Katoɓara a Jigawa: Ya kashe mahaifinsa, kan an ki ayi masa aure

Katoɓara a Jigawa: Ya kashe mahaifinsa, kan an ki ayi masa aure

Jami’an rundunar yansandan jihar Jigawa sunyi caraf da wani matashi mai shekaru 25 da laifin hallaka mahaifinsa kan yaki yayi masa aure.

Katoɓara a Jigawa: Ya kashe mahaifinsa, kan an ki ayi masa aure

Kaakakin rundunar yansandan jihar SP Jinjiri Abdullahi ya bayyana haka yayin dayake yi ma yan jaridu karin bayani ta waya.

KU KARANTA: Masu ciwon Sikila su dubu 17 ne a jihar Katsina

SP Jinjiri yace matashin mai suna Abdulhamid Abdullahi mazaunin karamar hukumar Kirikasamma ya kashe mahaifin nasa ne saboda yaki yayi masa aure, duk kuwa tare da cewar mahaifin yayi ma yayunsa aure.

SP jinjiri ya cigaba da fadin Abdulhamid ya mamayi mahaifin nasa ne da misalin karfe 3 na daren Lahadi 5 ga watan Feburairun shekara 2017 yayin da yake cikin sharbar barci, inda ya maka masa ice, sa’annan ya bishi da gatari.

Sai dai yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa, amma yace shifa ba uban nasa yake hari ba, babban yayansa yake hari, sai aka samu sabani.

Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu!

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel