Biyan 'Yan Bindiga Kudi: Gwamna Uba Sani Ya Yi Martani kan Zargin El Rufai

Biyan 'Yan Bindiga Kudi: Gwamna Uba Sani Ya Yi Martani kan Zargin El Rufai

  • A kwanakin baya tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa ana biyan 'yan bindiga kudi a jihar
  • El-Rufai ya yi zargin cewa biyan kudaden na daga cikin shirn sulhu da gwamnatin Kaduna ta bullo da shi
  • Sai dai, Gwamna Uba Sani ya fito ya fede biri har wutsiya kan yadda shirin gwamnatinsa na yin sulhu yake

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi martani kan zargin cewa gwamnatinsa na biyan 'yan bindiga kudade.

Gwamna Uba Sani ya karyata zargin cewa gwamnatinsa na biyan ‘yan bindiga kudi, inda ya bayyana ikirarin a matsayin surutun banza na siyasa.

Gwamna Uba Sani ya nuna yatsa ga El-Rufai
Hoton Gwamna Uba Sani a ofis da na tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a gefe Hoto: @ubasanius, @elrufai
Source: Facebook

Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Politics on Sunday' na tashar TVC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin Uba Sani kan zargin Nasir El-Rufai

Kara karanta wannan

Yaron El Rufa'i: Uba ya yi raddi ga kalamai da zarge zargen tsohon Gwamnan Kaduna

Uba Sani ya maida martani ne ga Nasir El-Rufai, wanda ya zargi gwamnatin tarayya da ta jihar Kaduna da ba kungiyoyin ‘yan bindiga kuɗi a karkashin shirin yin sulhu.

El-Rufai dai ya yi ikirarin cewa gwamnati na bin manufar da ya kira faranta ran 'yan bindiga, wadda ta haɗa da biyan alawus da samar da kayan abinci ga 'yan ta'adda.

Sai dai, Gwamna Uba Sani ya soki wannan zargi, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba ta taɓa bayar da kuɗi ga ‘yan bindiga ba.

Ya bayyana cewa tsarin sulhu na Kaduna wanda aka gina bisa kan karfafa jama’a, warware matsalolin da suka haddasa ta’addanci da kuma gina amana, shi ne ingantaccen tsari da ya dace wajen shawo kan matsalar ta’addanci a Arewa maso Yamma.

“Ba mu taɓa biyan sisin kwabo ga ko mutum guda ba, ko Naira ba mu taba ba kowa ba. Tsarin sulhu na Kaduna na dogaro ne kan al’ummomi, tare da shugabannin addini da na gargajiya. Ba shi da wata alaka da biyan kuɗi ga ‘yan bindiga."
"Lokacin da muka fara wannan tsarin a Kaduna, da yawa sun yi tunanin ba za mu yi nasara ba. Amma a yau, an samu nasara."

Kara karanta wannan

"Mun gano tushen matsalar": Gwamna Uba Sani ya fadi dalilin sulhu da 'yan bindiga

"Shugabannin tsaro a faɗin Najeriya sun fito fili sun yaba da shi, sun kuma buƙaci a ɗauke shi a matsayin tsarin da za a yi aiki da shi a sauran jihohi."

- Gwamna Uba Sani

Uba Sani ya ce an samu zaman lafiya

Gwamna Uba Sani, wanda ya nuna cewa an samu zaman lafiya a wuraren da aka sha fama da matsalar tsaro kamar Birnin Gwari, ya zargi wasu ‘yan siyasa da amfani da matsalar tsaro don cimma manufar siyasa.

Gwamna Uba Sani ya musanta biyan 'yan bindiga kudade
Hoton gwamnan Kaduna, Uba Sani, yana jawabi a wajen taro Hoto: @ubasanius
Source: Facebook
“Wasu ‘yan siyasa suna kokarin yaudarar jama’a da yaɗa bayanan karya don cimma muradun siyasa. Amma a Kaduna, babu wanda aka biya kuɗi. An zaɓe mu domin mu magance matsaloli, ba domin mu dorawa wasu laifi ba."

- Gwamna Uba Sani

Uba Sani ya magantu kan sulhu da 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana dalilnsa na yin sulhu da 'yan bindiga.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa ya yi sulhun ne bayan ya gano tushen matsalolin da ke haifar da ta'addanci.

Ya nuna cewa dole ne shugabanni su dauki alhaki kan matsalar rashin tsaro maimakon su rika dora laifi a kan wasu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng