APC Ta Yi Rashi da Aka Sanar da Rasuwar Shugaban Ƙaramar Hukuma na 4 a Shekara 1
- Shugaban karamar hukuma karkashin mulkin APC a jihar Lagos ya rasu bayan fama da rashin lafiya na watanni
- Musbau Ashafa, wanda ke wa'adi na biyu, ya taba zama shugaban APC a Otto-Awori, kuma ya fara tashe tun shekarar 1997 a mulkin soja
- A cikin shekara guda, APC ta yi rashi mai yawa inda wasu shugabannin karamar hukuma uku, Olakanle, Shobowale da Toba Oke suka rasu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Shugaban karamar hukumar Otto-Awori da ke jihar Lagos, Prince Musbau Ashafa, ya riga mu gidan gaskiya.
Rasuwar ta girgiza al'ummar yankin lamarin da ya sa APC ta shiga jimami bayan rasa ciyamomi hudu a shekara daya kacal.

Asali: Original
Yadda shugaban karamar hukuma ya rasu a Lagos
Ashafa wanda ya fito daga masarautar Ijanikin, ya rasu jiya Juma’a bayan fama da wata rashin lafiya da ta shafe watanni, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa ba a gan shi a bainar jama’a na wani lokaci ba, kuma kaninsa Waliu Ashafa ne ke jagorantar harkokin ofis.
Ashafa yana wa’adi na biyu a matsayin shugaban karamar hukumar kafin Allah ya dauki rayuwarsa.
Kafin rasuwarsa, marigayin ya rike mukamin shugaban APC a karamar hukumar Otto-Awori.
Ashafa ya fara samun karbuwa a 1997 a mulkin Janar Sani Abacha lokacin da aka zabe shi shugaban tsohuwar karamar hukumar Ojo.
Tun daga wancan lokaci ya kasance mai tasiri a siyasar yankin Ojo har zuwa lokacin da ya zama shugaban APC da kuma shugaban karamar hukuma.

Asali: Facebook
Yawan ciyamomi da APC ta rasa a shekara 1
Ana iya tuna cewa jam'iyyar APC ta rasa kusan shugabannin karamar hukuma hudu a cikin shekara guda, Punch ta ruwaito.
Dukan shugabannin kananan hukumomi hudu da ake maganar APC ta rasa sun fito ne daga jihar Lagos wacce jam'iyyar ke mulki.
Har ila yau, daga cikinsu, uku sun mutu ne bayan fama da doguwar jinya wanda daya daga cikinsu har sai da aka naɗa mukaddashin ciyaman domin kula da harkokin mulki.
Haka kuma, tsohon shugaban karamar hukumar Ifako-Ijaiye, Toba Oke, ya rasu a watan Fabrairu bayan fama doguwar jinya na wata cuta mai tsanani.
Karanta sauran labarai da ke da alaƙa da wannan:
- Rai Ya Yi Halinsa: Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi Mutuwar Bazata, an Samu Bayanai kan silar mutuwar
- Lokaci Ya Yi: Shugaban Karamar Hukuma Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Hatsari a Jihar Niger
- Katsina: An Yi Babban Rashi a Katsina, Sabon Shugaban Karamar Hukumar Bakori Ya Rasu
- Mukaddashin Shugaban Karamar Hukuma Ya Rasu a Bauchi ana Saura 'Yan Kwanaki Zabe
Shugaban karamar hukuma ta rasu a Ramadan
Mun ba ku labarin cewa shugabar karamar hukumar Ayobo-Ipaja, Bolatito Shobowale, ta rasu bayan doguwar jinya, lamarin da ya jefa al’umma a alhini da jimami.
Mai rikon mukamin shugabar, Otunba Ladi Oluwaloni, ya tabbatar da mutuwarta, yana cewa lamarin ya girgiza shi matuka kuma sauran al'umma.
An yaba da irin gudunmawar Shobowale wajen ci gaban unguwanni, kiwon lafiya, da karfafa al'umma tun lokacin da take kan mulki a jihar Lagos.
Asali: Legit.ng