Sheikh Bashir Aliyu Umar Ya Nuna Rigunan Annabi SAW, Nana Fatima da Hussaini

Sheikh Bashir Aliyu Umar Ya Nuna Rigunan Annabi SAW, Nana Fatima da Hussaini

  • Dr. Bashir Aliyu Umar da ke Kano ya nuna rigunan Annabi (SAW) da ‘yarsa Sayyada Fatima (RA) da jikan Annabi, Hussaini (RA)
  • Malamin ya ce rigunan suna ajiye a wani gidan tarihi a birnin Istanbul na kasar Turkiyya inda masu ziyara ke ganinsu ido da ido
  • Ya ce ana sayar da hotunan rigunan a kan akalla Dala 100, kuma kafin shiga gidan tarihin sai an biya kudi ga masu jiran wajen

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano - Malamin addinin Musulunci, Dr Bashir Aliyu Umar, ya nuna wa dalibai rigunan Annabi (SAW) da ‘yarsa Sayyada Fatima (RA) da jikan Annabi Hussaini (RA).

Ya bayyana cewa asalin rigunan suna hannun Daular Abbasiyya tun da dadewa kafin daga bisani su koma hannun Daular Usmaniyya.

Kara karanta wannan

Wale Edun: Ministan kudi ya bayyana a London duk da rahoton rashin lafiyarsa

Dr Bashir Aliyu Umar
Dr Bashir yana nuna riguna da aka samu a tarihi. Hoto: Dr Bashir Aliyu Umar
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da hotunan da malamin ya nuna ne a wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce yanzu an adana rigunan ne a gidan tarihi na Daular Usmaniyya da ke birnin Istanbul a kasar Turkiyya, inda dubban mutane daga sassa daban-daban na duniya ke zuwa don ziyara.

Yadda aka adana rigar Annabi Muhammad (SAW)

Dr. Bashir ya ce, a lokacin da Daular Abbasiyya ke da iko, an rike wadannan kayan tarihi da girmamawa, sannan daga baya Daular Usmaniyya ta karbe su.

Ya ce an sanya rigunan a fadar Sarki a Istanbul, inda aka tanadi wajen ajiya a gidan tarihi domin kiyaye wadannan abubuwa masu tsarki.

Malamin a bayyana hakan ne yayin da yake bayanin hadisi da ya shafi tufafi domin mutane su samu damar ganinsu, ko da kuwa ba su je kasar Turkiyya ba.

Bayani kan rigar Annabi (SAW)

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato

Malamin ya bayyana cewa rigar Annabi (SAW) tana da muhimmanci sosai, kuma tana daya daga cikin abubuwan da aka samu kai tsaye a tarihi.

Yayin da yake bayyana rigar Sayyiduna Hussain (RA), ya karanta hadisin wani sahabi wanda ya taba hatimin annabta da ke jikin Annabi (SAW) ta cikin rigarsa.

Dr. Bashir ya ce irin wadannan riguna ba sa bukatar isnadi, domin abubuwa ne da aka same su a hannun halifofi da suka gaji shugabancin Musulunci tun bayan wafatin Annabi (SAW).

Darajar rigunan a tarihin Musulunci

Malamin ya bayyana cewa wadannan riguna abubuwa ne masu daraja da ba a wasa da su, domin suna cikin shaida ta kai tsaye ga tarihin Musulunci.

Dr Bashir ya kara da cewa ana iya yaki kan lalata wadannan abubuwa na tarihi saboda girman darajarsu.

Dr Bashir Aliyu Umar
Dr Bashir Aliyu Umar yana nuna kayan tarihi. Hoto: Dr Bashir Aliyu Umar
Source: Facebook

Ya ce kafin shiga wajen da aka ajiye rigunan, ana bukatar biyan kudin shiga, sannan ana sayar da hotunan rigunan a kan Dala 100 ga masu sha’awa.

Malamin ya ce duk wanda ya shiga gidan tarihi zai shaida abubuwan tarihi masu ban mamaki da suka shafi addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Jagoran APC ya kare yafiyar Tinubu ga masu manyan laifuffuka

Malaman Musulunci sun yi taro

A wani labarin, mun rahoto muku cewa gamayyar kungiyoyin malaman addinin Musulunci sun yi taro a jihar Kaduna.

Bayanai sun nuna cewa taron ya samu halartar manyan malaman Izala, Darika da sarakunan gargajiya daga Arewacin Najeriya.

Taron ya mayar da hankali ne kan matsalar tsaro da ta addabi Arewacin Najeriya da matsin tattalin arziki da ta jawo talauci a yankin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng