Gobara: Aminu Ado Ya Ziyarci Kasuwar Waya a Kano, Ya ba da Gudunmawar Miliyoyi
- Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya aike da wakili domin jajantawa game da gobarar da ta tashi a kasuwar wayar nan ta Farm Center
- Gobarar ta lakume dukiyoyi da dama, inda Baffa Babba Dan’agundi ya wakilci Sarkin wajen jajanta wa wadanda abin ya shafa a madadinsa
- Dan’agundi ya ce Sarkin ya damu matuka da lamarin, yana addu'ar Allah ya mayar wa jama'a da asarar, tare da ba da tallafin makudan kudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya ziyarci inda aka samu iftila'in gobara a jihar Kano.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa gobara ta tashi a kasuwar waya (Farm Centre) wanda ya jawo asarar dukiyoyi.

Asali: Facebook
Aminu Ado ya jajantawa yan kasuwar waya
Hakan na cikin wata sanarwa da shafin Masarautar Kano ya wallafa faifan bidiyon a manhajar Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce Baffa Babba Dan'agundi ne ya wakilci basaraken domin jajantawa al'umma abin da ya faru.
A cikin bidiyon, Dan'agundi ya yi alhini kan abin da ya faru inda ya ba wadanda abin ya shafa hakuri.
Aminu Ado ya shiga damuwa game da gobarar
Dan'agundi ya ce Aminu Ado ya kadu matuka da samun labarin inda ya ce Allah ne kaɗai zai iya mayar musu da abin da suka rasa.
Ya ce:
"Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW).
"Assalamu alaikum, za mu ce Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un, a madadin Mai Martaba, Sarkin Kano tun da muka ji labarin wannan gobara, muka yanke hukuncin a taho domin ta'aziyya.
"Da abin da ya faru ba mu samu daman zuwa ba saboda wasu dalilai da ba sai na fada ba."

Asali: Facebook
Gobara: Gudunmawar da Aminu Ado ya bayar
Dan'agundi ya bayyana yadda gobarar ta taɓa zuciyar Aminu Ado Bayero wanda ya so zuwa da kansa amma Allah bai nufa ba.
"Kamar yadda kuka sani lokacin da aka yi gobara a Kwari, ranar da ya dawo take muka je.
"Wannan abu ya dame shi kwarai da gaske, ya so ya zo da kansa, amma ba mu son don wani ya yi muma a ce sai munyi.
"Wannan abu ne na masifa dukanmu ya shafe mu, kannenmu ne ƴaƴanmu ne jikokinmu ne, muna yi muku jaje.
"Allah ne kaɗai zai iya mayar da abin da aka rasa, ba za mu ce sai mun yi abin da wasu suka yi ba, za mu ba da N2m."
- A cewar Dan'agundi
Aminu Ado ya ƙarawa Alan Waƙa girman sarauta
A baya, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya daga darajar sarautar da ya ba Aminu Ladan Abubakar.
Basaraken ya ce lokacin da yake Sarkin Bichi ya ba mawakin da aka fi sani da Alan Waƙa sarautar Ɗan Amanan Bichi.
A yanzu, basaraken ya ce bayan shawarwari da manyan mutane a kasa, ya daga darajar sarautar zuwa Ɗan Amanan Kano gaba daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng