Zamu damke manoman da suka ki biyan bashin da muka basu, CBN

Zamu damke manoman da suka ki biyan bashin da muka basu, CBN

  • Shirin Anchor Borrowers Programme (ABP) na daya daga cikin tallafin da Gwamnati ta fito da su a 2015
  • Gwamnatin tarayya ta hannun bankin CBN ta bada bashin miliyoyin kudi ga manoma don inganta harkokinsu
  • Amma maimakon zuba kudaden a harkar noma, wasu manoman kara aure suka fara yi kuma yanzu sun gaza biya
  • Bankin CBN ya lashi takobin damke dukkan wadanda suka bi biyan bashin da aka basu

Babban bankin Najeriya CBN ya fara barazanar amfani da yan sanda wajen damke manoman da suka ki biyan bashin da suka karba karkashin shirin Anchor Borrowers Programme(ABP).

A 2015, Gwamnati ta baiwa manoman shinkafa da wasu tsirrai kudade don inganta aikin noma a Najeriya.

CBN yace ba zai cigaba da lamuntan abinda manoman ke yi na ganin kyauta aka basu kuma kuma duk wanda bai biya ba zai shiga komar hukuma.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi

Zamu damke manoman da suka ki biyan bashin da muka basu, CBN
Zamu damke manoman da suka ki biyan bashin da muka basu, CBN
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai jagoran shirin CBN na jihar Bauchi, Saladu Idris, ya bayyana hakan ga manema labarai a sakatariyar NUJ.

Idris ya bayyana cewa yawancin wadanda suka ki biyan bashin manoman Shinkafa ne, Nairametrics ta ruwaito.

Yace:

"Yawancin mutane sun biya, amma akwai wadanda basu biya ba. Mun tuntubi shugabannin kungiyoyin manoman shinkafa, sun bamu tabbacin cewa zasu tabbatar sun biya."
"Daga cikin yarjejeniyar shine zasu biya muddin suka girbi amfanin gona. Wadanda basu biya ba kuma zasu fuskanci ukubu. Za'a damkesu har sai sun biya."
"Wadanda suka biya kuma za'a kara musu bashi da kudi mafi yawa."

Jaridar Punch a Maris 2021 ta ruwaito cewa ana bin manoma bashin sama da N463 billion.

Rahoton yace tsakanin Nuwamba 2015 da Maris 2021, an baiwa manoma guda 3.04 million bashin N615.4 billion amma har yanzu N152.3 billion kadai aka biya ciki.

Kara karanta wannan

2023: Ta kacame tsakanin gwamnonin APC kan batun fitowa takarar Tinubu

CBN ya ba bankin Sterling damar aiki a matsayin bankin Muslunci a Najeriya

Babban bankin Najeriya (CBN) ya bukaci bankin Sterling Plc da ya ci gaba da aiwatar da shirinsa na gyarawa tare da gudanar da lasisinsa domin kirkirar tsarin mu'amala ba kudin ruwa.

Amincewar bisa ka'ida ce kuma karkashin amincewar tsarin CBN.

Sabon reshen na bankin Sterling da za a kira shi da Alternative Bank Limited zai kuma yi aiki a karkashin ka'idodin addinin Musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel