Gwamna Uba Sani Ya Yi Wa 'Yan Siyasa Shagube, Ya Fadi Bambancinsa da Su

Gwamna Uba Sani Ya Yi Wa 'Yan Siyasa Shagube, Ya Fadi Bambancinsa da Su

  • Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya halarci wani wurin kaddamar da aikin gina titi a daya daga cikin kananan hukumomin jihar
  • A yayin da yake jawabi a wajen, Gwamna Uba Sani, ya yi shagube ga 'yan siyasa masu zuwa gidan talabijin suna ta yin surutu
  • Gwamnan ya bayyana cewa salon mulkinsa ba irin hakan ba ne, don yana da abubuwan da yake son cimmawa kan mutanen da suka zabe shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya soki ‘yan siyasa masu bayyana a gidan talabijin suna kurin suna da biliyoyi.

Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa gwamnatinsa ta fi mayar da hankali kan sakamako na zahiri fiye da hayaniya.

Gwamna Uba Sani ya yi wa 'yan siyasa shagube
Hoton gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, yana jawabi a wajen taro Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Uba Sani ya kaddamar da aikin titi

Jaridar TheCable ta ce Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ranar Litinin a Unguwan Dantsoho, mazabar Sabon Gari ta karamar hukumar Kudan.

Kara karanta wannan

Bayan tsawon lokaci, gwamna ya tabbatar da fara tattaunawar sulhu da 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya yi jawabin ne a wajen kaddamar da aikin titin kilomita shida da zai haɗa kananan hukumomin Kudan da Sabon Gari ta hanyar kwanar Hunkuyi da Basawa.

Gwamna Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar yin ayyuka ba a cikin babban birni kadai ba, har zuwa ƙauyuka da aka daɗe ana watsi da su.

Me Uba Sani ya ce kan 'yan siyasa?

"Wasu ‘yan siyasa sun kware wajen bayyana a talabijin kawai, suna ikirarin cewa gwamnatinsu ta tara biliyoyi, amma babu abin da ake iya nunawa a kasa. Mu ba gwamnati ce ta masu hayaniya ba."
"Lokacin da na hau mulki, na yi alkawarin kai ci gaba a birane da kauyuka saboda kudaden shiga na jihar Kaduna ba na masu zama a birni kaɗai ba ne.”

- Gwamna Uba Sani

Gwamna Uba Sani ya tuna da Kudan

Gwamna Uba Sani ya ce aikin na cikin alkawarinsa na gyara watsin da aka yi da Kudan, ɗaya daga cikin kananan hukumomi 12 da ba su ci gajiyar samun ko hanya daya ba a sama da shekara 10.

Kara karanta wannan

Biyan 'yan bindiga kudi: Gwamna Uba Sani ya yi martani kan zargin El Rufai

Gwamna Uba Sani ya soki 'yan siyasa
Hoton gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, yana jawabi Hoto: @ubasanius
Source: Facebook
“Karamar hukumar Kudan tana cikin kananan hukumomi 12 da ba su ci gajiyar samun ko da hanya guda ba cikin shekaru 12 da suka wuce. Ya kamata ‘yan siyasar wannan yanki su ji kunya."

- Gwamna Uba Sani

Haka kuma ya sanar da shirin gina asibiti a Unguwan Dantsoho da kuma samar da tallafin kuɗi ga mata don inganta rayuwarsu.

Uba Sani ya musanta biyan 'yan bindiga kudi

A wani labarin kuma, kun ni cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya fito ya maida martani kan zarginsa cewa gwamnatinsa na biyan 'yan bindiga kudade a shirin sulhu don samun zaman lafiya.

Gwamna Uba Sani ya musanta zargin, inda ya bayyana cewa ko sisin kwabo gwamnatinsa ba ta taba biyan 'yan bindiga ba.

Ya bayyana cewa zargin ba komai ba ne illa surutun banza irin na 'yan siyasa, inda ya nuna cewa shirinsa na sulhu ya sanya an samu zaman lafiya a wuraren da ke fama da rikici.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng