Bayani Dalla Dalla kan Hukuncin Sallar Juma'a da Azahar a Ranar Idi
Malamin Musulunci, Farfesa Rashid Abdulganiy ya yi bayani kan hukuncin sallar Juma'a da azahar idan ranar Idi ta kama ranar Juma'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - A makon da ya wuce mai alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da cewa babbar sallah za ta kasance ranar Juma'a, 10 ga watan Zul Hijja.
Kamar kullum, an samu rudani kan hukuncin sallar Juma'a da azahar idan ranar Idi ta fado a ranar Juma'a.

Asali: Facebook
A wannan rahoton, Mun tattauna malamin addini a jami'ar jihar Gombe, Farfesa Rashid Abdulganiy domin bayani kan hakuncin sallar Juma'a da azahar a irin wannan yanayi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a yi sallar Idi ranar Juma'a a 2025
A makon da ya wuce gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da cewa za a yi hawan Arafa a ranar Alhamis mai zuwa.
Hakan na zuwa ne bayan ganin watan Zul Hijja da aka yi a kasar Saudiyya bayan watan Zul Ka'ada ya kare.
A Najeriya ma, mai alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da cewa an ga watan Zul Hijja kuma za a yi Idin sallar layya a ranar Juma'a, 10 ga Zul Hijja.

Asali: Facebook
A sakon da ta wallafa a X, gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Juma'a a matsayin ranar hutu domin ba mutane damar yin bikin sallah lafiya.
Hukuncin sallar Juma'a a ranar Idi
A wata tattaunawa da Legit Hausa ta yi da Farfesa Rashid Abdulganiy, malamin ya bayyana cewa ba wannan ne karon farko da aka samu Idi ya hadu da Juma'a ba.
Malamin ya bayyana cewa sallar Idi ta taba haduwa da ranar Juma'a a zamanin Annabi Muhammad (SAW).
A karkashin haka ya ce da lamarin ya faru, Annabi (SAW) da kansa ya bayyana hukuncin sallar Juma'a idan ta hadu da Idi.

Asali: Facebook
Farfesa Rashid ya ce a ranar da Idi ya hadu da Juma'a, Annabi (SAW) ya ce:
“Idi biyu sun haɗu a wannan ranar, don haka duk wanda ya so, sallar Idi za ta wadatar masa a maimakon sallar Jumu'a, amma mu kuwa za mu yi sallar Jumu'a bayan Idi."
A karkashin haka malamin ya ce hukuncin sallar Juma'a a ranar Idi ya bayyana karara a wannan Hadisin na Annabi (SAW).
A takaice, Malamin ya ce babu laifi idan mutum bai je sallar Juma'a ba bayan ya halarci sallar Idi a ranar sallah.
Hukuncin azahar idan aka yi idi ranar Juma'a
Farfesa Rashid ya ce a cikin bayanin da aka yi ba inda hadisin ya ce sallar azahar ta fadi idan aka yi Idi ranar Juma'a.
Malamin ya ce malamai da dama sun soki ra'ayin cewa babu sallar azahar idan aka yi sallar Idi ranar Juma'a saboda magana ce mai rauni.

Asali: Getty Images
Sheikh Rashid Abdulganiy ya ce:
"Abin da ya fi zama daidai shi ne mutum ya yi sallar azahar idan ba zai je Juma'a ba."
Nasiha ga daliban ilimi kan yanke hukunci
Farfesa Rashid Abdulganiy ya ce ya kamata daliban ilimi su rika taka tsantsan wajen yanke hukunci ko fatawa kan wani lamari.

Asali: UGC
Malamin ya ce yana da kyau dalibi ya tabbatar ya yi bincike sosai kafin yanke matsaya kan wata mas'ala.
A cewarsa:
"Yana da kyau dalibi ya karanta littattafai kamar 10 da suka yi magana a kan mas'ala ba wai kawai su rika yanke hukunci bayan karanta littafi daya ba."
Tun tsirar yanar gizo ake samun yawaitar bullar malamai da ke fitowa tare da yada da'awa duk da basu cancanta ba.
Wannan ya sa ake samun sabani da dama a fannin da ya shafi a addini, musamman a kasa mai yawan Musulmi kamar Najeriya.
Za a fassara hudubar Arafah zuwa Hausa
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya sanar da yarukan da za a fassara hudubar Arafa ta shekarar 2025.
A wannan shekarar, za a fassara hudubar cikin yaren Hausa, Fulatanci da Yoruba tare da wasu harsuna da dama.
Rahotanni sun nuna cewa kasar Saudiyya ta yi hakan ne domin tabbatar da cewa sakon cikin hudubar ya isa ga mutane da dama a duniya.
Asali: Legit.ng