NPower da Shirye Shirye 6 da Buhari Ya Kirkiro don Canza Rayuwar Talakan Najeriya

NPower da Shirye Shirye 6 da Buhari Ya Kirkiro don Canza Rayuwar Talakan Najeriya

  • Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kirkiro shirye-shirye karkashin NSIP domin tsamo 'yan Najeriya daga talauci da rashin aikin yi
  • Buhari ya kashe sama da Naira tiriliyan 2 daga 2016 zuwa 2022 a wajen aiwatar a shirye-shiryen N-Power, GEEP da CCT da sauransu
  • A rahoton nan, Legit Hausa ta yi bayani kan abin da ya jawo shirye-shiryen Buhari bakwai suka lalace da gaza azurta talakan Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Daga 2015 zuwa 2023, gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta jajirce wajen yaki da talauci da rashin aikin yi ta hanyar shirin zuba jari na jama’a (NSIP).

Buhari ya kirkiri wadannan shirye shirye domin karfafa al'umma, da ba su hanyar dogaro da kai, la'akari da cewa fiye da mutane miliyan 133 ke rayuwa cikin talauci a 2022.

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da bayyana ayyukan alheran Buhari, Malami faɗI abin da ya sani

Muhammadu Buhari ya kirkiro da shirye-shirye da dama domin tsamo 'yan Najeriya daga talauci
Muhammadu Buhari, shugaban kasar Najeriya daga 2015 zuwa 2025. Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

An kashe fiye da Naira tiriliyan 3.5 wajen tallafawa matasa, mata, manoma, da kananan ‘yan kasuwa ta hanyar ba su tallafin kudi, horaswa, inji wani bincike a Research Gate.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirye-shiryen Buhari da kudin da suka ci

Gwamnatin Buhari ta bayyana cewa ta zuba sama da Naira tiriliyan 1.3 a cikin shekaru 7 daga 2016 zuwa 2022 domin tallafawa rayuwar marasa galihu ta hanyar shirin NSIP.

Shirye-shiryen sun hada da N-Power, GEEP, NHGSFP, Conditional Cash Transfer (CCT) da kuma Independent Monitors (IM).

Wata makala da aka wallafa a shafin Cibiyar Lafiya Ta Kasa (NHI) ya rahoto tsohuwar ministar ma'aikaar jinkai da yaki da talauci, Zainab Farouq ta bayyana cewa:

  • An kashe N890.7bn a kan N-Power,
  • N246bn a kan CCT,
  • N17.6bn a kan GEEP,
  • N2.7m a kan IM,
  • N200.9bn kuma a kan shirin ciyar da ɗalibai (NHGSFP).

Ta ce ma’aikatar ta kai tallafi kai tsaye ga mutane sama da miliyan 15 da iyalansu.

Kara karanta wannan

'Da yanzu an mutu,' Tsohon minista ya fadi gatan da Buhari ya yiwa 'yan Najerya

Cikakken bayani ya nuna cewa:

  • Dalibai miliyan 9.9 aka ciyar a jihohi 36 da Abuja,
  • Matasa miliyan 3 sun ci gajiyar N-Power, daga ciki miliyan 1 na karɓar N30,000 kowanne wata,
  • Mutane 185,919 sun ci gajiyar GEEP,
  • Marasa galihu miliyan 1.9 sun karɓi N5,000 a kowane wata ta CCT,
  • Mutane 355,000 kuma sun samu tallafin N20,000.

Matsalolin da shirye-shiryen Buhari suka samu

Amma duk da haka, an samu cikas a shirye-shiryen, saboda cin hanci, rashin aiwatarwa, da yadda masu cin gajiyar shirin suka yi amfani da albarkatu ba bisa ka’ida ba.

A cikin wannan rahoton, Legit Hausa ta yi bayani dalla-dalla kan manyan shirye-shirye shida da Buhari ya kirkiro don canja rayuwar talakan Najeriya a lokacin mulkinsa.

Mun kawo wannan rahoto ne matsayin waiwaye ga irin ayyukan tsohon shugaban kasar, bayan rasuwarsa a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025 a wani asibitin London.

Ga jerin shirye-shiryen Buhari a kasa:

Matasa miliyan 3 ne suka ci gajiyar shirin N-Power, daga ciki miliyan 1 na karbar N30,000 duk wata.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo tare da matasan da suka ci gajiyar N-Power. Hoto: @npower_ng
Source: Twitter

1. Shirin N‑Power

Bayani game da shirin:

Kara karanta wannan

Bidiyo: Cikin hawaye, Fatima Buhari ta isa Daura inda za a binne gawar mahaifinta

An kaddamar da N‑Power a 2016 don samar wa matasa masu neman aiki ƙwarewa, da kuma tallafin kudi, inji rahoton Punch.

An dauki matasa 500,000 masu shekaru tsakanin shekarun 18–35 aiki, inda ake basu ₦30,000 duk wata tare da ba su horo a fannin ilimi, noma, da kiwon lafiya.

Gwamnatin Buhari ta bullo da shirin N-Power da niyyar baiwa matasa ilimi da kwarewar da suke bukata don kawo sauyi a garuruwansu, da kuma hana su zaman banza.

Zuwa 2022, akalla matasa miliyan daya ne aka ce sun shiga shirin, kuma an tura su koyarwa a makarantun firamare, tallafa wa manoma, ko aiki a cibiyoyin kiwon lafiya.

Sanadin rashin nasarar shirin:

Tun a tashin farko aka fara samun tangarda a shafin yanar gizon shiga shirin N-Power. Sannan an samu jinkirin biyan kudin tallafi, wanda ya sa wasu matasa ke tunanin an watsar da su ne.

Jaridar BluePrint ta rahoto cewa shirin N-Power da aka ƙaddamar a 2016 don rage rashin aikin yi bai cimma burinsa na samar da ingantaccen aikin yi ga matasa ba.

Kara karanta wannan

Mutanen Daura sun fadi yadda Buhari ya rayu a tsakaninsu bayan sauka a mulki

Rashin isassun kayan aiki, horo da tsarin tallafawa ya sanya yawancin matasa suka gaza samun aiki na dogon lokaci a fannonin noma, lafiya da ilimi.

An danganta shirin N-Power da wasu manyan laifukan cin hanci da suka hada da karkatar da kudade da kuma rashin biyan masu amfana da shirin hakkokinsu.

Wasu daga cikin matsalolin da aka gano sun hada da rajistar karya da kuma karɓar albashi daga wadanda ba su halarci aikin ba.

Gwamnatin Buhari ta ce ƙananan manoma miliyan 4.8 sun amfana da tallafin shirin Anchor Borrowers.
Muhammadu Buhari, gwamnan CBN da wasu jami'an gwamnati wajen baje kolin dalar shinkafar Anchor Borrowers. Hoto: @KOKUNSANI
Source: Twitter

2. Shirin Anchor Borrowers

Bayani game da shirin:

An kaddamar da wannan shiri a 2015 ta hannun CBN domin taimakawa kananan manoma, ta hanyar ba su rance, iri, da taki don noma shinkafa da masara, inji rahoton bankin.

Buhari ya bullo da shirin ne da nufin bunkasa tsarin samar da abinci, kara ayyukan yi a karkara, da rage dogaro da shigo da kayayyaki.

Rahoton Channels TV ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta ce ta kashe akalla Naira tiriliyan 1.1 domin tallafawa manoma miliyan 4.67 a karkashin shirin.

Sanadin rashin nasarar shirin:

Shirin Anchor Borrowers ya fuskanci matsaloli masu yawa da suka haifar da gazawa wajen cimma burin samar da isasshen abinci da bunkasa noma.

Kara karanta wannan

Mamman Daura: Bayanai sun fara fito wa kan rasuwar Muhammadu Buhari

Babban kalubale sun hada da rashin kulawar gwamnati, kuskuren manoma wajen tafiyar da rancen da suka samu, da kuma rashin tsarin kulawa mai kyau.

Matsalolin tsaro da sauyin yanayi sun kara dagula lamarin, inda galibin manoma suka ki biyan bashin da suka karba daga shirin.

An kuma zargi wasu ma'aikatan gwamnati da karkatar da kudade, iri da kayan gona da aka ware domin wannan shiri, sannan wasu manoman sun ki dawo da rancen da aka basu.

An kuma rahoto cewa wasu manoman sun rika sayar da iri da sauran kayan noma da aka ba su domin su ci abinci, sakamako yunwa da ake fama da ita a kasar.

A Yunin 2025, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majalisar wakilai ta fara bincike kan yadda aka kashe Naira tiriliyan 1.1 na shirin Anchor Borrowers bayan an yi zargin badakala a shirin.

Gwamnatin Buhari ta kawo shirin GEEP wanda ya hada da TraderMoni domin tallafawa kananan 'yan kasuwa
Lokacin da ake kaddamar da shirin TraderMoni a wani sashe na Najeriya. Hoto: @ProfOsinbajo
Source: UGC

3. Shirin GEEP

Bayani game da shirin:

An kaddamar da GEEP a 2016 don tallafawa kananan ‘yan kasuwa, musamman mata, a cewar rahoton bankin BOI.

A karkashin tsarin GEEP ne aka bullo da shirin TraderMoni, MarketMoni da FarmerMoni, domin bunkasa tattalin arzikin ƙasa ta hanyar bai wa kananan manoma da ‘yan kasuwa rance da sauƙin biyansa.

Kara karanta wannan

'Akwai alaƙa mai kyau tsakaninsu': Bidiyon haɗuwar Buhari da Tinubu na ƙarshe

Shirin ya bai wa kananan ‘yan kasuwa damar faɗaɗa harkokinsu ta hanyar ba su rancen N10,000. Ana biyan rancen a hankali cikin watanni shida.

Bayan an biya rancen N10,000 a cikin wa’adin da aka tsara, ana ba mai cin gajiyar shirin damar samun rance mai girma daga N15,000 zuwa N300,000.

Zuwa 2019, mutane sama da 1.7 miliyan suka amfana da shirin TraderMoni kamar yadda bayanai daga shafin shirin na intanet suka nuna.

Sanadin rashin nasarar shirin:

Kokarin gwamnatin tarayya na raba fiye da Naira biliyan 12 ga mutane miliyan 1.2 a shirin GEEP bai rage yawan talakawa a Najeriya ba.

Binciken BusinessDay ya gano cewa masu cin gajiyar rancen ba sa ci gaba da amfani da asusun bankinsu bayan sun cire N10,000.

Ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Najeriya ta ce shirin bai kai ga matakin ƙasa ba, kuma bai taimaka wa masu sana’o’i yadda ya kamata ba.

Duk da an fitar da karin Naira biliyan 36.6, da dama daga cikin ‘yan kasuwa a fadin ƙasar ba su samu wannan tallafi ba, wadanda aka ba sun ki mayar da bashin.

Kara karanta wannan

Sun kwanta dama: Buhari, Dantata da wasu manyan ƴan Najeriya da suka rasu a 2025

Rashin sa ido ya sa wasu 'yan kasuwar sun ki yin amfani da kudin wajen inganta kasuwancinsu, wasu sun yi amfani da kuɗin don bukatun kansu.

Gwamnatin Buhari ta kaddamar da shirin CCT domin tallafawa iyalan da ke fama da talauci
Tsohuwar ministar jin-kai, Sadiya Farouq tana raba tallafin N5,000 ga iyalai karkashin shirin CCT. Hoto: @Sadiya_farouq
Source: Twitter

4. Shirin Conditional Cash Transfer (CCT)

Bayani game da shirin:

CCT wani ɓangare ne na NSIP da aka kaddamar domin tallafawa iyalan da suka fi fama da talauci, ta hanyar ba su tallafin N5,000 a kowane wata don ciyar da kansu, kula da lafiya da kuma ilimin yara.

Gwamnatin Buhari ta yi niyyar amfani da wannan shiri domin ba talakawa da marasa galihu damar rayuwa cikin 'yar kwanciyar hankali da tunanin makoma mai kyau.

Kafin shekarar 2023, an rahoto cewa mutane miliyan 2.3 ne suka amfana da wannan shiri domin bayan annobar COVID-19, aka faɗaɗa rajistar jama’a.

Sanadin rashin nasarar shirin:

Matsalar farko da shirin ya fuskanta shi ne yawan kudin da ake bayarwa bai dace da hauhawar farashin kayayyaki a lokacin ba.

Yayin da wasu ke amfani da kuɗin don ci gaba da rayuwa ba tare da dogaro da kai ba, a hannu daya kuma an ce cin hanci da rashin gaskiya sun rage tasirin shirin.

Kara karanta wannan

Kalaman Buhari 12 da suka yi amo a Najeriya kuma za su sa a rika tunawa da shi

Binciken Research Gate ya nuna cewa shirin ya fuskanci ƙalubale da dama kamar rashin daidaitaccen tantancewa, rashin cikakken biyan kuɗi, rashawa da rashin ingantaccen sa ido.

An kuma zargi wasu jami'an gwamnati da ke kula da shirin da karkatar da kudin shirin, wanda ya sa shirin bai kai ga kowane gida ba.

An rahoto cewa majalisar wakilai ta shirya bincike kan shirin Conditional Cash Transfer (CCT), kan zargin cewa ana karbar N50,00 daga wadanda za su ci gajiyar shirin.

Gwamnatin Buhari ta kaddamar da shirin P-YES a 2020 domin rage zaman banza tsakanin matasa, ta hanyar basu kayan aiki, horo, da tallafi
Shugaba Buhari lokacin da ya kaddamar da shirin P-Yes tare da baje kolin kayayyakin da za a rarraba a Abuja. Hoto: @NigeriaGov
Source: Twitter

5. Shirin matasa na P-YES

Game da shirin:

Gwamnatin Buhari ta kaddamar da shirin P-YES a 2020 domin farfado da burin matasa da ke fama da rashin aikin yi, ta hanyar basu kayan aiki, horo, da tallafi domin fara sana’o’i a bangaren noma, fasaha, da sana’o’in hannu.

Shirin ya zo a daidai lokacin da rashin aikin yi a tsakanin matasa ya kai kashi 33.4% a 2020, inda aka sa ran matasa za su koma masu dogaro da kansu.

Bayani daga shafin P-Yes na intanet ya nuna cewa, an tsara shirin ne domin tallafawa aƙalla mutane 774,000 a faɗin Najeriya, da nufin bayar da tallafi ga mutum 1,000 a kowace ƙaramar hukuma.

Kara karanta wannan

Tuna Baya: Kalamai masu ratsa zuciya da Buhari ya faɗa kan ciwon da ke damunsa

Sanadin rashin nasarar shirin:

Akwai rahotanni na matasa da suka sayar da kayan aikin da aka ba su kamar babura da kekunan dinki don biyan bukatun kansu.

Rashin horo na gaskiya da rashin kulawa daga gwamnati sun hana shirin P-YES yin tasiri, yayin da matsalolin tattalin arziki kamar raunin Naira da hauhawar farashi suka hana nasarar shirin.

Wani babban kalubale na shirin shi ne rashin cikakken bayanai da raunanan cibiyoyi da za su tabbatar an gudanar da shirin ba tare da almundahana, son kai, damfara ko boye-boye ba ga matasa marasa aikin yi a Najeriya.

6. Shirin AGSMEIS

Game da shirin:

Gwamnatin tarayya ta kirkiro wannan shirin karkashin CBN domin karfafa manya, matsakaita da kananun 'yan kasuwa da kamfanonin noma.

Hakazalika shirin zai taimakawa masana’antu da sauran fannonin tattalin arziki, ta hanyar bayar da rance mai ƙarancin ruwa har zuwa Naira miliyan 3.

An bayar da fiye da Naira biliyan 150 zuwa 2022 domin kara ayyuka da rage talauci a kasar kamar yadda rahoton CBN ya bayyana.

Kara karanta wannan

Shugabannin duniya da suka fara ta'aziyyar Muhammadu Buhari

Sanadin rashin nasarar shirin:

Wasu sun karkatar da rancen zuwa biyan bashi ko bukatunsu na yau da kullum maimakon amfani da shi wajen bunƙasa kasuwanci.

An rahoto cewa da yawa daga wadanda suka amfana da shirin sun ki dawo da rancen kudin da aka basu, wanda ya sa shirin ya gaza ci gaba.

An kuma yi zargin cewa wasu na samun damar shiga ne saboda suna da alaƙa da manya yayin da rashin kulawa da karancin biyan bashi sun takaita tasirin shirin.

Gwamnatin Buhari ya kirkiro da shirin ciyar da dalibai abinci domin rage yawan yara marasa zuwa makaranta
Wasu daga cikin yara 'yan aji 1 zuwa 3 da gwamnati ke ciyarwa karkashin shirin HGSFP. Hoto: @BashirAhmaad
Source: Twitter

7. Shirin ciyar da dalibai - HGSF

Bayani game da shirin:

Buhari ya kirkiro da shirin ciyar da dalibai a makarantu don samar da abinci mai gina jiki da daidaitaccen sinadari ga yara kimanin miliyan 5.5 daga aji 1 zuwa 3.

Manufar shirin ita ce karfafa rajistar yara a makarantun firamare da rage yawan barin makaranta, wanda ya kai sama da kashi 30.

Rashin wadataccen abinci da talauci na daga cikin manyan dalilan barin makaranta, don haka aka tsara wannan shiri ne don magance bukatar asali ta yara da kuma samar musu da abincin da zai ba su kuzarin koyo.

Kara karanta wannan

Garba shehu: Yadda ake shirin dawo da gawar Muhammadu Buhari zuwa Daura

Fiye da mata masu girki 44,000 ne ke cikin shirin, inda ake ciyar da sama da dalibai miliyan 4 a jihohi 30 na Najeriya.

Dalilin rashin nasarar shirin:

Rahoton jaridar The Guardian ya nuna cewa rashin tsari mai kyau da kuma cin hanci da rashawa sun lalata shirin ciyar da ɗalibai da aka kashewa sama da Naira biliyan 200.

Bayan wasu shekaru ana gudanar da shirin, matsaloli da dama da suka turnuke shi sun tilasta gwamnatin Buhari dakatar da shi.

Yunkurin Shugaba Bola Tinubu na farfado da shirin ya gamu da jerin badakalar da suka sa aka dakatar da dukkan shirye-shiryen tallafin gwamnati.

Gatan da Buhari ya yiwa 'yan Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon ministan ilimi ya ce tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya ki cire tallafin man fetur don kare 'yan Najeriya daga mutuwa.

Chukwuemeka Nwajiuba ya jaddada cewa gwamnatinsa ta daidaita manyan sassan tattalin arziki duk da matsin da aka samu a duniya.

Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya farfado sau biyu kuma ya tsira daga COVID-19 karkashin Buhari, sannan ya rike Naira kasa da N500/$1.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com