Fadar shugaban kasa ta saki jerin jihohi 30 da ke cin moriyar shirin ciyar da dalibai
- Gwamnatin tarayya ta ce shirin ciyar da daliban makarantar firamare da abincin da aka noma a Najeriya ya mamaye jihohi 30 na kasar nan
- Ta bayyana cewar yanzu haka shirin na ciyar da dalibai miliyan 9.2 a cikin dalibai miliyan 12 da shirin ke da niyyar ciyar wa a fadin Najeriya
- Gwamnatin ta Buhari ta ce manufar shirinta na tallafa wa 'yan kasa (N-SIP) shine inganta rayuwar talakan Najeriya
Shirin nan na ciyar da daliban makarantun firamare da abincin da aka noma a Najeriya (HGSFP) ya yi mamaya zuwa jihohi 30 na kasar nan ya zuwa yanzu, kamar yadda wani jawabi daga fadar shugaban kasa ya bayyana.
Laolu Akande, babban mai taimaka wa mataimakin shugaban kasa a bangaren yada labarai, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu, a Abuja. Ya ce, burin gwamnatin shugaba Buhari shine inganta rayuwar 'yan Najeriya.
Ya bayyana cewar shirin tallafa wa 'yan kasa (N-SIP) da gwamnatin tarayya ta bullo da shi, ya na matukar kawo canji mai kyau a rayuwar 'yan Najeriya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.
Akande ya ce, yanzu haka dalibai miliyan 9.5 na cin moriyar shirin, sannan ya kara da cewa gwamnatin na da burin ciyar da dalibai miliyan 12 ne a karkashin shirin a jihohi 36.
DUBA WANNAN: Kotu ta bawa EFCC damar kama wasu manyan ministoci biyu a gwamnatin PDP
Jihohin da yanzu haka ke cin moriyar shirin kamar yadda Akande ya lissafa su ne; Anambra, Abia, Akwa Ibom, Adamawa, Bauchi, Benue, Borno, Kuros Riba, Ebonyi, Enugu, Kaduna, Kebbi, Kogi, Sokoto, da Nasarawa.
Ragowar su ne hada da; Taraba, Ogun, Oyo, Osun, Filato, Delta, Imo, Kano, Jigawa, Katisna, Neja, Gombe, Ondo, Edo da Zamfara.
Ya kara da cewa bayan ciyar da daliban, shirin ya samar da aiki ga masu girka abinci 101,913 a jihohin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng