Dubu Ta Cika: Yadda Gwamnatin Jigawa Ta Gano Ma'aikatan Bogi 7,000

Dubu Ta Cika: Yadda Gwamnatin Jigawa Ta Gano Ma'aikatan Bogi 7,000

  • Gwamnatin jihar Jigawa ta samu nasarar bankaɗo ma'aikatan bogi waɗanda ke karɓar albashi daga cikin asusunta
  • Kwamishinar kuɗi ta jihar, Hannatu Sabo ta bayyana cewa tuni aka kori ma'aikatan daga cikin jerin masu karɓar albashi
  • Sabo ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta kuma ƙara ɗaukar sababbin ma'aikata a ɓangaren noma, lafiya da ilmi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana cewa ta gano kusan ma’aikata guda 7,000 na bogi da ke karɓar albashi.

Gwamnatin ta ce ta gano hakan ne yayin wani bincike da aka gudanar domin tantance ma’aikatan da ke aiki a hukumomi da sassan gwamnati daban-daban.

Gwamnatin Jigawa ta gano ma'aikatan bogi
Gwamnatin Jigawa ta kori ma'aikatan bogi Hoto: @aunamadi
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce kwamishiniyar kuɗi ta jihar, Hannatu Sabo, ce ta bayyana hakan a ranar Laraba a birnin Dutse, yayin wata hira da manema labarai domin bikin cika shekaru biyu da Gwamna Umar Namadi ya yi a kan mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asirin ma'aikatan bogi ya tonu a Jigawa

A cewar Hannatu Sabo, ma’aikatan bogin sun ƙi bayyana don tantance su, wanda hakan ya sa aka cire sunayensu daga jerin masu karɓar albashi.

“Wadanda ake zargin ma’aikatan bogi ne an cire su daga tsarin biyan albashi saboda sun kasa bayyana domin tantancewa."
“Gwamnati ta nuna ƙudirinta na gaskiya da riƙon amana ta hanyar wannan binciken da kuma cire ma’aikata na bogi daga tsarin biyan albashi."

- Hannatu Sabo

Kwamishiniyar ta danganta nasarar tantancewar da ƙoƙarin gwamnatin wajen daidaita tsarin ma’aikata da kuma kawar da yaudara a cikin aikin gwamnati.
“Ƙoƙarin gwamnatin jihar Jigawa na kawar da ma’aikatan bogi da kuma daidaita tsarin ma’aikata na nuna jajircewarta wajen gaskiya da amana."

- Hannatu Sabo

Gwamnatin Jigawa ta ɗauki sababbin ma'aikata

Ta bayyana cewa binciken ya bai wa gwamnati damar ɗaukar sababbin ma’aikata a ƙarƙashin shirye-shiryen J-Health, J-Teach, da J-Agro, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Haka kuma, Hannatu Sabo ta yi bayani kan yadda gwamnatin ke biyan albashi mai tsoka ga ma’aikatanta, tana mai cewa jihar na biyan kashi 100 cikin 100 na sabon tsarin albashi, wanda ya sanya ta cikin jihohi masu biyan albashi mafi tsoka a Najeriya.

Gwamnatin Jigawa ta dauki sababbin ma'aikatan
Gwamnatin Jigawa ta bankado ma'aikatan bogi a Jigawa Hoto: @aunamadi
Asali: Facebook

Baya ga albashi, kwamishiniyar ta bayyana cewa jihar ta samu ƙarin kuɗi daga gwamnatin tarayya, wanda hakan zai ƙara ƙarfin kuɗin shiga na jihar.

"Mun samu ƙarin kuɗi daga gwamnatin tarayya ta hanyar rabon kuɗin wata-wata ga jihar da kuma ƙananan hukumomi, kuma wannan zai taimaka matuƙa wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba."

- Hannatu Sabo

Kwamishina ya maida ragowar kuɗi a Jigawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Auwalu Danladi Sankara, ya nuna halin dattako da gaskiya.

Kwamishinan ya maida ragowar kuɗin da suka ragu bayan an kammala aikin ciyarwa na watan azumin Ramadan.

Auwalu Danladi Sankara ya maida Naira miliyan 301 a asusun gwamnatin jihar a matsayin abin da ya yi rara bayan an kammala shirin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng