Yanzu yanzu: Shirin TraderMoni ya samu babbar matsala a Abeokuta

Yanzu yanzu: Shirin TraderMoni ya samu babbar matsala a Abeokuta

- Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan ta'adda ne sun kai hari a kasuwar Lafenwa da ke garin Abeokuta, jihar Ogun

- An ruwaito cewa 'yan ta'addan sun tarwatsa shirin raba tallafin 'TraderMoni' a lokacin da jami'an shirin ke tattara sunayen wadanda za su ci gajiyar shirin

- Shirin 'TraderMoni', shirin gwamnatin tarayya ne da aka bullo da shi domin tallafawa kanana da matsakaitun 'yan kasuwa, ta hanyar basu rancen kudi

Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan ta'adda ne sun kai hari a kasuwar Lafenwa da ke garin Abeokuta, jihar Ogun, inda ake tsakiyar raba tallafin shirin gwamnatin tarayya na 'TraderMoni' ga 'yan kasuwar.

Wakilin jaridar SaharaReporters ya ruwaito cewa 'yan ta'addar sun tarwatsa shirin raba tallafin a lokacin da jami'an gudanar da shirin suke kan tattara sunayen wadanda za su ci gajiyar shirin a karkashin jagorancin Mrs Ramotalai Olatunji.

KARANTA WANNAN: Maganar gaskiya: Buhari na son ganin ana zubar da jinin 'yan Nigeria - Secondus

Yanzu yanzu: Shirin TraderMoni ya samu babbar matsala a Abeokuta
Yanzu yanzu: Shirin TraderMoni ya samu babbar matsala a Abeokuta
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda za su gajiyar shirin sun ranta a na kare, a lokacin da 'yan ta'addan suka kai hari cikin kasuwar.

A lokacin da wakilin jaridar ya ziyarci kasuwar bayan kai harin, ya ruwaito cewa ya taras da wasu tsirarun mata na zaune a cikin inuwa domin jiran dawowar jami'an shirin.

Shirin 'TraderMoni', shirin gwamnatin tarayya ne da aka bullo da shi domin tallafawa kanana da matsakaitun 'yan kasuwa, ta hanyar basu rancen kudi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel