Dalung Ya Yiwa Tinubu Wankin Babban Bargo, Ya Fadi Abin da Zai Hana Shi Mulki a 2027
- Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya nuna ƙarara cewa baya ƙaunar talaka
- Ya yi zargin Tinubu ne ne shugaban Najeriya na farko dake amfani da talauci da tsananin yunwa wajen daƙile al'ummarsa
- Dalung ya kara da cewa wannan na daga cikin dalilan da talakawa ke kara marawa hadakar su Atiku Abubakar baya gabanin 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da azabtar da talakawa da yunwa.
Solomon Dalung ya ce Tinubu ne shugaban Najeriya tilo da ya bayyana karara cewa yana ƙin talakawa ta hanyar jefa su a talauci da wahala.

Asali: Facebook
The Guardian ta wallafa tsohon Ministan na cewa ka da a ɗauki sauya shekar da wasu 'yan siyasa ke yi zuwa jam’iyyar APC a matsayin alamar karɓuwar Shugaba Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalung: "APC na kwasar yan siyasa masu laifi"
Independent Newspaper ta ruwaito Dalung ya yi zargin cewa yawancin marasa gaskiya ne ke shiga jam’iyyar APC domin samun kariya daga bincike ko hukunci.
Ya ce:
"Sun aikata miyagun laifuffuka ga al’umma kuma suna neman gafara ta hanyar shiga jam’iyyar APC, ba wai suna da kishin Tinubu ba ne.”
Ya kara da cewa Shugaba Tinubu na amfani da kalmar saudakarwa ga ƙasa ba a gurbinta ba, domin shi, mai ɗakinsa da ɗansa na rayuwa a cikin walwala.
Dalung na da ƙwarin gwiwa kan haɗakar adawa
Dangane da batun sabuwar haɗakar siyasa da Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da wasu ke jagoranta kafin zaɓen 2027, Dalung ya ce wannan karon abubuwa sun sha bamban.
A cewar Dalung:
“Wannan haɗaka ta bambanta da duk wanda aka yi tun daga Jamhuriyar farko, Shugaban ƙasa ya bayyana kansa a matsayin abokin gaba ga talakawa kuma talakawa na mutuwa da yunwa da rashin abinci mai gina jiki."

Asali: Getty Images
Tsohon Ministan ya ce kodayake 'yan siyasar da ke cikin haɗakar suna da bambancin ra’ayi, duk sun haɗu ne da burin kawo ƙarshen salon mulkin da APC ke yi.
Ya kara da cewa:
"Wannan haɗaka na kara karɓuwa a tsakanin talakawa, ba za su damu da wanda aka tsayar takara ba, illa ba su bayar da muhimmanci wajen kawo ƙarshen wahalar da suke sha."
Solomon Dalung ya ce hadakar yan adawa zaɓi ce ga talakawa yayin babban zaben 2027 dake gabatowa.
'Marasa kishi sun kewaye Tinubu,' Dalung
A baya, mun ruwaito cewa tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana cewa ‘yan-ba-ni-na-iya ne suka zagaye Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce mutanen da suka dabaibaye Shugaban kasa sun fi na lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari dabara da tasiri wajen tafiyar da gwamnati.
A cewarsa, mutanen na amfani da ilimi da fahimtarsu wajen toshe hanyoyin da bayanai za su kai wa Shugaba Tinubu kai tsaye.
Asali: Legit.ng