Eid El Adha: Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Sanar da Ranar Babbar Sallah a Najeriya

Eid El Adha: Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Sanar da Ranar Babbar Sallah a Najeriya

  • Fadar Sarkin Musulmi ta tabbatar da cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah, wanda ke nuna cewa watan Dhul Qa'adah ya kare yau Talata
  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar II ya ayyana ranar Laraba, 28 ga watan Mayu a matsayin 1 ga watan Dhul Hijjah, 1446H
  • Hakan dai na nufin musulmin Najeriya za su yi hawan idin sallar layya a makon gobe, ranar Juma'a 6 ga watan Yuni, 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya sanar da cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah yau Talata, 27 ga watan Mayu, 2025 a Najeriya.

Sultan ya bayyana ranar Laraba, 28 ga watan Mayu, 2025 a matsayin 1 ga watan Dhul Hijjah na shekarar 1446H, watan sallar layya.

Sultan.
Sarkin Musulmi ya ce an ga jaririn watan Dhul Hijjah a Najeriya Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Getty Images

Ɗan kwamitin ganin wata na fadar sarkin musulmi kuma masanin ilimin taurari, Simwal Usman Jibrin ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu labarin ganin wata a Najeriya

Simwal ya ce:

"Assalamu alaikum, Mai Alfarma Sarkin Musulmi na Sakkwato ya bayyana gobe Laraba, 28 ga Mayu, a matsayin ranar farko ta watan Dhul Hijjah.
"Nan ba da jimawa ba fadar sarkin musulmi za ta fitar da cikakken bayani a hukumance in sha Allah."

Hakan dai na nuna cwwa al'ummar musulmi a Najeriya za su yi babbar sallah watau Eid El Adha ranar Juma'a 6 ga watan Yuni, 2025, daidai da 10 ga watan Dhul Hijjah, 1446.

Sallah: Sanarwa daga fadar sarkin Musulmi

Fadar Sarkin Musulmi ta fitar da sanarwa a hukumance, tana mai tabbatar da ganin jaririn watan Dhul Hijjah a Najeriya.

Sanarwar na ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin kula da harkokin addinai na fadar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu.

Ya ce mai alfarma Sarkin Musulmi wanda shi ne shugaban Majalisar ƙoli mai kula da harkokin musulunci a Najeriya (NSCIA), Alhaji Sa'ad Abubakar ya ayyana Laraba a matsayin 1 ga Dhul Hijjah.

Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Laraba, 28 ga watan Mayu a matsayin 1 ga watan babbar sallah 2025 Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Facebook

Farfesa Sambo Wali ya ce:

"Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, CFR, mni, shugaban Majalisar kula da harkokin musulunci (NSCIA) ya bayyana gobe Laraba a matsayin ranar farko a watan Dhul Hijjah.

Wannan wata na Dhul Hijjah na da matuƙar daraja a addinin musulunci, a cikinsa ne musulmi ke yin ibadar aikin hajji, ɗaya daga cikin rukunan addinin.

An ga watan sallar layya a Saudiyya

A wani labarin, kun ji cewa hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah a yau Talata, 29 ga watan Dhul Qa'adah, 1446 daidai da 27 ga watan Mayu.

A cewar sanarwar da mahukuntan Saudiyya suka fitar, alhazai za su yi hawan Arafah a ranar Alhamis, 9 ga watan Dhul Hijjah, wanda zai yi daidai da 5 ga watan Yuni, 2025.

Wannan sanarwa dai ta tabbatar da cewa watan Dhul Qa'adah ya kare, gobe Laraba ne 1 ga watan Dhul Hijjah, 1446H, sannan ranar Juma'a 6 ga Yuni za a yi sallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262