Jami'an EFCC Sun Kai Samame a Hedkwatar Hukumar NAHCON, an Samu Bayanai

Jami'an EFCC Sun Kai Samame a Hedkwatar Hukumar NAHCON, an Samu Bayanai

  • Jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, sun yi dirar mikiya a hedkwatar hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) da ke Abuja
  • A yayin samamen da jami'an na EFCC suka kai, sun tsare kakakin hukumar NAHCON tare da wasu mutane uku domin gudanar da bincike
  • Jami'an sun kai samamen ne a binciken da suke ci gaba da yi kan zargin karkatar da tallafin N90bn da aka ba da a lokacin aikin Hajjin 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) sun kai samame a hedikwatar hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) da ke birnin tarayya Abuja.

Jami'an na EFCC sun kai samamen ne a ranar Talata, biyo bayan zargin almundahana da karkatar da kuɗaɗe.

Jami'an EFCC sun kai samame a hedkwatar NAHCON
Jami'an EFCC cafke wasu jami'an hukumar NAHCON Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa jami'an na EFCC sun gudanar da samamen ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe.

Kara karanta wannan

"Ba wanda ya fi karfin doka": Gwamnan CBN da wasu kusoshin Gwamnatin Tinubu sun shiga matsala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an EFCC sn tsare kakakin NAHCON

Jami'an na EFCC sun kama kakakin hukumar NAHCON, Fatimah Usara, tare da wasu ma’aikata uku da ba a bayyana sunayensu ba.

Ma'aikatan EFCC sun je hedkwatar hukumar ne ɗauke da sahihiyar takardar izinin kama mutane, abin da ke nuna matuƙar muhimmancin lamarin.

Wannan bincike na daga cikin ci gaba da ƙoƙarin bankaɗo zargin karkatar da Naira biliyan 90 da aka ware domin tallafin aikin Hajjin 2024.

Wata majiya daga hedikwatar EFCC ta bayyana cewa akwai zarge-zarge masu nauyi da ake yi wa NAHCON dangane da yadda aka tafiyar da kuɗin.

Ana zargin hukumar NAHCON da laifuffuka

Matakin na EFCC na zuwa ne bayan wani samame da hukumar ICPC ta kai a kwanakin baya, wanda hakan ke ƙara nuna zargin da ake yi kan yadda ake tafiyar da kuɗi a NAHCON.

Lokacin da aka tuntuɓi mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale, domin jin ta bakinsa kan samamen, ya ƙi yin wani gamsashshen bayani.

Kara karanta wannan

"Zargin baki biyu": Fusatattun mutane sun bankawa gidan basarake wuta a Kano

Amma ya bayyana cewa za a fitar da ƙarin bayani game da kama mutanen da kuma binciken a nan gaba.

Gwamna Dikko Radda ya ba NAHCON shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ba da shawara ga hukumar alhazai ta ƙasa kan kuɗin da mahajjata suke kashewa.

Gwamna Radda ya buƙaci hukumar da ta rage yawan kwanakin da Alhazai suke yi a ƙasa mai tsarki, domin hakan zai taƙaita kuɗaden da suke kashewa yayin aikin Hajji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng