"Sojoji ba Za Su Iya Murkushe Yan Bindiga a Jihohi 7 ba," Gwamna Ya Tsage Gaskiya
- Gwamnan Kaduna ya bayyana cewa daukar matakin soji ba zai iya magance matsalar tsaron da ta addabi Arewa maso Yamma ba
- Sanata Uba Sani ya ce ya zama wajibi gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su warware abubuwan da suka haifar da matsalar tsaron tun daga tushe
- Ya ce talauci, nuna wa wasu jama'a wariya, rashin shugabanci nagari da zaman kashe wandon matasa na cikin tushen tabarbarewar tsaro a yankin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce dakarun soji da matakan da ake dauka na karfi ba za su iya kawo karshen ta'addanci a Arewa maso Yamma ba.
Uba Sani ya bayyana cewa matsalar tsaron Arewa ta samo asali ne daga talauci, rashin daidaito, wariya, rashin shugabanci nagari da zaman kashe wandon matasa.

Source: Twitter
Ya jaddada cewa matukar ba a magance waɗannan dalilai ba, duk wata nasarar da sojoji za su samu ba za ta dore ba, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Gwamnan ya fadi haka ne yayin da yake jawabin bude taron kwanaki biyu na lalubo hanyoyin magance tsattsayran ra'ayin ta'addanci (PCVE) a Kaduna.
Ana ganin dai gwamnatin tarayya ta haɗa waɗannan dalilan cikin dabarun yaƙi da ta’addanci, inda ta raba ayyukanta zuwa hanyoyi biyu: matakin soji da na zaman lafiya.
Taron koli kan tsaro a Arewa maso Yamma, ya haɗa jami’an tsaro, masu tsara manufofi da kungiyoyin farar hula da shugabannin yankin a Kaduna.
Kwamishina ya wakilci gwamnan Kaduna a taro
Gwamnan Kaduna, wanda Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Sule Shuaibu, ya wakilta, ya bayyana tsattsauran ra’ayi a matsayin babbar barazana ga tsaro cigaban ƙasa.
Ya ce matsalar ta tilasta wa mutane barin gidajensu saboda hare-hare, ya lalata hanyoyin samun abinci, ta ruguza ilimi, ta kuma rusa amincewar jama’a ga gwamnati.
"Dole ne mu ɗauki tsari mai faɗi da kuma haɗin kai,” inda ya jaddada buƙatar adalci, haɗin kai da mutunta haƙƙin ɗan adam.
Uba Sani ya samu goyon baya daga NCTC
Shugaban cibiyar yaki da ta'addanci NCTC, wacce da hadin gwiwarta aka shirya taron, Adamu Laka, ya maimaita maganar Gwamna Uba Sani.
Ya lissafo rikicin kan iyaka, rikice-rikicen da sauyin yanayi ya haifar, da kuma raunin shugabanci a matsayin manyan abubuwan da ke ƙara tabarbarewar tsaro.

Source: Twitter
A nasa ɓangaren, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na PAVE, Jaiye Gaskiya, ya jaddada bukatar sakar wa kananan hukumomi mara su ci gashin kansu.
Ya ce gudanar da harkokin gwamnati daga tushe ma'ana kananan hukumomi shi ne abin da zai iya magance matsalolin jama'a, cewar rahoton The Cable.
Kamar sauran jihohin Arewacin Yamma, Kaduna ma ta shafe shekaru tana fama da matsalolin ’yan bindiga da kuma yaɗuwar ta’addancin Boko Haram daga Arewa maso Gabas.
Gwamna ya karyata zancen biyan 'yan bindiga kudi
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan jihar, Uba Sani, ya ƙaryata zargin da ake yi masa na biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda domin samun zaman lafiya.
Uba Sani ya tuna cewa lokacin da ya hau kujerar mulki, akwai masu zargin shi da kokarin sulhu ta hanyar biyan kudi ga ‘yan bindiga domin magance matsalar tsaro.
Gwamnan ya ce babu ƙamshin gaskiya a zargin, kuma a matsayinsa na mai son jama'arsa da zaman lafiya, ba zai biye wa ƴan ta'adda ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


