Amsoshin Tambayoyi 7 kan Harajin Fetur na 5% da za a Kawo a Najeriya
Mun tattaro muku amsoshin tambayoyi 7 game da harajin 5% da ake sa ran zai fara aiki a kan man fetur a nan gaba.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja -'Yan Najeriya na cigaba da tambayoyi game da harajin 5% da ake cewa gwamnatin tarayya za ta fara karba.
Yayin da aka rika musayar yawu kan harajin, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba a yanke matsaya kan lokacin fara karbar harajin ba.

Source: UGC
A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin tambayoyi da amsoshinsu game da dokar da ke cigaba da jan hankalin 'yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Tinubu ne ya kawo harajin 5%?
Shugaban kwamitin shugaban kasa a kan gyaran haraji, Taiwo Oyedele ya wallafa a Facebook cewa harajin ba sabon abu ba ne a Najeriya.
Ya bayyana cewa yana cikin dokar FERMA ta 2007, saboda haka baya daga cikin sababbin dokokin haraji da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kawo.

Source: Twitter
2. Za a fara biyan harajin a 2026?
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa harajin ba zai fara aiki kai tsaye tare da sababbin dokokin haraji ba.
Sai dai a cewar gwamnatin, ministan kuɗi zai fitar da sanarwar a kan lokacin fara karbar harajin bayan la’akari da yanayin tattalin arziƙi da lokacin da ya dace.

Source: Getty Images
3. Harajin zai shafi dukkan makamashi?
An ware wasu kayan makamashi da ake amfani da su a gida da ba za su shiga karkashin dokar harajin ba.
Oyedele ya bayyana cewa makamashin da aka ware sun haɗa da man girki na kalanzir, iskar gas ta girki (LPG), da kuma iskar gas ta CNG.

Source: UGC
4. Me yasa ba a soke harajin 5% ba?
Punch ta wallafa cewa gwamnatin ta ce an yi karin ne a matsayin kuɗi na musamman da za a tara domin gyaran hanyoyi da gina sababbbi.
A cewar gwamnatin tarayya, idan aka yi amfani da kudin yadda ya kamata, zai taimaka wajen rage haɗura a hanya, sauƙaƙa tafiye-tafiye, rage kuɗin sufuri da gyaran mota.

Kara karanta wannan
Yadda za ka lissafa harajin da za ka biya gwargwadon kuɗin da kake samu a Najeriya

Source: Facebook
5. Ina aka kai kudin tallafin mai?
Duk da cewa kuɗin cire tallafin mai zai taimaka wa kasa, gwamnatin tarayya ta ce ba zai isa ya biya buƙatun gina hanyoyi masu yawan gaske a Najeriya ba.
Daily Trust ta rahoto cewa gwamnatin ta ce za a tara kuɗin harajin 5% ne domin tabbatar da an samu tushe mai dorewa da tabbataccen kuɗin yin hanyoyi, baya ga kasafin kuɗi.

Source: Getty Images
6. Harajin 5% zai kara nauyi ga jama'a?
Gwamnatin tarayya ta ce sauye-sauyen da aka yi sun riga sun rage nauyin haraji da dama kuma sun soke wasu ƙarin kuɗi da suka shafi jama’a da ƙananan masana’antu kai tsaye.
Ta ce harajin 5% ba zai zama karin nauyi ba saboda an cire harajin VAT kan man fetur da harajin tsaron yanar gizo.

Source: Getty Images
7. Za a cire harajin daga dokar FERMA?
Fadar shugaban kasa ta ce an riga an cire shi daga dokar FERMA an haɗa shi cikin sababbin dokokin haraji da aka tsara.
Gwamnatin ta ce harajin 5% ya tabbatar da cewa Najeriya ta shirya wajen fuskantar manyan ƙalubale, irin su samar da kuɗin hanyoyi a fadin Najeriya.

Source: UGC
Harajin gwamnatin Tinubu zai shafi jama'a
A wani rahoton, kun ji cewa masana sun fara bahasi kan yadda dokar harajin shugaba Bola Tinubu za ta shafi al'umma.
An bayyana cewa dokar za ta shafi kusan dukkan harkokin 'yan Najeriya da zarar ta fara aiki a nan gaba.
Wani bincike ya nuna cewa zai shafi masu sana'o'in hannu da ma'aikatan gwamnati musamman wajen zirga zirga.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

