CBN da NMfB Sun Fara Bibiyar Asusun Wadanda Suka Ci Bashin Banki Na Lokacin Korona, Suna Cire Kudi

CBN da NMfB Sun Fara Bibiyar Asusun Wadanda Suka Ci Bashin Banki Na Lokacin Korona, Suna Cire Kudi

  • Babban bankin Najeriya (CBN) da bankin NIRSAL sun fara karbar kudin da suka ba mutane da sunan bashin tallafin Korona
  • An ruwaito cewa, bankin ya fara cire kudi daga asusun wadanda yake bi bashi a ranar Juma'a 28 ga watan Oktoba
  • A nan gaba kadan, bankunan za su fara bibiyar wadanda suka ci bashin shirin TCF da kuma AGSMEIS

Babban bankin Najeriya (CBN) da kuma bankin NIRSAL sun fara karbo kudaden da suka ba 'yan Najeriya rance a 'yan shekarun baya.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, an fara karbo kudaden ne a ranar Juma'a 28 ga watan Oktoban 2022 ta hanyar amfani da lambar bankin bai daya na BVN.

CBN ya fara cire kudi daga asusun 'yan Najeriyan da suka ci bashin Korona
CBN da NMfB Sun Fara Bibiyar Asusun Wadanda Suka Ci Bashin Banki Na Lokacin Korona, Suna Cire Kudi | Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Wadanda za a fara karbo kudaden da suka ci nan gaba

Hakazalika, bankin na NIRSAL zai fara dawo da kudaden da 'yan Najeriya suka karba a lokacin Korona karkashin shirin TCF da kuma na 'yan kasuwa karkashin shirin AGSMEIS.

Kara karanta wannan

CBN Zai Dagargaza Naira Tiriliyan 6 Cikin Shekaru 8 a Mulkin Shugaba Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bankin CBN ya yi barazana ga duk wanda ya ci wannan bashi da cewa, nan ba da jimawa ba zai fara karbar kudinsa.

Hakazalika, tuni bankin ya daura wadanda suka ci rancen Korona na TCF da AGSMEIS a kan tsarin Global Standing Instruction (GSI) mai ba da damar cire kudi ta asusun kwastoma kai tsaye.

Wannan tsari na GSI zai ba bankuna daman cire kudin duk wanda ya ci bashin kai tsaye daga asusu, ko da kuwa asusu nawa ya mallaka.

Wadanda suka ci bashin Anchor Borrowers, tuni an fara cire kudi daga asusunsu na banki, inji rahotanni.

Yadda aka ba da bashin kudin Korona

A karkashin rancen Korona na TCF Household kadai, an ba mutane 639,197 bashin da ya kai N258.1bn yayin da aka ba ma'aikatu 112,291 bashin da ya kai N112.2bn.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

An ba mutane da dama akalla N250,000 zuwa N500,000 domin samun daman rage radadin annobar Korona da ta addabi mutane a 2020.

Wakilin Legit.ng Hausa ya tattauna da wani wanda ya ci gajiyar shirin, Muhammad Ibrahim kuma ma'aikacin banki, wanda ya bayyana yadda ya ji da aka ce za a biya kudin da aka bayar karkashin TCF.

A cewarsa:
"Mutane da yawa suna tsammanin cin banza daga gwamnati, amma ba haka bane, domin wallahi sai sun biya tun da banki ne ya ba da bashin.
"Na ji dadi da aka kawo tsarin biya cikin sauki, yana da kyau mutum ya zamana ya rabu da bashin dake kansa, wannan ya yi kyau sosai.
"Kuma idan ka duba, ba wai kudin za cire daga asusun mutum kai tsaye ba duka, dole kadan-kadan za a ke cirewa, to ba abin damuwa bane."

Sai dai, wata matar da ta ci gajiyar TCF, Fatima Abdullahi ta nuna damuwa da yadda ta samu labarin, inda tace tabbas akwai matsala.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu Ya Shigar da Karar Gwamnatin Buhari, Yana Neman a Biya Shi N100bn

A kalamanta:

"Ni da naje cikawa ce min aka yi ba rance bane, tallafi ne na gwamnati, yanzu kuma an ce za mu biya? Gaskiya ya kamata gwamnati ta duba ta yafe irin wadannan kudaden, abinci muka saya dasu a lokacin Korona. Ba juyawa muka yi ba, kuma har yanzu jari na bai wuce N4000 ba, to ina zan iya biyan kudin da ya kai N450,000?"

Dalilin Da Yasa CBN Zata Sauya Wasu Takardun Kudaden Najeriya

A wani yunkuri da ta sanar matsayin mataki na yaki da ayyukan ta’addanci, boye kudade da kuma yaki da kudin jabu, babban bankin Najeriya (CBN) ya ce zai fara rarraba sabbin takardun N100, N200, N500 da kuma takardar N1000 daga ranar 15 ga Disamba.

Gwamnan babban bankin kasa, CBN, Godwin Emefiele, wanda ya bayyana hakan a jiya yayin wani taron tattaunawa na musamman ya ce za a sake fasalin kudin Naira ne bayan amincewar gwamnatin tarayya, Daily Trust ta rahoto hakan.

Kara karanta wannan

Ministar Tattalin Arziki Ta Jero Sharuda 8 Game da Sababbin Kudin da Za a Buga

An gano cewa, duk da cewa mafi kyawun abin da ya fi dacewa a duniya shi ne manyan bankunasu sake tsarawa, samarwa da rarraba sababbin takardun kudin cikin gida a kowacce shekara 5-8, Naira ba a sake fasalin ba a cikin shekaru 20 da suka wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel