Mutanen da muka baiwa bashin Trader-Moni sun ki biya - Gwamnatin tarayya

Mutanen da muka baiwa bashin Trader-Moni sun ki biya - Gwamnatin tarayya

Yan Kasuwan da aka baiwa bashin jari karkashin shirin 'Trader Moni' da gwamnatin tarayya ta shirya karkashin ma'aikatar jin dadin da walwalan al'umma domin rage talauci, sun ki biya.

Jagorar shirin NSIP ta jihar Kwara, Hajiya Bashirah AbdulRazaq-Sanusi, ta bayyana hakan ranar Laraba, The Punch ta ruwaito.

Hajiya Bashirah tace kimanin mutane 10,000 suka samu bashin 'Trader Moni' a jihar idan aka raba musu kimanin bilyan 1.3.

Ta ce abin damuwan shine mutanen na ikirarin cewa ba zasu biya ba.

"Talakawa basu shirya biyan bashin da aka basu ba saboda tunanin yan Najeriya kan duk wani abin dake da alaka da gwamnati, a ganinsu sun ci banza."

"Hakazalika wadanda suka raba musu kudin basu rubuta sunaye, adireshi da lambobin wayansu ba, saboda haka, tilastasu biya na da bakar wahala." Hajiya Bashirah tace

Ta yi bayanin cewa an kaddamar da shirin ne domin baiwa kananan yan kasuwa bashi domin bunkasa kasuwarsu.

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya kaddamar da shirin a shekarar 2019 inda aka rabawa mata N10,000 da sharadin zasu biya.

A tsarin shirin, duk wanda ya biya N10,000 zai samu sabon bashin N50,000.

KU KARANTA WANNAN: Mun ceto mutane 5 cikin wadanda aka sace a Abuja cikin daren Laraba - Yan sanda

Mutanen da muka baiwa bashin Trader-Moni sun ki biya - Gwamnatin tarayya
Mutanen da muka baiwa bashin Trader-Moni sun ki biya - Gwamnatin tarayya
Source: UGC

DUBA WANNAN: Sheikh Murtala Sokoto ya ce irinsu Isa Pantami su ka fi dacewa da shugabanci

A wani labarin daban, Kimanin manoma 3,383 da suka karbi bashin N364 million domin noman rani da damina tsakanin 2018 da 2019 a jihar Taraba sun yi batan dabo.

A rahoton The Guardian, reshen kungiyar manoman shinkafa a Najeriya na jihar Taraba (RIFAN), ta bayyana hakan. Mukaddashin shugaban kungiyar, Tanko Andami, yace kudin da manoman kungiyarsa suka karba bashi sun ki biya, kuma da dama cikinsu sun gudu.

Andami ya bayyana mamakin dalilin da zai sa manoma su ki cika alkawuran da suka dauka ba.

Yace: "Babu ko daya cikinsu yanzu haka da ya dawo da kudin bashin da aka bashi, kuma da dama cikinsu sun gudu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel