Shirin bayar da rance na CBN da babu ruwa zai bunkasa tattalin arziki - NSCIA

Shirin bayar da rance na CBN da babu ruwa zai bunkasa tattalin arziki - NSCIA

- Majalisar NSCIA ta yabawa babban bankin Nigeria (CBN) bisa kokarinsa na kawo rancen da ruwa a kansu

- NSCIA ta ce mafi akasarin Musulmai zasu gwammace ci gaba da zama a cikin talauci da dai su fuskanci ubangijinsu da laifin cin bashi mai kudin ruwa

- Majalisar ta roki CBN da ta samar da tsarin karbar bashin cikin sauki ta yadda talaka fitik zai amfana daga shirin

Majalisar koli ta gudanar da harkokin Musulunci ta Nigeria (NSCIA) ta yabawa babban bankin Nigeria (CBN) bisa kokarin kawo shirin bayar da rancen da ba a biyan kudin ruwa.

Wata sanarwa karkashin shugaban cibiyar, Sa'ad Abubakar, Sarkin Musulmi, ta ce shirye shiryen da ba kudin ruwa sun hada da shirin 'Anchor Borrowers Programme' (ABP).

Akwai kuma shirin bayar da rance don bunkasa masana'antu CIFI, Shirin bada rance ga kananu da matsakaitan 'yan kasuwa MSMEDF.

Da kuma shirin bada rance don bunkasa manyan masana'antu RSSF, da kuma shirin bayar da rance don bunkasa fannin kiwon lafiya.

Sanarwar, mai dauke da sa hannun mataimakin shugaba, Salisu Shehu, ta yi nuni da cewa cibiyar tana kallon ci gaban a matsayin hanyar bunkasa tattalin arzikin kasar.

Cibiyar NSCIA ta ce babban bankin Nigeria CBN ya saki wasu jadawalin ka'idoji da mutane zasu bi domin samun rancen kudade ba tare da sun biya da kudin ruwa ba.

KARANTA WANNAN: Muna da tabbaci: PDP zata samu nasara kan APC a zaben Ondo - Ekweremadu

Shirin bayar da rance na CBN da babu ruwa zai bunkasa tattalin arziki - NSCIA
Shirin bayar da rance na CBN da babu ruwa zai bunkasa tattalin arziki - NSCIA Source: Twitter
Asali: UGC

Yayin da take addu'ar tabbatar da tsare tsaren, NSCIA ta kuma jinjinawa CBN da gwamnatin tarayya na cimma irin wannan nasarar.

"Sama da shekaru masu yawa, 'yan Nigeria Musulmai sun kasance koma baya a bangaren bayar da rance saboda gudun kudin ruwan da ake sanyawa kusan kowanne shiri".

"Dole Musulmai su kaucewa kudin ruwa, haka zalika mafi akasarin Musulmai zasu gwammace ci gaba da zama a talauci da dai su fuskanci ubangijinsu da laifin cin kudin ruwa.

"Amma a bashin da babu kudin ruwa, to tabbas Musulmai zasu ci gajiyar ire iren wadannan shirye shirye, kusan kaso 60 ne zasu amfana.

"Abun lura a nan shine, idan bankin CBN ya samar da shirin, hakan zai ba bankin damar cimma kudirin kaso 80 na masu cin moriyar shirye shiryen bankin a 2020."

Cibiyar NSCIA bukaci bankin CBN da ya yi amfani da dukkanin hukumomi da kafofin watsa labarai don samun sanar shirye shiryen.

Da tallafin hukumar wayar da kai ta kasa, da shirye shiryen talabijin da rediyo, za a wayar da kan al'umma da kuma yadda za subi don cin gajiyar shirin.

"Ya kamata ace an samar da tsarin karbar bashin cikin sauki ta yadda talaka fitik zai amfana daga shirin," a cewarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng