Sauye Sauye 5 da Gwamnatin Tinubu Ta Kawo a Tsarin Karatun Firamare da Sakandare

Sauye Sauye 5 da Gwamnatin Tinubu Ta Kawo a Tsarin Karatun Firamare da Sakandare

  • Gwamnatin Tarayya ta kawo sababbin sauye sauye a kundin tsarin karatu, wanda zai shafi makarantun firamare, sakandare da na fasaha
  • Karamar ministar ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad, ta ce sabon tsarin zai rage yawan darussan da ake koyarwa don karfafa fahimtar dalibai
  • Legit Hausa, ta tattaro sababbin sauye sauye biyar da gwamnatin ta kawo a tsarin ilimin, da nufin inganta koyo da koyarwa a kasar nan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Gwamnatin Tarayya ta sabunta kundin tsarin koyarwa a makarantun Najeriya wanda ya shafi firamare, sakandare da makarantun fasaha.

An gabatar da sabon tsarin karatun domin rage yawan darussa ga ɗalibai tare da ƙara zurfafa ilimi, don samar da ingantaccen sakamako a gaba.

Gwamnatin tarayya ta kawo sauye sauye a tsarin karatun firamare da sakandare na Najeriya
Daliban makarantun sakandare na kokarin shiga aji a wata makaranta da ke Borno. Hoto: Audu Marte
Source: Getty Images

Dalilin sabunta karatun firamare da sakandare

Karamar ministar ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad, ta ce sabon tsarin zai baiwa ɗalibai lokaci mai yawa don koyo ba tare da damuwa da ɗimbin darussa ba, inji rahoton BBC.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi yankin da ya fi more ayyukanta na alheri

Farfesa Suwaiba ta ce sauyin ya zama dole saboda tsohon tsarin karatun, mai dauke da yawan darussa, ya dakile ɗalibai daga fahimtar abubuwan da ake koya masu sosai.

Bugu da ƙari, rahoton hukumar WAEC ya nuna cewa, sakamakon jarabawar SSSCE na baya shi ne mafi tabarbarewa a cikin shekaru biyar.

Hukumomin da suka kawo sauye sauyen karatun

Wannan ya gwamnati ta ga dacewa gabatar da sauye sauye a tsarin karatun kasar, domin mayar da hankali kan ƙwarewa da fahimta, ba wai kawai yawan darussa ba.

Sabon kundin an tsara shi ne tare da haɗin gwiwar hukumomi da dama ciki har da NERDC, UBEC, NSSEC, NBTE, da kuma sassa daban-daban na ma’aikatar ilimi.

Farfesa Suwaiba Ahmad ta ce an gina tsarin ne ta hanyar tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa zai dace da bukatun ɗalibai da ƙasar gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin NEMA, Ambaliya ta afka wa dubban mutane a Adamawa

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa sauye-sauyen za su taimaka wajen inganta ilimi a kananun makarantu don gina su kafin shiga manyan makarantu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a yayin da ake shirin fara taron majalisar zartarwa na kasa a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Sauye sauye 5 da aka kawo a firamare, sakandare

1. Firamare 1–3: Za su ɗauki darussa 9 zuwa 10, ciki har da Turanci, Lissafi, Kimiyya da Fasaha, Al'adu da Fikira, Addini da Ƙimomin Ƙasa, da harshe guda na gida.

2. Firamare 4–6: Za su ɗauki darussa 10 zuwa 12, ciki har da darasin koyon sana'o'i da sauran darussan da firamare 1-3 za su dauka.

3. Ƙaramar sakandare (JSS): Za su ɗauki darussa 12 zuwa 14, ciki har da darasin kasuwanci, Faransanci, da harshe guda na Najeriya.

4. Babbar sakandare (SSS): Za su rage zuwa darussa 8 zuwa 9, ciki har da Civic Education, Humanities, Kasuwanci, da Kimiyya.

5. Makarantun Fasaha: Za su ɗauki darussa 9 zuwa 11 domin tabbatar da daidaiton koyarwa da sana’o’i.

Ko da yake ba a bayyana ranar da sabon tsarin karatun zai fara aiki ba tukuna, ministar ta ce za a aiwatar da shi tare da tsauraran matakan sa ido, a cewar Punch.

Kara karanta wannan

Sokoto: Yan bindiga sun yashe gari tas, sun sace basarake da duka limaman gari

Gwamnati ta rushe tsarin makarantun sakandare

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya ta kawo sabon tsarin karatun bai daya, wanda ya zi kawo karshen tsarin makarantun JSS da SSS.

Ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa ya bayyana cewa sabon tsarin karatun na shekaru 12 a jere, zai rage yawan daliban da ba sa iya kammala karatu a kasar.

Dr. Tunji Alausa ya kara da cewa, sabon tsarin zai kawo cigaba mai dorewa a fannin ilimi, wanda ake sa ran zai dace da bukatun ilimin sakandare na duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com