Gwamnatin Buhari Ta Bankado Makarantun Bogi 349 Dake Cin Gajiyar Shirin Ciyar da Dalbai a Nasarawa

Gwamnatin Buhari Ta Bankado Makarantun Bogi 349 Dake Cin Gajiyar Shirin Ciyar da Dalbai a Nasarawa

  • Akalla makarantu 349 ne aka gano babu su kwata-kwata a jihar Nasarawa, kuma suna cin gajiyar wani shirin gwamnati
  • Kwamitin duba da kididdiga na gwamnatin tarayya ya gano cewa, wasu daidaikun mutane ne ke cike aljihunsu da kudaden
  • An shaidawa gwamnan jihar Nasarawa abin da ke faruwa, kuma tuni ma'aikatar jin kai a Najeriya ta dauki mataki

Jihar Nasarawa - A karkashin shirin ciyar da 'yan makaranta na gwamnatin tarayya, an gano akalla makarantun bogi 349 a jihar Nasarawa dake cin gajiyar wannan shiri da aka yi don makarantun firamaren gwamnati.

Wannan batu na gano badakala na kunshe a cikin wani rahoton jaridar The Nation, kamar yadda Legit.ng Hausa ta tattaro.

Yadda aka gano makarantun bogi a jihar Nasarawa
Gwamnatin Buhari Ta Bankado Makarantun Bogi 349 Dake Cin Gajiyar Shirin Ciyar da Dalbai a Nasarawa | Hoto: 1049277976
Asali: UGC

Rahoton ya bayyana cewa, kudaden da gwamnati ta ware don ciyar da dalibai a wadannan makarantu da babu su sun fada aljihun wasu mahandama, inji kwamitin ma'aikatar jin kai karkashin Mallam Abdullahi Usman.

Kara karanta wannan

Wani Gwamna Ya Umurci Dalibai Da Ma’aikatan Gwamnatin Jiharsa Su Fara Sanya Kayan Gargajiya Ranar Juma’a

An shaidawa gwamna abin da ke faruwa

A cewar Usman a lokacin da yake bayyanawa gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule badakalar dake tattare da shirin a ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba, ya ce jihar na gab da fita daga jerin jihohin dake cin gajiyar shirin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa, tuni aka dakatar da ofishin tafiyar da shirin tare da maye gurbin jami'an dake kula dashi a jihar, rahoton Daily Trust.

A kalamansa:

"Bayan bincike cikin tsanaki, kwamitin ya gano cewa, akwai makarantun bogi 349, da wasu manya ke kunshe kudaden shirin a aljihunsu da sunan shirin ciyarwa."

Hakazalika, hadimin na ministar jin kai ya ce, manya a ma'aikatar dama sun nemi a cire Nasarawa daga jerin jihohin dake cin gajiyar shiri.

Akalla makarantun firamre 1,203 ne a tun farko aka dauki bayansu a jihar da sunan masu cin gajiyar shirin ciyar da dalibai.

Kara karanta wannan

Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

Daga karshe ya mika godiya ga hukumar wayar da kan jama'a (NOA) da kuma shirin bautar kasa na NYSC wajen taimakawa a gani badakalar.

'Yan Kwangilar Magungunan Yaki da Cutar Korona Sun Yi Zanga-Zanga a Abuja

A wani labarin, an samu tashin-tashina a birnin tarayya Abuja daga 'yan kwangilar da suka samar magani da kayayyakin yaki da Korona ga hukumar babban birnin tarayya (FCTA) bisa rashin biyansu hakkinsu tun 2019.

Rahoton da muke samu daga jaridar The Nation ya bayyana cewa, 'yan kwangilar na zanga-zanga ne bisa rashin samun cikon kudin da suke bin gwamnati.

An ce 'yan kwangilar sun toshe mashiga ma'aikatar FCT, lamarin da ya jawo cunkoso tare da hana ababen hawa shiga sakateriyar FCTA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel