Jami'ai da Muƙarraban Abba da Suka Jawowa Gwamnatin Kano Magana a Shekaru 2
A cikin shekara biyu da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hau karagar mulki a jihar Kano, wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatinsa sun jawo cece-kuce da suka daga jama’a da ‘yan adawa.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Daga shekarar 2023 zuwa yau, akalla jami’an gwamnati hudu sun shiga sabani ko zargi da ya janyo tambayoyi kan nagartar tafiyar da mulki a gwamnatin NNPP ta Kano.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattara jerin manyan abubuwan da suka ja hankali a wannan lokaci:
1. Namadi ya ja wa gwamnatin Abba magana
Kwamishinan sufuri na jihar Kano, Ibrahim Namadi, ya jawo cece-kuce bayan da aka zarge shi da karɓar cin hanci domin bailin fitaccen ɗan safarar miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Ɗanwawu.

Kara karanta wannan
Dilan ƙwaya: Bayanai sun bulloƙo kan kwamishinan Kano, ana zargin ya karbi $30,000
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Namadi ne ya tsaya wa Ɗanwawu jingina, duk da cewa gwamnatin Kano ta sha alwashin yaki da safarar ƙwayoyi da ‘yan daba.

Source: Facebook
Daga baya rahotanni suka kara bayyana cewa hukumar DSS ce ta gudanar da bincike inda aka ce Namadi ya karɓi kuɗi har $30,000 daga hannun Ɗanwawu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin bincike domin nazarin al’amarin, amma har zuwa yanzu babu sabon mataki da gwamnatin ta sanar game da sakamakon binciken da aka ruwaito DSS ta yi a kan kwamishinan.
2. Yadda Muhyi ya jawo magana ga gwamnatin Abba
Tsohon shugaban hukumar karɓar korafe-korafe ta jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya shiga sabani da wasu jami’an gwamnati bayan wani bidiyo da ya nuna yadda ya masu kaca-kaca kan rushe allon tallan shagon Rahama Sa’idu.
Rahama, fitacciyar ‘yar TikTok a Kano, ta kai ƙorafi ga hukumar da Muhyi ke jagoranta bayan jami’an KNUPDA sun rushe allon da ke bakin shagon ta.

Source: Facebook
Muhyi ya tsawatarwa jami’an hukumar cikin fushi, abin da ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta.
Daga baya, a wata hira da DCL Hausa, ya musanta cewa yana da wata alaka ta musamman da Rahama, yana mai cewa ya tsaya ne kan gaskiya.
3. Zargin tsohon CoS da karkatar da tallafin shinkafa
Shehu Sagagi, tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano, ya fuskanci zargi a shekarar 2024 bisa rawar da aka ce ya taka wajen karkatar da tallafin shinkafar da gwamnatin tarayya ta raba.
Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta Kano ce ta fara binciken, inda aka gano cewa wasu buhunan shinkafar da aka tanadar don rabawa jama’a sun sauka a makarantar Islamiyya mallakin Sagagi.

Source: Facebook
Duk da haka, Sagagi ya karyata zargin, yana cewa shinkafar da aka samu a makarantar tasa ya tallafi ne da wasu suka ba shi don ciyar da dalibai.
Sai dai jam’iyyar APC a Kano ta matsa lamba cewa dole ne a gudanar da cikakken bincike, kuma daga baya gwamnatin Kano ta sauke Sagagi daga mukaminsa.

Kara karanta wannan
Bayan Muhuyi ya sauka, Gwamna Abba ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano
4. Kano: Zargin tsohon SSG da ya jawo cece-kuce
Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi, ya shiga sabani da jam’iyyarsa ta NNPP bayan zargin cewa yana kokarin hana biyayya ga jagoran jam’iyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
An zarge shi da daukar nauyin gangamin “Abba tsaya da kafarka”, lamarin da ya jawo NNPP ta dakatar da shi.
Daga baya gwamnatin Abba ta bayyana cewa an kore shi daga mukamin SSG bisa dalilan rashin lafiya.
A cikin watan Janairu 2025, Baffa Bichi ya bayyana cewa zai fito da gaskiya a kan masu cin amanar mutanen Kano.
Ya ce:
“Allah ya hada mu da wasu mutanen da ba su da gaskiya, kuma lokaci na zuwa da za mu fallasa su. Ba su da abin da ya wuce yaudara da cin amanar jama’a."
Ya gode wa al’ummar Bichi bisa goyon bayansu, yana mai cewa za su ji daga gare shi nan ba da jima wa ba.
Abba: Jami'yyar NNPP ta soki PDP

Kara karanta wannan
ADC: El Rufai da manyan ƴan siyasar Kaduna da suka fice daga PDP, APC, suka shiga haɗaka
A baya, kun ji Shugaban jam’iyyar NNPP a Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya bayyana cewa babu wata farfaɗowa da jam’iyyar PDP ke yi a jihar.
Dungurawa ya bayyana hakan ne a yayin da yake martani ga sukar da ‘yan adawa ke yi wa yadda ake gudanar da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya ce duk da suna sukar gwamnatin yanzu, ba su da wani abin kirki da za su nuna daga shekarun da suka yi suna mulki a jihar na ci gaban jama'a.
Asali: Legit.ng
