Tirkashi: Malaman Makaranta Za Su Tsunduma Yajin Aiki a Kaduna, Sun Sanya Lokaci
- Ƙungiyar malaman NUT a Kaduna ta ce za ta shiga yajin aiki idan gwamnati ta gaza biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000 nan da Agusta
- Shugaban NUT, Ibrahim Dalhatu, ya ce malamai da ma’aikatan kananan hukumomi sun shafe watanni ba tare da samun sabon albashi ba
- Yayin da tuni wasu jihohi suka fara biyan sabon albashi, NUT ta ce ta fahimci gwamnatin Kaduna ba da ta damu da jin dadin malamai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Ƙungiyar malaman makaranta ta Najeriya (NUT) reshen Kaduna ta yi barazanar dakatar da koyarwa a makarantun jihar.
A cewar NUT-Kaduna, za ta rufe makarantu idan gwamnatin jihar ta gaza fara biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga malamai nan da watan Agusta, 2025.

Source: Twitter
Malamai za su tsunduma yajin aiki a Kaduna
Shugaban ƙungiyar NUT na jihar Kaduna, Ibrahim Dalhatu, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da jaridar Punch, inda ya ce gwamnati ta nuna ba ta damu da jin daɗin malamai ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalhatu ya ce:
“Idan suka ci amanar mu, ba mu da wani zaɓi illa fara yajin aiki na sai baba-ta-gani. Idan ba mu shiga yajin aiki ba, ba za su saurare mu ba.”
Ya ce malamai da ma’aikatan da ke karɓar albashi daga asusun ƙananan hukumomi sun gaza amfana da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi.
Jihar Kaduna ba ta fara biyan N70000 ba
Legit Hausa ta rahoto cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa dokar sabon mafi karancin albashi na N70,000 hannu tun ranar 29 ga Mayu, 2024.
Duk da cewa wasu jihohi kamar Zamfara, Lagos da Oyo sun fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi, jihar Kaduna ba ta fara ba, yayin da jihar Gombe ke jiran bayanai daga NLC.
Sai dai, wata sanarwar gwamnatin Kaduna ta nuna cewa Gwamna Uba Sani ya ce tuni ya fara biyan sabon albashin, inda ya ce babu wani ma'aikacin Kaduna da ke karbar kasa da N70,000.
Dalhatu ya bayyana cewa an cimma matsaya a wani zama da jami’an gwamnati da masu gudanar da tantance ma’aikata cewa duk wanda bai halarci tantancewar ba, za a dakatar da albashinsa.

Source: Facebook
Babu sabon albashi duk da tantance malamai
Ya kuma ƙara da cewa an riga an kammala kimanin kashi 80 zuwa 90 na aikin tantancewar ta hanyar fasahar zamani, amma za a ba wadanda suka rasa dama su sake gabatar da kansu.
Shugaban ƙungiyar ya zargi gwamnatin jihar Kaduna da nuna rashin kulawa da walwalar malamai, yana mai cewa sai da matsin lamba ta hanyar yajin aiki gwamnati za ta fara ɗaukar lamarin da muhimmanci.
“Yanzu haka dai gwamnati ba ta da niyyar biyan mu sabon mafi ƙarancin albashi.”
- Ibrahim Dalhatu.
Uba Sani ya fara biyan sabon mafi karancin albashi
Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Uba Sani ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin N72,000 da ta yiwa ma'aikatan Kaduna alkawari a Oktobar 2024.
Sanarwa daga babban mataimaki ga Gwamna Uba Sani kan sababbin kafofin sadarwa, ta ce an fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashin daga Nuwamban 2024.
Gwamnatin jihar ta bukaci ma'aikatan Kaduna da su hanzarta kai koke ofishin babban akawun jihar idan sun ga gibi a albashin ko kuma ba su ga karin kudin ba.
Asali: Legit.ng

