Gwamnatin Kaduna Ta Kori Malamai 2,357 Daga Aiki Ciki Har Da Shugaban Kungiyar Malamai NUT

Gwamnatin Kaduna Ta Kori Malamai 2,357 Daga Aiki Ciki Har Da Shugaban Kungiyar Malamai NUT

  • Hukumar Ilimi Bai Daya ta Jihar Kaduna (KADSUBEB) ta ce ta kori malaman makaranta 2,357 a jihar saboda faduwar jarrabawar da ta shirya musu
  • Mai magana da yawun hukumar, Hauwa Mohammed ne ta sanar da hakan tana mai cewa tun Disambar 2021 aka shirya jarrabawar
  • A martaninsa, Shugaban NUT na Jihar Kaduna, Ibrahim Dalhatu, ya yi watsi da jarabawar inda ya bayyana shi a matsayin wanda aka yi ba bisa ka'ida ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kaduna - Hukumar Ilimi Bai Daya na Jihar Kaduna, KADSUBEB, ta ce ta kori malamai 2,357 wadanda suka fadi jarrabawar cancanta da aka gudanar a baya-bayan nan, rahoton Vanguard.

Mai magana da yawun hukumar, Mrs Hauwa Mohammed cikin wata sanar da ta fitar, a ranar Lahadi a Kaduna ta ce hukumar ta yi wa fiye da malamai 300000 gwajin cancantar a watan Disambar 2021.

Malamai a aji.
Gwamnatin Kaduna Ta Kori Malamai 2,357 Daga Aiki, Jami'i. Hoto: @Vanguardngr.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta ce an kori malamai 2,192 na frimari ciki har da shugaban kungiyar malamai na kasa, NUT, Mr Audu Amba, saboda kin rubuta jarrabawar ta cancanta.

Ta ce an sallami malamai 165 cikin 27662 da suka rubuta jarrabawar saboda ba su ci ba.

Idan za a iya tunawa gwamnatin a 2018 ta sallami malamai 21,780 wadanda suka fadi jarrabawar, ta maye gurbinsu da wasu sabbin malamai 25,000 da aka yi wa gwajin sosai.

A watan Disambar 2021, hukumar ta kuma sallami malamai 233 kan malakar takardun kammala karatu na bogi.

"Bisa tsarin gwamnatin na cigaba da yi wa malamai gwaji don tabbatar da bawa daliban Kaduna ingantaccen ilimi, KADSUBEB ta sake yin wani gwajin cacanta ga malamai a watan Disambar 2021.
"Dukkan malamai da suka ci kasa da kashi 40 cikin 100 ba a bukatarsu kuma an sallame su saboda rashin kwazonsu a jarrabawar.

"Malamai da suka ci kashi 75 cikin 100 da fiye suna suka ci jarrabawar kuma za su tafi kwasa-kwasai na jagoranci da kula da makarantu," in ji ta.

A cewarta, malamai da suka cancanta za a saka su a tsarin bawa kwararrun malamai horaswa ta TPD don inganta ayyukansu.

Mohammed ta ce malamai da suka ci kashi 40 zuwa 74 cikin 100 ba su cika maki mafi karanci ba, amma za a sake basu wani damar su habbaka aikinsu.

Hukumar ta ce ta fara shirin bawa malaman horaswa da kara sanin makamashin aiki ne karkashin shirin TPD da taimakon gwamnatin jiha da abokan cigaba.

Martanin kungiyar malamai NUT

Shugaban NUT na Kaduna, Mr Ibrahim Dalhatu ya yi watsi da gwajin sanin makamashin aiki da aka yi da korar ma'aikatan yana mai cewa 'ya saba doka'.

Dalhatu ya ce kungiyar ta tafi kotu an kuma bada umurnin kada gwamnatin ta yi jarrabawar amma duk da hakan ta karya doka ta yi gwajin.

Ya tunatar da cewa kungiyar ta umurci malaman kada su rubuta jarrabawar bayan sun gano cewa za a yi ne da nufin korar su.

Da aka tuntube shi, shugaban NUT na kasa ya ce ya san da maganan, ya kara da cea kwamitin koli na kungiyar za ta zauna ranar Laraba, 22 ga watan Yuni ta cimma matsaya.

Legit Hausa ta tuntubi wata cikin malaman frimare a Kaduna don jin ra'ayinta game da jarabawar da korar malaman.

Malaman da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce korar abokan aikin nata bai mata dadi ba duk da bai shafe ta ba, tana mai cewa akwai alaman tambaya kan jarabawar don adadin mutanen da suka fadi.

"Akwai alamar tambaya kan jarrabawar, gaskiya adadin malaman da suka fadi ya yi yawa, ina ganin dai ana son rage ma'aikatan ne kawai aka bijiro da jarabawar.

"Idan an sallami wadanda ke karbar albashi mai kauri, wadanda za a dauka albashinsu ba zai kai na tsaffin ba," in ji ta.

An Rage Wa Wasu Farfesoshi Uku Mukami a Jami'ar Adamawa

A wani rahoton, Jami'ar Modibbo Adama ta Jihar Adamawa, MAU, ta rage wa wasu farfesoshi uku mukami saboda samunsu da laifuka masu alaka da karatu, Daily Trust ta rahoto.

Mataimakin shugaban jami'ar, bangaren mulki, Farfesa Muhammad Ja'afaru, ne ya sanar da hakan a bikin cika shekara uku na Farfesa Abdullahi Tukur, Shugaban MAU, a ranar Asabar a Yola.

Ya ce an mika batun ga sashin hukunta masu laifi a jami'ar kuma aka amince da rage wa malaman da abin ya shafa mukami.

Asali: Legit.ng

Online view pixel