Ana Shirin Hadaka, Tsohon Na Kusa da Atiku Ya Gana da Shugaba Tinubu
- Tsohon mai magana da yawun Atiku Abubakar, Segun Showunmi ya sanya labule da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Babban ƙusan na jam'iyyar PDP ya ziyarci Shugaba Tinubu ne a gidansa da ke Legas domin yi masa barka da Sallah
- Segun Showunmi ya bayyana cewa sun tattauna sosai tsakaninsa da shugaban ƙasan a yayin ziyarar da ya kai masa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Segun Showunmi, tsohon mai magana da yawun Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Segun Showunmi ya ziyarci shugaban ƙasan ne domin murnar barka da Sallah a gidansa da ke Legas.

Asali: Twitter
Babban ƙusan na jam'iyyar PDP ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a ranar Lahadi, 8 ga watan Yunin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon na kusa da Atiku ya gana da Tinubu
Segun Showunmi ya wallafa hoto a shafinsa na X a daren ranar Lahadi yana tsaye kusa da Shugaba Tinubu.
Ya kuma bayyana cewa sun yi muhimmiyar tattaunawa tsakaninsa da shugaban ƙasan.
"Ranar Sallah ta uku! Na samu lokaci mai inganci tare da shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunonin sojojin Najeriya, @officialABAT GCFR. Tattaunawar ta kasance mai armashi."
- Segun Showunmi
Wannan wallafa ta Showunmi ta zo ne a daidai lokacin da ƴan majalisa da dama daga jam’iyyun adawa, ciki har da PDP, ke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
Yawaitar sauya sheƙar ya haifar da damuwa daga shugabannin jam’iyyun adawa dangane da matsayinsu na siyasa gabanin zaɓen 2027.
Showunmi ya taɓo batun haɗaka
A watan Afrilu, Showunmi ya bayyana cewa PDP ba za ta bari a tilasta mata shiga wata haɗakar siyasa maras tabbas ba.
Ya ce kowane mutum na da ƴancin yin alaƙa ta siyasa da kowa, amma jam'iyyu irin PDP dole ne a tunkare su da girmamawa ga tsari da aƙidar jam’iyyar, cewar rahoton jaridar The Cable.

Asali: Twitter
Showunmi ya ƙara da cewa tsohon ubangidansa, Atiku Abubakar, wanda ke riƙe da ra’ayin kafa haɗakar jam’iyyun adawa, har yanzu bai yi wata takamammiyar tattaunawa da jam’iyyar PDP ba kan batun.
Showunmi ba shine kaɗai daga cikin na kusa da Atiku da suka ziyarci Shugaba Tinubu ba.
Ƴan adawa na ziyartar shugaba Tinubu
Ziyararsa ta ƙara fito da jerin ganawa tsakanin Tinubu da wasu fitattun mutane da suka taɓa kasancewa ƙwararan ƴan adawa, wanda hakan ke haifar da tambayoyi kan inda za su nufa gabanin 2027.
A watan Nuwamba da ya gabata, Tinubu ya naɗa Daniel Bwala, wanda shi ne mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku a 2023, a matsayin mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin sadarwa da yaɗa labarai.
Ndume ya ƙi goyon bayan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa bai tare da APC wajen goyawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027.
Ndume ya bayyana cewa bai gamsu da matakin da jam'iyyar ta ɗauka na goyon bayan tazarcen Tinubu a 2027.
Ya bayyana cewa yana jin tausayin shugaban ƙasan domin idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, ba zai kai labari ba.
Asali: Legit.ng