N-Power: Fiye da 'yan Najeriya miliyan biyar sun nemi aikin wucin gadi

N-Power: Fiye da 'yan Najeriya miliyan biyar sun nemi aikin wucin gadi

Ma'aikatar jin kai, walwalar 'yan kasa da bayar da tallafi yayin annoba ta ce 'yan Najeriya miliyan 5,042,001 ne suka nemi aikin wucin gadi a karkashin tsarin tallafawa matasan da su ka kammala karatu amma ba su samu aiki ba; watau N-Power.

A ranar 9 ga watan Agusta ne ma'aikatar ta rufe shafin yanar gizo da ta bude domin daukan sabbin matasan da za su ci moriyar shirin N-Power a karkashin rukunin 'C'.

Za a dauki sabbin matasa bayan an yaye wasu matasan 500,000 da aka fara dauka a rukunin farko; 'A', da na biyu; 'B'.

A cikin wani jawabi da mai dauke da sa hannun Halima Oyelade, mai bayar da shawara a kan sadarwa a ma'aikatar, ta ce za a bayar da fifiko a kan mutane ma su bukata ta musamman yayin zaben matasan da za su moriyar shiri.

A cewar jawabin, shirin N-Power na daga cikin hanyoyin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai yi amfani da su wajen tsamo 'yan Najeriya miliyan 100 daga kangin fatara da talauci a cikin shekaru 10 ma su zuwa.

A ranar 26 ga watan Yuni ne ma'aikatar jin kai, walwalar 'yan kasa da bayar da tallafi yayin annoba ta bude shafin yanar gizo domin fara karbar bayanan ma su sha'awar samun gurbin cin moriyar shirin N-Power a rukunin 'C'.

Da farko ma'aikatar ta bayyana cewa za a rufe karbar bayanan ne a ranar 26 ga watan Yuli kafin daga bisani ta kara wa'adin mako biyu domin bawa matasa da yawa damar neman cin moriyar shiri.

N-Power: Fiye da 'yan Najeriya miliyan biyar sun nemi aikin wucin gadi
Sadiya Umar Farouq
Asali: Twitter

Ministar ma'aikatar, Sadiya Umar Farouq, ta bawa 'yan Najeriya tabbacin cewa za a yi adalci yayin zaben matasan da su ka cancanta su ci moriyar shirin.

DUBA WANNAN: Akwai hannun 'yan siyasa a rashin tsaron arewa - Gwamna Matawalle ya fasa kwai

Kazalika, ta bayar da tabbacin cewa ma'aikatarta za ta ke fitar da bayanai domin sanar da ma su nema da sauran jama'a halin da ake ciki a kowannen mataki.

Ministar ta kara da cewa an kirkiri shirin N-Power ne domin bawa matasan Najeriya damar koyon dabarun aiki da na kasuwanci domin su kasance ma su dogaro da kansu.

A cewar ministar, daukan sabbin jerin matasan zai taimakawa kasa wajen murmurewa daga matsin tattalin arziki da annobar korona ta haifar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel