Eid El Adha: 'Yan Sanda Sun Sake Cin Karo da Sarki Sanusi II, An Haramta Hawan Sallah a Kano
- Rundunar ƴan sandan Kano ta sake saɓawa sarki na 16, Muhammadu Sanusi II kan batun hawan sallah yayin da ake shirin sallar layya
- Ƴan sanda sun jaddada haramcin hawan sallah a Kano saboda barazanar tsaro kamar yadda ta faru a lokacin bikin ƙaramar sallah
- Wannan mataki dai ya ci karo da sanarwar da masarautar Kano ta fitar, wacce ta gayyaci hakimai zuwa zuwa hawan babbar sallar bana
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta sake jaddada haramcin gudanar da hawa a fadin jihar yayin bukukuwan babbar sallah saboda dalilan tsaro.
Rundunar ta sake haramta hawan sallah ne a wata sanarwa ta haɗin gwiwar hukumomin tsaro da aka fitar yau Talata a birnin Kano.

Asali: Facebook
'Yan sanda sun saɓawa Muhammadu Sanusi II
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan sanarwa ta fito ne awanni kadan bayan Masarautar Kano ta fitar da katin gayyatar hakimai da masu dawaki zuwa hawan sallah na shekara-shekara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masarautar ta gayyaci sarakuna da hakimai su shigo Kano tare da dawakansu domin fara shirin hawan sallah a ranar Laraba, 4 ga Yuni 2025 (8 Dhul Hijjah 1446 AH).
A cikin wata sanarwar, rundunar ƴan sanda ta taya musulmi da mazauna jihar Kano murnar zagayowar babbar Sallah, tare da kira da a kiyaye doka da oda.
An sake haramta hawan sallah a Kano
‘Yan sanda sun bayyana cewa bayan samun sahihan bayanan leƙen asiri da kuma nazarin tsaro na baya-bayan nan, haramcin gudanar da duk wani nau’i na hawan sallah a jihar Kano yana nan daram.
Rundunar ƴan sandan ta ce haramcin na nan kamar yadda aka sanar tun lokacin Sallar Eid-el-Fitr da ta gabata saboda barazanar tsaro da har yanzu ba a magance ba.
Sanarwar ta ce:
“Barazanar da ta sa aka hana hawan sallah a baya har yanzu tana nan ba a kau da ita gaba ɗaya ba.
"Mun samu bayanan sirri da ke nuna cewa wasu baragurbi da masu daukar nauyinsu na shirin yin amfani da hawan sallah don tayar da zaune tsaye, kamar yadda aka gani a Sallah da ta gabata.”
Abubuwan da ƴan sanda suka haramta
Don kare doka da oda, yan sanda sun hana hawan kilisa, tseren mota da tuƙin rashin hankali, mallakar bindiga ko makami ba bisa ka’ida ba da ɗaukar abu mai hadari a bainar jama'a.
An kuma bukaci iyaye da masu kula da yara su ja kunnen ‘ya’yansu kada su bari su fada hannun masu tada fitina, Leadership ta rahoto.

Asali: Facebook
Rundunar ta jaddada cewa hukumomin tsaro za su tabbatar da an bi waɗannan dokoki ba tare da sassauci ba.
Sanarwar ta kuma bukaci al’umma da su yi amfani da lokacin Sallah wajen nuna hakuri da hadin kai, tare da cewa:
“Yayin da muke murnar wannan lokaci mai albarka, mu roƙi Allah ya tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya, mu roki Allah ya yiwa ‘yan wasa da suka rasu a hadarin mota rahama."
Sarki Sanusi II ya yi magana kan talauci
A wani labarin, kun ji cewa Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa ya fahimci asalin ma’anar talauci ne bayan ya hau karagar mulki a matsayin Sarkin Kano.
Sarkin na 16 ya yi ikirarin cewa manyan ƙasar nan da yawa ba su san menene talauci ba, kawai dai suna ji ana faɗa.
Sanusi II ya yi kira ga shugabanni da su kasance masu jin ƙai da nuna tausayi ga mutanen da aka damƙa musu jagoranci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng