An Zo Wajen: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magana kan Lokacin Fara Biyan Harajin Fetur
- Batun sabon haraji kan fetur ya jawo 'yan Najeriya da dama na sukar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Ministan tattalin arziki, ya fito ya yi magana kan lokacin da za a fara aiwatar da harajin wanda zai sanya a samu karin N45 kan kowace lita
- Wale Edun ya bayyana cewa harajin tsohon abu ne wanda ba gwamnatin Tinubu ba ce ta kirkiro da shi ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi magana kan lokacin fara aiwatar da harajin man fetur.
Gwamnatin tarayya ta ce ba ta wani shiri a halin yanzu na aiwatar da harajin fetur na kaso 5% da aka sanya a cikin sabuwar dokar haraji ta 2025.

Source: Getty Images
Jaridar TheCable ta kawo rahoto cewa ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin kasa, Wale Edun, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Talata, 9 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan
Yadda za ka lissafa harajin da za ka biya gwargwadon kuɗin da kake samu a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin ministan ya biyo bayan damuwar da mutane da dama suka nuna kan aiwatar da harajin.
Yaushe za a fara biyan harajin fetur?
Yayin da yake magana kan harajin, Wale Edun ya bayyana cewa harajin, tsohon tanadi ne da aka fara gabatarwa tun shekarar 2007 karkashin dokar hukumar FERMA.
Ya bayyana cewa ba sabon haraji ba ne da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta kirkiro.
A cewarsa, sanya tanadinsa a cikin dokar haraji ta 2025 wani ɓangare ne na kokarin hada dokokin da ake da su wuri guda.
"Yana da muhimmanci a fayyace wannan batu: sanya karin a cikin dokar haraji ta Najeriya ta 2025 ba yana nufin an kawo sabon haraji bane. Ba yana nufin za a fara biyan wani sabon haraji kai tsaye bane."
- Wale Edun
Ministan ya kuma bayyana cewa sabuwar dokar ba za ta fara aiki ba sai daga 1 ga watan Janairu, 2026.
Hanyoyin da za a bi kafin aiwatar da harajin
Haka nan, duk wani yunkuri na aiwatar da harajin zai buƙaci a samu umarni na musamman daga ministan kuɗi wanda za a wallafa a hukumance.
"Akwai tsari na musamman da ake bi kafin hakan. A halin yanzu, babu wata sanarwa da aka bayar, babu wata da ake shirin bayarwa, kuma babu wani shiri na gaggawa na aiwatar da wannan harajin."
- Wale Edun
Vanguard ta ce Wale Edun ya kara da cewa babban burin gwamnati a shirin gyaran tsarin haraji shi ne sake fasalinsa, domin kawar da rudani.

Source: Facebook
Ya ce dokar haraji tana daga cikin dokoki guda huɗu da aka amince da su domin inganta gaskiya, saukaka bin doka ga ‘yan kasa da kamfanoni da tattara kudaden shiga.
Wale Edun ya kara da cewa shirin gyaran ya biyo bayan shekaru ana tattaunawa, aikin fasaha da haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki daban-daban.
Barazanar yajin aiki kan harajin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar kwadago ta TUC ta nuna rashin amincewarta kan harajin man fetur da aka bullo da shi.
Shugabannin TUC sun bayyana cewa harajin da gwamnatin tarayya ta dorawa 'yan Najeriya sun yi yawa.
Kungiyar ta yi barazanar tsunduma cikin yajin aiki idan har gwamnatin tarayya ba ta yi gaggawar janye harajin ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

