Yakin Iran da Israila Ya Lafa, Amurka Ta Gargadi Mutanenta game da Najeriya

Yakin Iran da Israila Ya Lafa, Amurka Ta Gargadi Mutanenta game da Najeriya

  • Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da saƙon gargaɗi ga Amurkawa da ke zaune musmman a babban birnin Abuja
  • An buƙace su da su ƙara sanya lura da taka tsan-tsan sosai da yadda suke gudanar da rayuwarsu a babban birnin na Najeriya
  • Hakazalika an shawarce su da su guji yin tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa sansanin sojoji da wasu wuraren gwamnati

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da sanarwar gargaɗin tsaro ga Amurkawa da ke zaune a babban birnin tarayya Abuja.

Ofishin jakadancin ya shawarci ƴan Amurka da su guji yin tafiye-tafiye marasa muhimmanci a birnin Abuja.

An gargadi Amurkawa a Najeriya
Amurka ta gargadi mutanenta da ke Abuja Hoto: @RealDonaldTrump
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An buƙaci Amurkawa su yi taka tsan-tsan a Abuja

Ofishin jakadancin ya shawarci ƴan ƙasar Amurka da su guji yin tafiye-tafiye marasa mahimmanci zuwa sansanonin sojoji da kuma wuraren gwamnati da ke Abuja, bisa la’akari da ƙaruwar matsalar tsaro a duniya baki ɗaya.

Sanarwar ta bayyana cewa yanzu haka, an haramtawa dukkan ma’aikatan ofishin jakadancin da iyalansu ziyartar sansanonin sojoji ko wasu wuraren gwamnati a cikin Abuja, sai dai idan hakan ya zama dole saboda ayyukan hukumomi.

Wannan matakin ya biyo bayan wasu sauye-sauyen da ba a bayyana ba a faɗin duniya, wanda suka haddasa ƙarin fargaba da kuma sake nazarin hanyoyin zirga-zirga a wurare masu matuƙar tsaro.

Hakazalika an shawarci ƴan ƙasar Amurka da ke zaune ko masu yawo a Najeriya da su kasance cikin shiri a kowane lokaci, musamman a yankunan da baƙi daga ƙasashen yamma, ma'aikatan gwamnati, da kuma ƴan ƙetare ke yawan ziyarta.

Sanarwar ta kuma shawarci ƴan ƙasar Amurka da su guji tarurruka masu yawa, su guji yin amfani da hanya ɗaya a kullum, sannan su san hanyoyin fita na gaggawa a gine-ginen da suke shiga.

An ba Amurkawa shawara

An kuma shawarce su da su sake nazarin matakan tsaro na kansu tare da kiyaye tsattsauran matakin kula da lafiyarsu da tsaronsu yayin da suke Najeriya, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Amurkawa sun samu shawara kan zamansu a Abuja
An bukaci Amurkawa su lura sosai kan zamansu a Abuja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Saboda ƙaruwar matsalolin tsaro da ke tasowa daga halin da ake ciki a duniya, ofishin jakadancin Amurka a Najeriya na sanar da Amurkawa cewa an haramta wa dukkan ma’aikatan jakadanci da iyalansu yin tafiye-tafiye marasa alaka da aiki zuwa sansanonin soja ko wasu wuraren gwamnati a Abuja a halin yanzu."

Hakazalika sanarwar ta ƙara da cewa sassan kula da harkokin fasfo da takardun izinin shiga na Ofishin Jakadanci a Abuja da na Legas za su ci gaba da kasancewa a buɗe.

Amurka ta samo maganin kariya daga HIV

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kula da maganguna da abinci ta Amurka (FDA) ta amince da maganin kare kamuwa da cutar HIV.

Allurar wacce aka amince da ita, ana buƙatar a riƙa yin ta sau biyu a shekara don hana kamuwa da cutar.

Hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) ta yaba da wannan nasara wadda ta ce babban ci gaba ne a yaƙin da ake yi da HIV.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng