Kwana Ya Kare: Manyan Malaman Darikar Tijjaniya 2 Sun Rasu, Gwamna Ya Yi Magana

Kwana Ya Kare: Manyan Malaman Darikar Tijjaniya 2 Sun Rasu, Gwamna Ya Yi Magana

  • Gwamnan Osun ya yi alhinin rasuwar manyan malaman Darikar Tijjaniya biyu a Najeriya, ya ce musulunci ya yi rashi
  • Sanata Ademola Adeleke ya bayyana malaman a matsayin jagororin hadin kai, wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa addini hidima
  • Malaman da suka koma ga Allah su ne Sheikh Abdul Kareem Raji da Sheikh Abubakar Siddeeq Agbade Abayawo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Rasuwar manyan malaman Darikar Tijjaniya guda biyu ta jefa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke cikin yanayin alhini da jimami.

Malaman da suka rasu su ne Khalifan Tijjaniyya na Jihar Osun, Sheikh Abdul Kareem Raji, da Khalifan Tijjaniyya na Jihar Kwara, Sheikh Abubakar Siddeeq Agbade Abayawo.

Gwamna Adeleke na jihar Osun ya mika sakon ta'aziyya.
Hoton manyan malaman Tijjaniyya da Gwamna Adeleke ya yi alhinin rasuwarsu Hoto: @Osun_State_Gov
Source: Twitter

Sakon ta'aziyyar gwamnan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin jihar Osun ta wallafa shafinta na X mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Mallam Olawale Rasheed.

Kara karanta wannan

Nadin Sarauta: Sarkin Musulmi ya isa Ibadan, ana dakon Tinubu da Atiku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya yi alhinin rasuwar malamai 2

Gwamna Ademola Adeleke, ya bayyana bakin cikinsa tare da mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar wadannan manyan malamai na addinin musulunci guda biyu.

A cikin sakon ta’aziyarsa, Gwamna Adeleke ya ce rasuwar malaman babban rashi ne ga darikar Tijjaniyya, al’ummar Musulmi da kuma kasa baki daya.

Ya ce dukkansu sun sadaukar da rayuwarsu wajen bautar Allah, kokarin shiryar da muminai zuwa tafarkin gaskiya da kuma yada zaman lafiya da hadin kai tsakanin ‘yan kasa.

Adeleke ya mika ta'aziyya ga musulman Najeriya

Gwamna Adeleke ya ce:

“Sheikh Abdul Kareem Raji da Sheikh Abubakar Siddeeq Agbade Abayawo sun kasance ginshikai wajen koyar da ilimin addini da kuma jagoranci.
“Shugabancinsu ya karfafa darikar Tijjaniyya tare da jawo dubbannin mabiyansu zuwa rayuwar imani, sadaukarwa da kyawawan dabi’u. Rasuwarsu babban rashi ne ga Ede, Kwara da Najeriya baki daya.”

Gwamna Adeleke ya jajanta wa al’ummar Musulmi na garin Ede da Jihar Osun kan rasuwar Sheikh Abdul Kareem Raji.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan tsintar gawarwakin yaran masoyin Gwamna Zulum

Ya bayyana shi a matsayin jagoran karfafa imani wanda rashinsa zai bar babban gibi a Osun da ma kasashen waje.

Gwamna ya yiwa mutanen Kwara ta'aziyya

Haka kuma ya aika da ta’aziyarsa ga Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, al’ummar Musulmi da mabiyan Tijjaniyya a fadin kasa bisa rasuwar Sheikh Abubakar Siddeeq Agbade Abayawo.

Gwamna Adeleke ya ce tasirin malamin ya wuce jihar Kwara kadai, ya karade daukacin Musulman Najeriya.

Gwamna Ademola Adeleke.
Hoton Gwamna Adeleke na jihar Osun Hoto: @AAdeleke01
Source: Twitter

A madadin gwamnatin da mutanen Jihar Osun, Gwamna Adeleke ya mika ta'aziyya ga mabiya darikar Tijjaniyya, iyalan malamai biyun da duka mabiyansu a fadin Najeriya.

“Na roki Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta musu kurakuransu, Ya ba su Aljannatul Firdaus, Ya kuma ba iyalansu da mabiyan Tijjaniyya hakurin jure wannan babban rashi,” in ji shi.

Sheikh Modibbo Dahiru ya rasu a Adamawa

A wani rahoton, kun ji cewa malamin addinin musulunci a jihar Adamawa, Sheikh Modibbo Dahiru Aliyu Ganye ya rasu a ranar Talata.

Daya daga cikin hadiman shugaban karamar hukumar Ganye, Farouq Mohammed Ganye ya ce tuni aka binne marigayin bisa tsarin Musulunci.

Kara karanta wannan

Abin Mamaki: Tsohon Sanata ya koma kauyensu, ya karbi sarautar Magajin Gari

Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya nuna kaduwarsa bisa rashin da aka yi inda ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262