FG ta kaddamar da rabon N5,000 ga mutane 130,764 a jihar Zamfara

FG ta kaddamar da rabon N5,000 ga mutane 130,764 a jihar Zamfara

- FG ta kaddamar da shirin bada tallafin N5,000 ga mutane 130,764 a jihar Zamfara

- Wadanda zasu ci gajiyar tallafin sun fito daga kananan hukumomi 6 na jihar kuma suna cikin rejistar shirin tallafawa 'yan kasuwa

- Haka zalika, gwamnati ta jaddada aniyarta na kawo karshen ta'addanci a jihar Zamfara dama jihohin da ke fama da matsalar 'yan ta'adda

Gwamnatin tarayya ta hannun ma'aikatar jin kai da bada tallafi ta kasa ta kaddamar da shirin bada tallafin N5,000 ga mutane 130,764 a jihar Zamfara.

Mutanen da zasu ci gajiyar tallafin shirin na CCT sun fito ne daga kananan hukumomi 6 na jihar, wadanda suka shiga cikin rejistar shirin tallafawa 'yan kasuwa GEEF, na jihar.

A cewar Sadiya Umar Farouq, shirin CCT na a cikin bishiyar li'irabin shirin samar da walwala na kasa NSIP, da aka kaddamar a 2016 karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

An samar da shirin da nufin tsamo talaka daga kangin talauci ta hanyar bada tallafin N5,000 a kowanne wata, ga wadanda ake kallo a matsayin mafi talauci a cikin al'umma.

Ta bukaci wadanda zasu ci gajiyar shirin da suyi amfani da wannan tallafi wajen bunkasa kasuwancinsu.

Ministar a madadin gwamnatin tarayya ta jajantawa gwamnati da al'ummar jihar Zamfara na asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi a jihar sakamakon harin 'yan ta'adda.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Joy Nunieh ta fayyacewa majalisar tarayya gaskiya kan badakalar NDDC

FG ta kaddamar da rabon N5,000 ga mutane 130,764 a jihar Zamfara
FG ta kaddamar da rabon N5,000 ga mutane 130,764 a jihar Zamfara Source: Twitter
Asali: UGC

Ta roki al'ummar jihar da su baiwa gwamnatin tarayya goyon baya wajen kawo karshen irin wannan kashe kashen wulakancin da ake yi.

Farouq ta tabbatarwa jihar cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari na yi duk mai yiyuwa wajen ganin ta kawo karshen 'yan ta'adda a jihar Zamfara da sauran jihohin da abun ya shafa.

Ta ce nan bada jimawa ba, kowa zai koma gudanar da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar hare haren 'yan ta'adda ba.

A wani labarin kuma, Tsohuwar shugabar hukumar Niger Delta, Joy Nunieh, ta fayyace gaskiya gaban majalisar tarayya kan badakalar da aka tafka a hukumar NDDC na karkatar da wasu kudade.

Daga ranar Alhamis ne binciken da akeyi na badakalar hukumar NDDC ya kara daukar zafi inda jami'an rundunar 'yan sanda suka mamaye gidan Nunieh da ke Fatakwal.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng