Majalisa Ta Gindaya Sharudan Dawo da Sanata Natasha Ofis bayan Umarnin Kotu
- A ranar Juma'a kotun tarayya ta soke dakatarwar wata 6 da Majalisa ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
- Majalisar Dattawa ta ce dole ne Natasha ta bi umarnin kotu, ciki har da neman gafara kafin a dawo da ita kan kujerarta
- Rahotanni sun tabbatar da cewa majalisar ta ce hukuncin kotu bai hana ikon Majalisa na ladabtar da mambobinta ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja Abuja - Majalisar Dattawa ta bayyana cewa dole ne Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta cika wasu sharudda da kotu ta gindaya kafin ta dawo kujerarta.
A ranar Juma’a, Mai shari’a Binta Nyako ta yanke hukunci inda ta ce dakatarwar wata shida da Majalisar Dattawa ta yi wa sanatar Kogi ta Tsakiya ba ta dace ba, tana mai umartar a dawo da ita.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ce ta yi hira da mai magana da yawun majalisar dattawa kuma shi ya bayyana sharudan da ake so Natasha ta cika.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dakatar da Natasha a watan Maris bayan rikici tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda ya samo asali daga batun yadda aka tsara zaman zauren majalisar.
Asalin rikicin Natasha Akpoti da majalisa
Lamarin ya ƙara zafi ne bayan da Natasha ta bayyana a gidan talabijin inda ta zargi Akpabio da dakatar da ita ne saboda kin amincewa da bukatunsa na lalata, zargin da shugaban ya musanta.
Natasha, wadda ke jam’iyyar PDP, ta kai kara gaban kotu inda ta nemi a soke dakatarwar da Majalisar ta yi mata, tana mai cewa an tauye mata hakkin ta bisa dokar kasa.
Kotun ta soki dokar Majalisa da aka dogara da ita wajen dakatar da ita, tana mai cewa ta yi tsauri fiye da kima kuma ta sabawa tsarin ladabtarwa na majalisun dokoki.
Majalisa ta ce dole Natasha ta cika sharudda
Yayin da yake mayar da martani kan hukuncin, mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya bayyana cewa Natasha ba za ta dawo ba har sai ta cika sharuddan kotu.
Ya ce hukuncin kotun bai soke ikon Majalisa na hukunta mambobinta ba, domin kotun ma ta tabbatar cewa Sanata Natasha ta aikata kuskure.
“Ba wai kotu ta hana mu hukunta mambobi ba ne. Kotun ta ce akwai wasu abubuwa da dole ta yi, ciki har da neman gafara.
"Sai ta kammala hakan, sannan Majalisa za ta zauna ta tattauna kan dawowarta,”
Majalisar dattawa na jiran matakin Natasha
Adaramodu ya ce Majalisa za ta jira Natasha ta dauki matakin da kotu ta bukata kafin ta yanke hukuncin karshe.
Ya kara da cewa:
“Bai kamata mu fara daukar mataki yanzu ba. Kotu ta riga ta yanke hukunci, don haka sai mun ga abin da Natasha za ta yi.
"Idan ta nemi gafara kamar yadda kotu ta ce, sannan za mu zauna mu duba matakinmu,”

Asali: Facebook
Ana so majalisar tarayya ta kirkiri jihohi 46
A wani rahoton, kun ji cewa an bukaci karin jihohi yayin da majalisa ke tattara bayanai kan bukatar sauye sauye a Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa majalisar ta samu bukatu daga Arewa da Kudu domin kirkirar sababbin jihohi 46.
A yanzu haka dai majalisar za ta cigaba da zama domin duba bukatun da ganin matakin da ya kamata da dauka kan lamarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng