Wata Sabuwa: Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Jirgin Shugaban Kasa a Kasuwa
- Gwamnatin Najeriya ta sanya jirgin shugaban kasa a kasuwa yayin da shugaban kasar y afara hawa sabon jirgi
- Rahotanni sun bayyana bayanai da aka gani a Shafin yanar gizo na yadda za a sayar da jirgin mai tsawon shekaru
- Hakazalika, an bayyana yadda a baya jirgin ya samu matsaloli na gyara, lamarin da ya kai ga sayar da shi nan take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta saka tsohon jirgin Shugaban Ƙasa Boeing 737-700 BBJ a kasuwa domin sayarwa. An sanya jirgin a jerin kayan siyarwa na kamfanin AMAC Aerospace da ke Basel, Switzerland.
An sayi jirgin ne a shekarar 2005 a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da kuɗi kimanin dala miliyan $43.
Wannan mataki na zuwa ne watanni bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma amfani da tsohon jirgin Airbus A330-200 da aka gyara, sakamakon matsin tattalin arziki da kuma sukar jama’a.

Asali: UGC
Wane jirgi shugaban zai koma hawa yanzu?
Jirgin Airbus ɗin, wanda aka samo daga wani bankin Jamus da ya karɓe shi daga wani kamfani, ya ci kusan dala miliyan $100.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin yanzu, an kai shi kasar Afirka ta Kudu domin sauya launinsa zuwa kore-fari-kore da kuma sanya alamomin shugaban ƙasar Najeriya.
A halin yanzu, Shugaba Tinubu na amfani da wani jirgin BBJ na wucin gadi da aka yi rajista a San Marino, mai lamba T7-NAS.
Matsalar da jirgin ya samu a baya
Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa tsohon jirgin BBJ mai lamba 5N-FGT ya fuskanci matsala a wata tafiya zuwa Saudiyya a watan Afrilu 2024, lamarin da ya tada hankali kan tsaron jirgin.
Duk da an yi masa gyara a watan Yuli 2024 – ciki har da sabbin kafet da kujerun aji na farko – hakan bai haifar da da mai ido ba. Hakazalika, ba a haɗa jirgin cikin wani shirin kula da injinsa ba.
Injinan jirgin guda biyu na CFM56-7BE suna nuna "on condition", wato ana amfani da su har sai sun nuna gajiya ko lalacewa.
An tanadar da jirgin da sabbin kayan more rayuwa kamar Wi-Fi na Ka-Band da talabijin har guda biyar a sassa daban-daban na cikin jirgin. Kuma yana daukar fasinja sama da 33.
Karin abubuwan da ke cikin jirgin
Wurin girki a cikinsa na cike da kayan aiki na zamani: magasa mai tururi, injin sanyaya abinci, da sauran su. Hakanan akwai bandakuna guda hudu a cikin jirgin.
Jirgin yana da karfin tafiyar kasashe saboda yana ɗauke da tankunan mai har guda takwas da ke ƙara ƙarfin ajiyar mai zuwa fam 70,000.
Yanzu haka jirgin na fuskantar gwaje-gwajen B1-B2 a ofishin AMAC Aerospace, yayin da ake jiran a kammala domin fara siyarwa ga masu sha’awa.

Asali: UGC
Rahotanni sun ce za a iya tuntubar kamfanin domin samun farashin jirgin kai tsaye. Amma har yanzu fadar shugaban kasa ba ta fitar da sanarwa kai tsaye ba kan sayar da jirgin ba.
Yadda malajisa ta yi biris da sayawa Tinubu jirgi
Wani bincike ya gano cewa fadar shugaban kasa ta yi biris da majalisar dokokin kasar nan wajen sayowa shugaba Bola Ahmed jirgi.
A watan Yuni ne aka sansu bullar labarin cewa gwamnatin kasar nan ta sayo sabon jirgin sama Airbus A330 daga wani banki da ke kasar Jamus.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa tun daga fara shirin sayen jirgin, jami'an gwamnatin tarayya su ka yi gum da bakunansu a kan lamarin.
Asali: Legit.ng