Tsadar Abinci: CBN Ta Gano Mafita Kan Tsadar Masara, Za Ta Tallafawa 'Yan Kasa

Tsadar Abinci: CBN Ta Gano Mafita Kan Tsadar Masara, Za Ta Tallafawa 'Yan Kasa

  • Babban Bankin Najeriya ya bayyana kudurinsa na karya farashin masara a Najeriya don talakawa
  • Bankin ya ce ya za bi wasu kamfanoni 12 da za ta sayarwa tan dubu 50 saboda farashin ya sauka
  • Bankin a baya ya bayyana kudurinsa na amincewa da sakin tan miliyan tara na shinkafa a kasar

Babban Bankin Najeriya (CBN), a jiya Litinin, 28 ga watan Yuni, ya ce ya amince da sakin masara kimanin tan dubu 50 ga manyan masu samar da ita 12, karkashin dabarun samar da masara ta SMR da shirin Anchor Borrowers (ABP), Vanguard ta ruwaito.

Wannan shawarar, a cewar bankin, ita ce tsakaitawa da sarrafa farashin masara a kasuwannin Najeriya tare da dakile ayyukan 'yan handama da nufin tara masarar saboda su haifar da karancin abinci.

Wadanda zasu ci gajiyar yunkurin sun hada da Premier Flour Mills, Crown-Olam, Grand Cereals, Animal Care, Amobyn da Hybrid Feeds.

KARANTA WANNAN: Obasanjo Ya Yi Gargadin Matsalar da Najeriya Za Ta Shiga Saboda Yawan Haihuwa

Tsadar Abinci: Bayan Karya Farashin Shinkafa, CBN Ta Samo Mafita Kan Na Masara
Masara a jikin totuwarta | Hoto: dw.com
Asali: UGC

Sauran sun hada da Obasanjo Farms, Zartech, Wacot, Sayeed Farms, Pandagri Novum da Premium Farms.

Da yake magana game da ci gaban, Daraktan, Sashin Sadarwa na CBN, Osita Nwanisobi ya bayyana kwarin gwiwar cewa hakan zai karya farashin masara, ya rage matsi a kasuwa, sannan a samar da farashin kai tsaye, ta yadda za a rage farashin kaji a kasar.

Hakazalika, ya bayyana cewa, bankin zai ci gaba da samar da tallafi ga manoma masara da masu sarrafa ta a fadin kasar a karkashin shirin Anchor Borrowers.

Shima da yake magana kan ci gaban, Shugaban kungiyar samar da Masara ta kasa (MAAN), Dakta Bello Abubakar, ya bukaci 'yan kasuwa da su daina amfani da gibin da ake samu wajen kara farashin hatsi a kasar.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa, manoma a Najeriya za su ci gaba da sayen kayayyakin yadda ya kamata.

Tsadar Abinci: CBN Ta Kawo Mafita, Za Ta Karya Farashin Shinkafa a Najeriya

A daya bangaren, a kokarinsu na samar da wadataccen abinci ga 'yan Najeriya tare da karya farashin shinkafa, Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya, sun fara batun kaddamar da sayar da tan miliyan tara na tallafin shinkafa ga masu sarrafata.

Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele yayin da yake kaddamar da shirin sayarwar da kuma fara noman rani a Kaduna ya ce, bankin a shirye yake ko yaushe don tallafawa harkar noma, The Nation ta ruwaito.

Ahmed Mohammed na CBN reshen jihar wanda ya wakilci gwamnan, ya ce shirin an shirya shi ne don sayar da shinkafar a kan farashi mai rahusa da nufin karya farashin don amfanin kowa a Najeriya da ma wasu kasashen.

KARANTA WANNAN: Kabilar Ijaw Ta Gargadi Buhari Kan Tamkawa Tsagerun Neja Delta da Ya Yi

Duk da tsawon tarihin Gurasa a Kano, 'yan Gurasa sun yi barazanar daina sana'ar

A wani labarin, Masoyan Gurasa, sanannen abinci ga mutan Kano, na iya shiga mawuyacin hali domin kuwa masu sarrafa shi suna barazanar daina samar da shi saboda hauhawar farashin garin fulawa; babban sinadari don samar da gurasa.

Gurasa shine burodin gargajiya wanda akafi sani a tsakanin mutanen Kano kuma ana siyar dashi a yankuna da yawa ciki da wajen babban birni.

Hakanan mutane a wasu jihohin arewacin suma suna gudanar da kasuwancinsa duk da cewa ba za su iya daidaita dandano da kimarsa da na jama'ar Kano ba kasancewarsa abinci mai daraja da dinbin tarihi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel