfara da Sokoto, wanda zai iya kara sa shi ya fitini jama'a.

Source: Original
An ga karin motsin Turji a karkara
An gano cewa dakarun Bello Turji sun fara motsi cikin kauyuka da ke tsakanin Isa da Sabon Birni, suna gudanar da sintiri da tattara bayanai.
Wani mazaunin Sabon Birni ya ce, “Mutanen Turji sun dawo, amma yanzu suna ƙoƙarin guje wa kai hare-hare kai tsaye.”
Haka kuma, jami’an tsaro suna lura da wannan ci gaban tare da tattara bayanan sirri don hana sake barkewar rikici a wadannan yankuna.
Bello Turji ya saki bidiyo kan sulhu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Bello Turji ya saƙi sabon bidiyo a ranar Alhamis, 7 ga watan Agusta, 2025 kan batun sulhu da aka ce an yi da shi.
Ƙasurgumin ɗan bindigar ya tabbatar da cewa ana tattaunawa domin samar da zaman lafiya a jihar Zamfara da makwaftan jihohi a halin yanzu.

Kara karanta wannan
Tofa: Peter Obi ya maka sanannen lauya a kotu, yana neman diyyar Naira biliyan 1.5
Turji ya kuma caccaki Sheikh Murtala Asada, yana mai cewa ba shi da aiki sai ɓaɓatu da kira ga jami'an tsaro su gaggauta kama Bello Turji.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng