Gwamnatin Buhari ta fara kaddamar da shirin N-Power a karo na uku
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta shirya tsaf don fara aiwatar da shirin N-Power
- Gwamnatin ta kuma bayyana mafitar da shirin na N-Power zai samar a cikin al'ummar kasa
- Hakazalika, an tsara yadda shirin zai gudana cikin sauki yadda kowa zai mora yadda ya dace
Abuja - Gwamnatin tarayya a ranar Litinin 23 ga watan Agustan 2021 ta fara kaddamar da shirin N-Power rukunin C shashi na farko, The Nation ta ruwaito.
Ma'aikatar agaji da ayyukan jin kai ta kasa ta fara aikin yin rajista na rukuni na uku na masu cin gajiyar shirin a ranar 26 ga Yuni, 2020.
Ministar agaji da ayyukan jin kai, Sadiya Farouq ta ce sama da mutum miliyan shida suka nuna sha'awarsu ga cin gajiyar shirin.
Ta ce rukunin C zai dauki mutane 510,000 don cin gajiyar shirin sashi na farko da kuma mutane 490,000 a sashi na biyu.
Ta ci gaba da bayanin cewa a karkashin Batch C1, an zabi 450,000 don amfana a karkashin bangaren masu digiri yayin da masu cin gajiyar 60,000 za su zama wadanda ba su kammala karatun ba.
A cewar Ministar, a karkashin bangarorin da suka kammala karatun digiri, masu cin gajiyar shirin za su rika samun alawus na wata-wata na N30,000 yayin da sabanin su za a rika biyan su N10,000 a kowane wata.
An kirkiro shirin ne don taimakawa matasa 'yan Najeriya su samu da kuma habaka kwarewarsu a rayuwa don zama kwararru a kasuwannin cikin gida da na duniya.
Ana sa ran wadanda za su ci gajiyar shirin za su dukufa a fannonin ilimi, noma, kiwon lafiya, gini, ICT da fannonin masana'antu.
Da take magana game da shirin, Sadiya ta ce:
"Duk masu cin gajiyar shirin ana ba su jari don ba su damar fara kasuwancin a cikin sana'o'in da suka zaba."
Don tabbatar da biyan kudi ta tsarin bayanai ba tare da bata lokaci ba, ministar ya kuma ce an kaddamar da wasu tsare-tsare ta kafar NASIMS) tare da hadin gwiwar manyan MDAs ciki har da NYSC, UBEC, NPHCDA, NOA don aiwatar da ayyukan yadda ya kamata.
An sanar da mataki na gaba a shirin N-Power na gwamnatin Buhari
Ma'aikatar Aikin Jin Kai da Ci Gaban Jama'a ta sanar da mataki na gaba ga masu neman shiga shirin N-Power karkashin rukunin C sashi na farko.
Babban Sakatare, Bashir Alkali, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi ya ce ma’aikatar ta fara mataki na gaba na yin rajista tare da tabbatar da adiresoshin imel ta masu neman shiga shirin.
Alkali ya yi kira ga wadanda aka zaba da su duba asusun sakonnin adiresoshin imail din su don tabbatarwa da samun karin bayani, The Nation ta ruwaito.
An cimma nasara: Minista Pantami ya ce saura kiris 5G ya fara aiki a Najeriya
A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da jimawa ba za ta dasa cibiyar sadarwa ta 5G a cikin kasar don kara gudun cudanyar yanar gizo, in ji TheCable.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani Isa Pantami ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).
Pantami ya ce shawarar dasa cibiyar sadarwa ta 5G ta biyo bayan sakamakon cikakken bincike, kwakwaf da gwajin kawar shakku kan barazana ga tsaro ko kiwon lafiya.
Asali: Legit.ng