Bayan Tsawon Lokaci, Gwamna Ya Tabbatar da Fara Tattaunawar Sulhu da 'Yan Bindiga

Bayan Tsawon Lokaci, Gwamna Ya Tabbatar da Fara Tattaunawar Sulhu da 'Yan Bindiga

  • Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da batun tattaunawa da yan bindiga don dawo da zaman lafiya a jiharsa
  • A cewarsa, an samu zaman lafiya a kananan hukumomi hudu da hare-hare suka yi kamari, yayin da tattaunawa ta yi nisa a wasu wuraren
  • Gwamna Dikko Radda ya kaddamar da wani shirin hadin gwiwa da zai farfado da yankunan da matsalar tsaro ta fi muni a Katsina

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa da ’yan bindiga da suka addabi al’ummomin karkara a jihar.

Wannan tattaunar neman sulhu da yan ta'addan na zuwa ne bayan tsawon shekaru biyu Gwamna Radda na nanata cewa ba zai shiga yarjejeniyar sulhu da yan bindiga ba.

Kara karanta wannan

Birtaniya ta dage takunkumin tafiye tafiye da ta kakaba wa jihar Kaduna

Gwamna Dikko Radda.
Hoton Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda a fadar gwamnati Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Gwamna Dikko Radda na daya daga cikin gwamnonin Arewa da suka nesanta kansu daga shirin sulhu da ’yan bindiga a kwanakin baya, in ji rahoton This Day.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya tabbatar da ana tattunawa da 'yan bindiga

Amma a yau Litinin, Dikko Radda ya bayyana cewa tattaunawar ta kawo nasara a kananan hukumomi hudu daga cikin wadanda ke sahun gaba a fama da matsalar tsaro.

Ya yi wannan bayani ne yayin kaddamar da wani shiri na watanni 18 mai suna Conflict Prevention, Crisis Response and Resilience (CPCRR) wanda Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta dauki nauyi.

EU ta samu hadin gwiwar kungiyoyin IOM d CDD da Mercy Corps, domin inganta zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a Katsina da Zamfara.

Ana ci gaba da tattaunawar sulhu a Katsina

A cewar gwamnan:

“Wannan shiri na al’umma ne, su za su jagoranta kuma ya dace da al’adu. Za mu tabbatar da an jawo matasa, mata da masu nakasa wajen tsare-tsare da aiwatar da manufofin gwamnati.

Kara karanta wannan

Tawagar kasar Rasha ta dura Najeriya, ta sauka a jihar Neja

“Zan iya tabbatar muku cewa, saboda shirin tattaunawa zaman lafiya da al’umma suka kirkiro, mun samu damar warware matsalar tsaro a kananan hukumomi hudu daga cikin takwas.
"Sannan tattaunawa ta yi nisa a wasu kananan hukumomi biyu, wannan nasara ce."

Dikko Radda ya ce shirin zai magance tushen rikice-rikice a kananan hukumomi takwas da ke fuskantar barazana ta tsaro.

Ya ce komai na iya kara tabarbarewa matukar ba a dauki matakan magance matsalar tun daga tushe ba.

Malam Dikko Radda.
Hoton Mai girma Gwamna, Malam Dikko Radda a wurin taro a Katsina Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Twitter

Manyan matsalolin Katsina ke fama da su

Ya kara da cewa jihar na fama da matsalolin fari, hamada da karancin filayen noma, wadanda ke kara gasa da kuma jefa al’umma cikin mawuyacin hali.

Rashin aikin yi ga matasa da durkushewar tattalin arziki, a cewarsa, na kara rura wutar rikicin matsalar tsaro, cewar rahoton Punch.

Gwamnan ya jaddada cewa, “Wadannan matsaloli ba daban-daban suke ba, a hade suke wuri guda, muna bukatar ingantaccen tsari na al’umma da mafita mai dorewa.”

Wani matashi, wanda yana daya daga cikin masu sintiri don kare kansu a Katsina ya ce ba su adawa da sulhu amma ya kamata gwamnati ta sake nazari.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Kungiyar dattawan Arewa ta samo.mafita ga gwamninin yankin

Da yake zantawa da wakilin Legit Hausa bisa sharadin boye bayanansa, ya ce a tarihin Katsina, an yi sulhu da yan bindiga sau da dama amma suka ci amana.

"Duk wani mataki da zai kawo zaman lafiya mai dorewa a garuruwanmu muna maraba da shi amma batun sulhu, ba ma goyon bayan a yi irin wanda aka yi a baya.
"Idan suna son sulhu, to su tattaro duka makamansu su mika wa hukumomi, kuma a yi yarjejeniya duk wanda ya karya alkawari a dauki mataki a kansa.
"Ba zai yiwu a yi sulhu kuma dan ta'adda ya koma da makaminsa gida ba," in ji shi.

Gwamna Radda ya ziyarci kauyen Mantau

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa kauyen Mantau a karamar hukumar Malumfashi.

Wannan ziyara ta zo ne kwanaki kadan bayan mummunan harin da yan bindiga suka kai da asubah, suka kashe masallata sama da 30.

Bayan ganin halin da mutane ke ciki a kauyen, Dikko Radda ya sha alwashin taimakawa mutanen kauyen Mantau, inda ya ce za a ba kowane iyalin N500,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262